Showing 1 words to 3000 words out of 145565 words

Chapter 1 - TABARMAR KASHI BOOK 1 NA SAFIYYA HUGUMA.pdf

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_


*_TABARMAR K'ASHI_*

*SAFIYYA HUGUMA*

_AREWABOOKS:Huguma_
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 01


K'awataccen bedroom ne me yalwa,wanda ya wadatu da kyawawan kayan gado da suka
kasance cikamakin ado da kyawun dakin,komai dake cikin dakin an hada masa color iri daya
CREAMY WHITE da ratsin gold me daukar idanu,ya wadatu da sanyin ac da kuma haske sosai
tarwai.
Saidai kuma abinda zai baka mamaki shine,duk da irin kayan ado da qawar da
bedroom din ya mallaka,kusan komai na dakin a hargitse yake,hatta da tattausan farin bedsheet
din da comforter din dake daga gaban gadon a yamutse suke guri guda,uwa uba kuma
dukkansu sunyi staining da wasu abubuwa da bazaka iya tantance meye a jiki ba,illa dai ka
ragewa kanka wahala ka kirasu da datti kai tsaye.

Daga can tsakiyar gadon kuwa, matashiya ce zaune sannan a cure waje daya,tamkar
wadda ke shirin saka kanta cikin gangar jikinta ta koma abu guda,ta rungume gwiwoyinta sosai
a qirjinta. Baka iya hangen fuskarta,amma kana iya hangen sassalkan gashinta me tsaho da
santsi daya cukurkude,kwatankwacin yadda zare yake cakudewa guri guda,tsahon sumar ya
sanyata barbazuwa har saman qafafunta,ya kuma rufe dogayen fararen singalalin hannunta.
Rigar jikinta doguwar riga ce ta wani material ne ruwan madara,kallo daya zakayi masa kasan
me tsada ne,saidai shi kansa ya canza yanayi yayi wani irin azababben squeezing.

Idan ka kasa kunne da kyau zaka iya jin sautin kukanta,sautin da bashi da wani qarfi ko
karsashi a cikinsa ko misqala zarratin,saboda rashin wadatacciyar garkuwar jiki da zata bata
wannan damar,uwa uba kuma.......tayi kukan tayi kukan har batasan adadi ba,ta zubda
hawayen har sai data daina sanin lokacin tahowarsu......har sai da idanunta suka fara gani dishi
dishi,ta yanke tsammani daga samun dukkan dauki,ta kuma gama sallamawa qaddara
rayuwarta.

Duk da cewa a hankali ya bude qofar dakin amma hakan bai hanata jin alamun an bude
din ba,a hankali ta daga kanta,ta kuma sauke dubanta ga bakin qofar,duk da mummunar
wahala da ibtila'i me gigita hankali da gusar da imanin me raunin tauhidi da take fuskanta,amma
har yanzu kyakkyawar fuskar nan tata tana nan yadda take,wani irin kyau na daban me matuqar

tasiri da fusgar hankali da ya gagara gushewa shimfide saman fuskar tata,saidai kana kallonta
kasan ba haka take ba,abubuwa da yawa sun canza wanna fuskar.

Shi da ita suka zubawa juna ido kamar yau ce ranar farko da suka fara ganin
juna,kowannensu da kalar kallon da yakewa dan uwansa. Dariya ya saki ya cire hannuwansa
daga aljihun trouser din jikinsa,ya fara takowa zuwa cikin dakin bayan ya sanya hannu ya maida
murfin qofar dakin ya rufe. Yana takowa yana tafa hannayensa, idanuwansa kuma a kanta
kamar yadda dariyarsa bata yanke ba,ita kuma taci gaba da binsa da kallo,zuciyarta tana
la'antarsa,tana sake daukaka qararsa zuwa ga sammai wajen ubangijin al'arshi.

