Showing 1 words to 3000 words out of 81944 words
[10/10, 5:26 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KaÉ—aici*
12/11/2017
© *Rahma Kabir*
*Wattpad:*@rahmakabir
*_Page 1 ~ 2_*
Ranar juma'a babban rana ce ga duk kan musulmai, da misalin ƙarfe biyun rana, Haj. Beeba
wacce yaranta suke kira da Momy ce zaune a falo tana kallon tv, tana riƙe da juice mai sanyi a
cup tana sha, kana ganinta kasan tana cikin nishaÉ—i, natsuwa tare da kwanciyar hankali.
Husna ce ta shigo falon tana raɓe-raɓe, cikin tsawa Momy ta soma magana.
"Dan ubanki zo nan, daga aike ki siyo min kati shi ne zaki je ki daÉ—e haka"
Husna saboda tsananin tsoro kamar zata saki fitsari a wando jikinta ya soma ɓari, idon nan nata
kamar zai faɗo ƙasa dan tsoro, cikin inda-inda da sanyin murya ta ce.
"Momy kuÉ—in ya faÉ—i ne ina ta nima ban ganshi ba"
Wani irin mummunar ashar Momy ta yi.
"wallahi yau me rabani da ke sai Allah, wato na baki É—ari biyar ki siyo min kati shi ne zaki yar
min, toki sani a kuÉ—in break É—inki na makaranta, kuma sai na daki kuÉ—ina Æ´ar iskan yarinya, kina
kallo na kamar mayya"
A zabure ta miƙe ta rarimo wayar wuta ta cafkota, ta shiga zuba mata a jiki, Husna ta shi ga ihu
kamar ana yankata.
"Dan Allah Momy ki yi haƙuri ba zan sake ba, wallahi ba da gan-gan na yar miki da kuɗinki ba,
wayyo Allah Dady na, Momy na ki min rai na tuba"
Dukan ta take yi kamar ta samu kato, Husnah ganin dukan ya yi mata yawa sai ta falla waje a
guje tana gunjin kuka, a bayan Baba mai gadi taje ta ɓuya sai sosa jikinta take yi, Momy a sittin
ta biyo ta tana sirfa masifa.
"Wallahi yau sai kinci ubanki za kisan kin yar min kuÉ—i"
"Hajiya dan Allah ki mata haƙuri"
Cewar Baba mai gadi.
"Yi min shuru ba ruwanka, in kuma zaka biya kuÉ—in data yar min ne sai inji, kuma bani son
shishshigi kullun ina ja maka kunne akan haka"
Baba mai gadi yaja bakinsa ya tsuke gudun karya samu matsala a aikinsa, inma da sabo ya
kamata ace ya saba da irin wannan abun da Hajiya take yiwa Husna. Haka Momy ta yi
masifarta iya yinta, daga bisani ta ce.
"Zaki shigo ciki ki sameni"
ta yi kwafa ta juya cike da mita zuwa falo.
******
Zaune yake cikin harabar gidansa ta wajen gate, zaune yake cikin wata ruffa mai É—auke da
fararen kujeru uku da table a tsakiya, iska yana hura shi, da ganin alama yana jin daÉ—in wannan
yanayin da yake ciki, ihun Husna daya ji ne duk sai ya ji hankalinsa ya tashi, ransa ya dagule
har wani ajiyar zuciya yake yi. Kasantuwar gidansa yana jikin gidansu Husna maƙota suke, duk
abin da ke faruwa a cikin gidansu Husna yana ji in dai yana cikin gidan bai fita. Yau ma
dawowarsa kenan daga masallacin juma'a sai ya ji sha'awa zama a gurin dan É—ebe masa kewar
iyayensa, kasancewar shi kaÉ—ai yake rayuwa a cikin wannan gida, tsaki yaja yana mai jinjina
kansa.