A haka ya qaraso,ya jawo stool zuwa gaban gadon,ya zauna sosai yana fuskantarta
hadi da taka gefen gadon da qafarsa guda daya

"Kewai kina tunanin akwai abinda zakiyi da zai warware dukka shirina?,ko kina zaton zaki
kubuta da sauqi haka?" Kyawawan idanunta da suka sake zama manya manya ta
lumshe,ragowar hawayen da basu samu damar zubowa ba suka gangaro,sannan ta budesu
tarwai a kansa
"Bani da tsumi kuma bani da dabara,ban isa na fidda kaina ba,amma na kaiwa me kowa me
komai,mai iko akan kowa qararka,koda kayi ajalina.....koda bayan raina ina fatan nutsuwa da
salama suyi qaura daga rayuwarka,ka girbe fiye da abinda ka shuka" ido ya runtse ya kuma
bude a tare yana sakin qaramin murmushi,sai ya miqe tsaye
"Dadina dake tawakkali....." Yayi furucin yana qara taku biyu zuwa gaban gado,ya haye gefan
gadon ya zauna,sai tayi saurin sake tattare qafafunta ta rungumesu da kyau,kamar wanda yake
shirin raaba mata maciji a jikinta.

Qafafun nata yabi da kallo har ya zuwa fuskarta,sai ya sake qyalqyalewa da dariya

"Ina sonki.....kuma banajin zan daina sonki,saidai kin shiga hurumin daba naki ba,kin shigar
gonar daba taki ba,kin tsallake iyakarki,kuma a yanzu nafi buqatar wadan nan abubuwan fiye
dake,ki daukominsu ki damqamin,ke kuma na barki kici gaba da rayuwarki cikin salama" kai
take girgizawa tana hawaye,wani irin mamakinsa tana jin kamar zai kasheta, kowacce rana da
zata bullo zuwa faduwarta cikin shakka da kokwanto take,anya wannan din ADAM NE?,anya
adam dinta ne?,anya musanyensa akayi mata ba?,ko kuma wata rundunar mugayen shaidanun
aljanu ta shige jikinsa ne ta samu mafaka?,don abinda yakeyi a yanzun da ainihin wannan
suffar tasa ta yanzu.......bata taba ganinta a tattare da adam dinta ba,koda kuwa cikin mafarkan
bacci bare a kai ga rayuwa ta zahiri,adam din da ko quda baya qaunar ya sauka a kanta?,adam
din dake kuka da idanunsa idan bata da lafiya?,adam din da yake kasa bacci saboda ta shiga
damuwa?,adam din da yake kasa sukuni idan tana da buqata har sai ya adar mata?,dole ta
shiga shakka.....amma kuma kullum yana qara tabbatar mata da cewa shi dinne fa,bawai kama
ko musaye bane,to me yake faruwa?.

"Bazan taba baka ba.....burinka bazai taba cika ba,saidai na rasa rayuwata,kayi duk abinda
kaga dama" ta fada tana jin bacin rai yana taso mata,tare da wani irin qwarin gwiwar tunkarar
duk nau'in kalar azaba tuggu da makircin daya shirya mata.

Wani murmushi ya kuma saki yana dubanta,da wani irin kallo na qasa qasa mai cike da
tarin mugunta

"Ke kike jawa kanki koma meye,tunda ke muguwa ce ba zaki iya sallamamin abinda kikafi
qarfinsa ba tako ina,to nima bazan sassauta miki ba har sai sanda kika gasu,kikaji cewa zaki iya
sallamawa" daga haka ya miqe,ya fara fidda kayan jikinsa yana zubarwa a wajen.