"Wannan wace irin azzalumar mace ce? Haka nan kita azabtar da yaranki, tir da hali irin naki"
Ya ce a fili tare da ɗaukar ruwa ya kurɓa dan ya ji sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa. Haka
nan yake jin tausayin Husna saboda kusan kullun sai ya ji kukanta, hakan yana matuƙar ɓata
masa rai da sanya shi damuwa, wata rana har a cikin barcinsa yana jin kukanta yana masa
guzo. Miƙewa ya yi tsaye ya ɗauki key motarsa ya fice daga gidan a fusace, ko ƙila zai samu
sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke yi masa.
******
Baba mai gadi ya zaunar da Husna a gefensa ya ce cikin lallashi.
"Husna meyasa kika zubar mata da kuÉ—i? Kuma kinsan halin Mominki bata raga miki ko kaÉ—an"
"Uhum uhum um, Baba ba da gan-gan na zubar ba, wunya nake ji banci komai ba kuma ta
aikeni, kaga ko uniform bata bari na cire ba, ni kuma da kyar nake tafiya saboda wunya nake ji,
shi ne na tsaya na huta a wani dakali, barci ne ya fara É—aukata daga nan kuma sai banga kuÉ—in
ba"
Ta ce cikin sassheƙar kuma. Baba mai gadi shuru ya yi yana tunanin halin da take ciki yarinya
ƙarama wacce a yanzu bata wuce shekara bakwai ba a duniya. Shekarunsa uku da fara aiki a
gidan, amma kullun a cikin *kaɗaici* Husna take da takura, tsangwama da hantara, har yanzu
abu bai chanza zani ba.
'Ya Allah ka fidda yarinyar nan daga wannan ƙangi'
Ya ce a cikin ransa cike da damuwa. Sai ya miƙe ya shiga ɗakinsa ya ɗauko mata sauran
abincin da ya rage mata, dama kusan kullun duk abin da ya ci yana rage mata, saboda ba sosai
Momy take bata abinci ba. Cikin sauri ta karba abincin jikinta na rawa ta soma ci, bayan ta
kammala tasha ruwa, nan take gumi ya fara karyo mata alamar ta ƙoshi.
"Tashi ki je ki cire uniform É—inki sai ki dawo in miki karatu"
Cewar Baba yana mata murmushi, cikin jin daɗi Husna ta miƙe ta wuce cikin gida. Ta samu
babu kowa a falon, cikin sanÉ—a ta shige É—akinta, uniform ta soma cirewa ta sanya doguwar rigar
atamfa, sai ta shiga toilet ta yi fitsari sannan ta fito, kayan wankinta ne jibge a gefen gadonta, ta
zauna gefen gadon ta rafka tagumi kamar wata babbar mace, hawaye ya shiga kwaranya a
kuncinta, ta shiga rera kuka babu mai lallashinta, in da sabo ta saba da wannan rayuwa,
saboda kullun cikin *kaɗaici* take, Momy sam bata ƙaunarta balle ta kula da ɗawainiyarta.
Tana cikin wannan yanayin ne sai ta ji an turo mata ƙofa, da sauri ta kalli ƙofar dan ganin wanda
ya shigo, Momy ce tsaye tana mata kallon uku saura kwata, jikin Husna ya ɗauki rawa ta miƙe
tana kama jikinta.
"Yanzu ai ga shi kin shigo hannuna ko, amma na kyale ki tunda ko banza kin daku, sai dai zan
ja miki kunne in Dady É—inki ya dawo karki kuskura in ganki a falo, dan inna ganki wallahi sai
jikinki ya gaya miki. Sannan maza ki je ki min wanke-wanke gasu can na fitar miki da shi ta
bayan kitchen, kuma ki wanke min su da kyau, da fatan kina ji na?"
Cewar Mamy cikin faÉ—a.
"Eh Momy"
Ta ce a tsorace, Momy sai ta wuce, ita kuma Husna ta biyo bayanta dan yin aikin data sanya ta.
******
Momy tana zaune a falo ita da d'anta Nura, suna kallon wani series film a tashar zee word,
sallamar Dady ne ya katse musu kallon cikin farin ciki Momy ta mike.
"Barka da dawo wa Alhaji"
"Yauwa uwar gida, na same ku lafiya?"
"Lafiya lau"
Sai ya samu guri ya zauna, Nura ya yi masa sannu da zuwa, ya amsa cike da kulawa ya kara
da cewa.
"Ya makaranta? Da fatan kana maida hankali"
"Eh Dady ina maidawa sosai gobe zamu fara text"
"Da kyau, masha Allah, Allah ya taimaka"
"Ameen Dady"
Dady ya kai dubansa ga Momy yana dan murmushi ya ce.
"Hajiya wai ina Husnah ta ke? Ba dai har ta yi barci ba?"
"Ai kasan ita kasa ce akwai saurin barci da ta ci abinci shi kenan"
"Ikon Allah, ita kullun bana samun had'uwa da ita, inna dawo ta yi barci lokacin fitana kuma tana
barci, gaskiya bari dai yau na duba ta dan rabon da in sanyata a idona yafi sati biyu fa"
Cikin hanzari ya mike zai nufi d'akinta, da sauri Momy ta tari gabansa cike da kissa.
"Haba dear yanzu fa ka dawo ko wanka baka yi ba balle cin abinci, ka bari in ka natsa sai ka je
ka ganta din"
Murmushi ya yi ya ce. "Hakane to muje inna kammala naje naga Mamana kar ta yi fushi dani"
Haka suka tafi ba tare da yaje ganin Husnan ba. Ta bangaren Husnah tana zaune a d'aki gefen
gadon a takure kamar 'yar tsako, sai kalle-kalle take yi jikin nan nata cud'u-cud'u babu wanka
balle ma tasan ya za ta yi Alwala da sallah, Momy ce ta shigo dakin, a zabure Husna ta mike
tana kallonta cikin tsoro, motmy ta yi mata wani mugun kallo wanda ya ke kada mata hanjin ciki
"To dare ya yi me kike jira baki yi barci ba? ga Dady ya dawo maza ki kwanta, kuma yanzu zai
shigo karki kuskura ya gane ba barci kike ba, in ba haka ba wallahi jikin ki zai gaya miki, kwanta
in gani"
Da sauri ta koma ta kwanta ta bama Momy baya, Momy ta jawo wani bargo ta yafa mata a jiki ta
kashe wutan dakin ta fice.
Dady ne sanye cikin jallabiya milk color, yana tafiya Hajiya na biye da shi a baya, har suka isa
dakin Husna, ya ce.
"Hajiya kunna mana wutan dakin"
Nan take ta kunna haske ya gauraye dakin, Momy na cewa
"Ai tun dazu na leko na kashe mata dan naga ta yi nisa a barcin"
Dady ya shiga bin d'akin da kallo, ya mance yaushe rabonsa daya shigo ciki, cikin damuwa ya
kalli Hajiya.
"Lafiya naga d'akin nata a hargitse sai tashin warin datti yake yi"
Ya kai kallonsa ga inda ta jibge kayan wankinta.
"Wancen kuma kayan na meye a gun?"
"Alhaji kayan datti ne, kaga dare ya yi muje mu kwanta gobe za mu yi magana"
Cewar Hajiya cike da fad'uwar gaba, Dady ya bita da kallon da tuhuma, yana son ya karanto
wasu abubuwa a tattare da ita, Hajiya dakewa ta yi kamar mai gaskiya, girgiza kai ya yi ya fice
ba tare da ya ce komai ba, ita ma bin bayansa ta yi jiki a sanyaye. Suna fita Husna ta bi kofar
da kallo tana mai zubda hawaye, kiri-kiri a na son rabata da mahaifinta mai sonta, a haka har
barci ya yi awon gaba da ita.
****
*Da safe*
Ta farka bata san ta yi wanka ba da brush, balle ta san ta yi alwala da sallah. Ta fita babban
falon ba kowa sai Jimmai mai aikinsu da take kicin, shiga ta yi ta sameta tana had'a musu
breakfast.
"Husnan Momy kin tashi?"
"Eh Mama na tashi"
Da yake haka take kiranta, ta cigaba da cewa.
"Shi ne rannan kika tafi kika barni kin dad'e baki dawo ba sai yau"
Ta ce cike da shagwaba, Jimmai dariya ta yi.