Idanu ta bude da kyau cikin tsananin tashin hankali tana dubansa,kada dai ace
haqqinsa na aure yake shirin karba kamar yadda ya saba?,zallar rashin imanin da yake gwada
mata bai sanya ya daga mata qafa ba,yakance

"Har yanzu fa a sunan matata kike,ban saki igiyar ba,wannan abun dake faruwa wani issue ne
na daban daya shafi interest dina da kuma naki". A duk lokaci irin wannan idan ya rabeta tana
jin inama zata bude idanu taganta kwance cikin ramin qabarinta?,banda addininmu ya haramta
kisan kai,naka ko na Wani,tabbas da tuni ta tsufa da kai kanta kiyama.
Da gaske so yake ya kusanceta alhalin yasan cewa cikin jinin al'ada take,rashin imanin
nasa qara gaba yake,dole tace rundunar shaidanun aljanu ne suka shigeshi,don lamarinsa yafi
qarfin shaidani guda daya.

Kansa tsaye ya nufota gadan gadan,kamar ba adam din nan da abaya a lokutta irin
wanann yake sanyata taji babu ya ita cikin 'ya'ya mata ba,ya sanyata taji duk duniya babu
macen da tayi sa'ar abokin rayuwa irinta ba,a yanzu ya koma mata wani tsohon annamimin ifritu
mashayin jinin bil'adama da ko motsinsa bataso ji bare ya rabeta,bashi da maraba da qaton
shaidani a idanuwanta.

Ringing din wayarsa ya dakatar dashi daga sake tunkarota,sai ya koma cikin aljihun
wandonsa da ya yasar yana lalubar wayar. Cikin hanzari ya karata a kunnensa,sai kuma yace

"Ok,yanzu yanzu?,tom" ya latse wayar da sauri ya maidata,sannan ya soma mayar da kayan
jikin nasa tana daga zaune tana kallonsa.

Ga mamakinta sai taga yana bi yana balle button na rigarsa yana watsarwa,ya kama
gaban rigar da qarfin tsiya ya ciccisge,sannan ya tsugunna ya jawo plate din tangaran din dake
ajjiye gefe wanda ya kawo mata abincin da bata budawa bare ta taba,ya dagashi har abincin ya
tamfatsa shi da qasa ya tarwatse,ya dauki wani yanki daga ciki ya yanki jikinsa ya kuma
shashshafe maiqon a jikinsa.

Sake miqewa yayi ya fara fatali da kayan dake saman madubi da duk wani abu na glass

dake dakin yana cewa da matuqar daukaka murya

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ki tsaya......ki tsaya don Allah,ya salam,karki jiwa kanki ciwo,
Hasbunallahu wa ni'imal wakeel,ya hayyu ya qayyumu ya baki lafiya" yana fada hawaye na
sauka a idanunsa,yana kuma ci gaba da tarwatsa dakin tare da sake hargitsashi,bayan tsaiwa
da tayi tayi masa gyara na nutsuwa,waiko hakan zai sanya wani daga cikin ahalin nata su
ankara da cewa akwai hankali tattare da ita.

Sanqamewa tayi a zaune,tunaninta ya dinke cifff kan meye manufar adam na aikata
haka?,saidai koma meye tasan halinsa,ungulu ne baya jewar banza,ba shakka akwai abinda
yake shirin sake qullawa. Kafin takai ga lalubo abinda ke shirin faruwa sai ta tsinci muryoyin
mutanen da a kullum take addu'ar isowarsu gareta,qila akwai wani haske da zai risketa,ya kuma
zama silar fitarta daga duhu zuwa haske.

Da mugun qarfi ta yunqura zata dira daga gadon,yayi caraf ya tsallako ya damqeta ya
cukuikuyeta da kyau yana sake yamutsa rigata da yamutsatsen gashinta.

Ya mata mugun riqon da bazata iya qwacewa ba,saboda banbancin qarfi da kuma
qarancin garkuwa jiki dake tare da ita,don haka ta bude baki da zummar kiran daya daga ciki

"Koda kin kirasun ma sun shigo sunanki bazai canza ba a idanunsu,sunanki mahaukaciya har
yau har gobe,sai ranar da kika fanshi kanki,ni kuma zan wankeki a idon duniya" daga haka yaci
gaba da qaraji da ambaton sunan Allah yana mata kyakkyawan riqo,ita kuma taci gaba da
yunqurin qwacewa hawaye na gudu bisa fuskarta, kokawa ta barke a tsakaninsu duk da cewa
ba wata nasara a hakan sai azabar riqon da yayi mata da takesha,dai dai sanda aka turo qofar
da sauri aka shigo,ya saki wani lafiyayyen murmushi daga can qasan zuciyarsa,burinsa ya
cika,plan dinsa ya tafi a dai dai,dama abinda yakeso kenan.


FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800

Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_* 💔
_Arewabooks:Huguma_
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 02


*_1988_*

Cikin madaidaicin falon matsakaicin gidan,wanda bai cika da wani kayan ado da qawa na
rayuwa ba,saidai tsananin tsaftar data bayyana kanta jikin kowanne loko da saqo na gidan zai

matuqar burgeka tare da daukar hankalinka,har kayi sha'awar matsakaicin gidan.

Kyakkyawar macace fara sol,irin farin da zai iya daukan hankalinka,tare da alamta maka
cewa lallai mutum yana da nasaba da wani yare cikin yarukan nigeria zuwa afrikaans da kowa
yasan fatar duk wani dan yarensu farace,koda akwai baqaqe suna wahala qwarai. Duka duka
shekarun haihuwarta a ido ba zasu haura ashirin ba.
A gurguje take sakawa yaron dake tsaye a gabanta uniform dinsa,tana gyara masa
kwalar rigar uniform din,lokaci guda kuma tana jijjiga yarinyar dake goye a bayanta daketa
faman tsala kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta.

Kana kallonta zakasan a rude take,uwa uba kuma alamu sun nuna sauri takeyi sosai,fadi
takeyi cikin yanayin damuwar dake shinfide akan fuskarta

"Yi shuru......yi haquri yanzu zamu wuce kyasha iska a hanya" ta fada fana durqusawa tana
qoqarin sanyawa kyakkyawan yaron da sumarsa mai yawa da santsi ke sake kwantowa gaban
goshinsa saboda duqawar da yayi zai karba safar da take qoqarin saka masa

"Zansa da kaina ummee"

"Bari na dauko maka lunch box dinka da hijabina saimu wuce,kaima ka kusa makara yau" tayi
maganar tana miqewa,dai dai lokacin da aka bankada labulen falon aka shigo.

A nutse ta daga kai ta kalli matar,wadda zasuyi kusan sa'anni da ita,idanma ta girme
mata duka duka baifi ta bata shekara daya ba. Ita dinma ita ta kalla suka hada ido,saita dauke
kai tana yatsine fuska,ta kuma tattara dukka bacin ran duniya ta azawa fuskarta,ba tare data ko
kalli sassan da matar gidan take ba,ta wuce kanta tsaye zuwa kitchen din gidan.
Wani abune yazo ya tsaye mata a wuya,duk da cewa idan da sabo yaci ace ta saba da
mummunar hali da dabi'ar ta,amma akance,duk mutumin da yasan daraja da martabar kansa
baya iya jurewa cin xarafi daga wajen ko waye,tana da dukka hanyoyin da zata cusguna mata
ta hanata jin dadin zaman tarensu,to amma wannan ba shine muradinta ba a halin yanzu,don
haka tayi qoqarin share wannan daga ranta,ta wuce kitchen din tana dan bubbuga goyon nata
data samu ta lafa da kuka zuwa yanzu.