"Baba 'yar Momy shi ne kamar za ki yi kuka, ai gani na dawo, ki kwantar da hankalinki ba zan
sake tafiya in dad'e haka ba kin ji"
Ta gyad'a mata kai alamar ta gamsu, sai ta fita daga kicin din tabar Jimmai. Wurin Baba mai
gadi ta wuce tana dariya, ta sameshi zaune akan benci yana jin radio, tana ganinta ya washe
jajayen hakoransa wanda ya dafe da goro.
"Husna yar Baba kin tashi kenan"
"Eh Baba, ka rage min kunu da kosai na?"
"Husnah kenan, kununki yana nan a d'aki shiga ki d'auko kisha da kosan"
Ya ce yana murmushi, cikin jin dad'i ta nufi d'akin Baba ta d'auko ta dawo kusa da shita zauna,
ta soma ci cikin nutsuwa da santi.
Dady ne ke zagaye gidan dan shan hantsi, ya hango Husna gurin mai gadi sai hakan ya ba shi
mamaki, ya shiga tambayar kansa.
'Me take yi a gurinsa da safen nan?'
Da sauri ya katse tunaninsa ya karaso kusa dasu ya ce cikin daga murya
"Husna, Husnahhh, me kike yi a gurin nan maza zo nan"
Cikin sanyin jiki ta aje kunun da take sha da kosai, ta isa gurin Dady ta tsaya tana kallonsa,
shima binta da kallo ya yi duk ta fita hayyacinta, gaba d'aya ta bushe ta rame sai hasken wahala
ta kara, ya kai kallonta ga kanta wanda yake ba d'an kwali, gashinta ya dankare da datti ko layin
kitson ba a gani saboda daud'a, mamaki ne ya cika shi, sai ya kiran mai gadi, cikin sassarfa ya
zo ya ce
"Barka da safiya yallabai ya kwanan Iyalin?"
Dady bai amsa masa ba sai ma murtike fuska da ya yi.
"Karna sake gani cewa ka bama Husna abu tana ci, ban yarda ba kuma ban amince ba, da
fatan ka jini"
Jiki na rawa ya ce.
"Insha Allah yallabai zan kiyaye"
"Tashi ka tafi"
Jikinsa ba kwari ya mike ya tafi.
"Je kuma mu je ciki"
Dady ya yi maganar yana kallon husna, sai tabi bayansa tanakama jikinta. Momy ce zaune a
falo tana waya, da alama magana take yi daa kawarta.
"Hajiya Uwani dan Allah ki bani mafita, wallahi tunda Alhaji yaga d'akin Yarinyar nan yake
tuhumata na rasa me zance masa, ina tsoron ya kuma tambayata dan banda amsa"
Haj. Uwani ta kwashe da dariya.
"Haba Haj. habee karki bani kunya mana, sai kaceba uwar makirci,l ba, akan karamar alhaki kin
tada hankalinki"
"To ya zanyi Hajiya kin san fa Alhaji na mugun son ta dole in tashi tsaye fa"
"To ki kwantar da hankalinki kar kiji komai, ina ga ma ba sai kin yi asarar kudi zuwa wurin boka
ba, ki yi amfani da kissar ki da makirci kawai"
"To Hajiya me kike ganin zanyi ba tare dana samu matsala ba"
"Me zaki mata wanda ya wuce ki daura mata cutar Hauka"
"Hauka fa Hajiya? taya hakan zai yuwu?"
"Hahaha Haj. Habee kina bani mamaki kinbi kin damu kanki, dan Allah karki bani kunya mana"
Nan ta cigaba da jero mata yanda zata yi makirci cikin dubara da mugunta, har sai da Momy ta
gamsu. Sun cigaba da tattaunawa, sai ga Dady ya shigo Husna na biye da shi a baya, fuskar
shi ba annuri a murtuke, da sauri Momy ta katse wayar gabanta na fad'uwa, ta ce a zuciyarta..