Tsaiwa tayi turus tana dubanta cikin kitchen din,lunch box din yaron da tazo dauka tuni
ta budeshi,ta kuma zazzage duka soyayyen chips da indomie din data dafawa yaron,wanda su
kenan sukayi saura cikin gidan nasu,sai yau da take sanya ran samun albashi take tunanin ta
biya kasuwa ta taho masa dasu.
Ba yau ne karon farko data fara yi mata irin hakan ba,saidai na yau din yafi na ko yaushe
bata mata rai da quntata matuqa,idan a baya tanayin hakan ta qyaleta ta debo wani ta dafa
masa,yanzun basu da sauran abinda zata dafa masan,don haka cikin muryarta data cika da

bacin rai tace

"Wanne irin abune haka?,bakisan abincin waye bane da kika juye kina ci?" Cikin gadara ta
waiwayo,ta watsa mata wani banzan kallo da ya sake tunzurata matuqa

"Ko abincin me gidan ne ina da right din naci qarewa ma kenan,tunda dai yaya na ne ya
kawo,guminsa ne,saboda haka banga wanda ya isa ya dinga yimin shamaki ba" wani
mummunan bacin rai ya yunquro mata,taji ya tsaye mata a wuya,kamar ma da qyar take zuqar
numfashi,har batasan sanda ta isa gareta ba ta tankwabe plate din abincin ya warwatse a qasa
ba. Itama abun yazo mata a bazata,don bata taba tanka mata ba,duk da ire iren wadan nan
abubuwan da take mata masu yawan gaske.

Da yatsa ta nunata tana kafeta da idanunta da suka canza launi

"Wannan abincin dama saurana binciccikan da kike zuba rashin mutunci da rashin tarbiyya a
kansu to ba yayan naki bane ya kawosu ba,gumi na ne ke dashi duka kuke ci,kuma daga rana
irin ta yau kinci iya rabonki kenan,duk ranar da kika qara saka hannu kika taba min wani abu
dana ajiiye cikin kitchen dina,bama kitchen dina ba gidana ma gaba daya sai nayi maganinki
naga uban daya tsaya miki" tuni ta miqe tsaye,gabanta yana faduwa saboda ta tsorata da
yadda ta ganta,ta jima tana burin wannan ranar dama

"Ni kika zaga?" A fusace ta daga kai daga kwashe lunch box din yaron ta dubeta

"Muddin wannan shine zagi to na zagekin,kiyi duk abinda kika iya"

"Wallahi wallahi sai na sakaki kinyi nadamar wannan abun da kikayimin,zakiga iya matsiyina a
wajen dan uwana"

"Na nawa kuma?,annamimiya?,wadda ta sanadinta na rasa duk wani walwala jin dadi da
fahimtar junan dake tsakanina da mijina kuma me yayi saura?,ai ba abinda ya rage sai abu
daya......"

"Wannan abu dayan shi zan ida" ta fada idanunta carr a tsaye cikin nata. Haka kawai ta samu
kanta da faduwar gaban fitar lafazin daga bakin FAUZIYYA,amma saita gyada kai

"Karki fasa shashasha wofi" kai ta jijjiga da qarfi,sanna tabi takan indomie din da tayi kaca kaca
a qasan kitchen din ta fice.

Kasa tsayawa ta tsaftace gurin tayi,sai ta juya kawai ta fice ta saka yaron a gaba zasu
fita,har taje tsakar gida ta dawo,ta laluba maqulli ta datse qofar falonta ta wuce da key
din,abinda bata taba yiba tsahon zamansu da fauziyyan.

Tun daga cikin gidan harta isa titi,bus ta iso suka hau kwanyarta empty take,babu

abinda yake mata kai kawo sai zallar illar da zaman fauziyya cikin gidanta tayi mata,ta jima da
sanin cewa FAUZIYYA annoba ce cikin gidanta,tun daga randa ta tsoma qafarta cikin gidanta
bayan rasuwar mahaifiyarsu......komai ya fara jagule mata,makira hatsabibiya kuma
annoba,wadda ta kwashe dukkan wani walwala da jin dadi gami da fahimtar juna dake
tsakaninta da mijinta da sukayi auren soyayya.....tayi amfani da matsananciyar qaunar dake
tsakaninsu ta jini daya,uwa daya uba daya,take juya akalar gidan,take kuma juya komai yadda
taga dama.

Bata taba damuwa da furucinta ba,amma a yau abinda ta fada din ya tsaye mata a
rai,har ta sauke yaran bayan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login