'Allah yasa mai gadi bai min katsalan dan ya gayawa Alhaji abin da nakewa Husna'
Yanda taga yanayin Alhaji shi ne ya kara birkita mata ciki, duk iya makirci da asirin da take
takama dasu tana mugun shakkar Dady, saboda baya yi mata da wasa, binsu ta yi da kallo har
suka zauna.
Dady ya ce "...
*Rahma ce*
[10/12, 3:15 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KAÆŠAICI*
© *Rahma Kabir*
*Wattpad:*@rahmakabir
*_Page 3 ~ 4_*
Dady ya ce.
"Hajiya jiya na tambaye ki akan Husna amma kin min shuru, wai me yake faruwa ne? ji jikin
yarinya yadda duk ta lalace, ta zama kamar wacce ba tada galihu, ji kanta kamar kitson da ya yi
shekara, anya Hajiya kin kasance mai amana kuwa?"
A kid'ime Momy ta ce
"Haba Alhaji me kake nufi dani ne? duk irin ƙoƙarin da nake yi da Husna, yarinyar da..."
"Dakata! bance ki gaya min shirme ba, gaskiyar magana nake son ji"
Hajiya ta fara kukan kissa.
"Alhaji baka yarda dani ba kenan, wallahi in kaga yadda nake fama da Husna sai ka yi mamaki,
kayan wankinta da kaina nake wanke mata amma yarinyar nan ta ce bata so, kitso kuwa da
dambe ake mata, in na bata abinci sai ta zubar ta ce baza ta ci ba, wanka ko har cizona take yi
wai bata so.
Alhaji ni ce Husna take zagi, kuma ban isa in sata abu ba sai taƙi yi, ba zan yiwa mata sharri ba
ran nan cewa ta yi ai bani ce uwarta ba, dan haka karna sake yi mata wanka, na rasa ta ina
tasan bani ce na haifeta ba"
Ta ƙarasa maganar tana kuka. Husna dai na zaune tana jin ƙarairayin da Momy ke yi akanta,
wanda wasu ma bata iya gane su ba, Alhaji jikinsa ya yi sanyi.
"Yanzu Habeeba duk wannan abu yana faruwa shi ne zaki yi shuru ba zaki sanar min ba,
gaskiya baki kyauta min ba, haka zaki zuba mata ido ba tare da d'aukar mataki ba"
Wani farin ciki ne Momy taji ya lullub'eta amma sai ta b'oye hakan, ta ce.
"Alhaji abin da yasa ban gaya maka, ina ganin ai Husna yarinya ce zata daina nan gaba, kuma
wasu lokutan ina mamaki yanda take yin wasu abubuwa, zama shuru-shuru, kullun ita kad'ai a
d'aki, yawan surutai ita kad'ai, hakanan kaga tana soshe-soshe kamar wacce take da taɓin
hankali, hakan yasa nake ganin bai kamata na É—auki hukunci ba, ba tare da tabbatacin sanin
halin da take ciki ba, dan mutum mai lafiya ba zai yi haka ba"
Ta ƙara maganar cike da damuwa a fuskarta, Dady ya shiga itashin hankali.
"Amma shi ne baki taɓa sanar min ba?"
"To Alhaji banda tabbacin hakan shiyasa ban gaya maka ba, na jira ne naga in abun ya fara
yawa in sanar maka sai mu tafi asibiti"
"Ikon Allah, to ai yanzu ba shuru zamu yi ba, dole mu tafi asibiti dan a duba lafiyar
kwakwalwarta, ba za mu bari abun ya cigaba da tafiya ba, kar yazo ya sha k'arfin mu"
"Hakane Alhaji, to mu bari zuwa Monday in Allah ta kaimu sai muje muga likita, in yaso koni na
kaita saboda yanayin aikinka"
"Anya Hajiya? ina ga tare zamu dan hankalina bai kwanta ba"
"Haba Alhaji wannan abu ba wani babba bane, ai ko ni zan iya komai akai, karka damu insha
Allah ba wata matsala ba ce"
"To shi kenan tunda kin ce haka Allah ya kaimu Monday É—in"
"Ameen"
Sai ya kalli Husna wanda ta