Showing 69001 words to 72000 words out of 81944 words
Chapter 24 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
Yasir a wayar Sadiq, ya d'auka da yi masa izini
su shigo kawai, kallon Husna ya yi.
"Tashi ki je ki d'auko mayafi ki yafa"
Cikin shagwaba ta ce.
"Uncle ana zafi fa, kuma ai a falo muke ko fita za mu yi ne?"
Sadiq ya yi mqta hararan wasa.
"Malama ta shi kije kisa tun kan raina ya b'aci, su Yasir ne fa suka zo, kina nufin a haka zasu
ganki?"
Dole ta tashi ta shiga tana shagwab'a harda buga k'afa, aiko Minal ta kwashe da dariya ta ce.
"Sisi Allah ya shirkeyi har yau baki girma ba"
Dariya shima Sadiq ya yi ya ce.
"Rabu da ita zata bari ne ai"
Rufe bakinsa keda wuya sai ga sallamar su Yasir, nan suka baje a falo su bakwai harda Ema da
wani Mujaheed, falon ya gauraye da kamshin turare dana abinci, su Yasir har sun fara had'iye
yawu, suka gaisa da Minal ta mik'e dan kiran Husna, ta cimmata zata fito nan suka dawo tare,
Husna ta gaishe su, daga nan suka shiga kawo musu juices dasu plata, bayan sun gama
had'awa Husna ta zuk'unna zata zuba musu, Uncle ya dakatar da ita ya ce.
"Ki barshi kowa zai zuba iya cikinsa"
Ba musu ta mik'e ta wuce d'akinta, Minal ita ma ta take mata baya.
Sun ci abinci sun sha juice suna santi, shi kanci Sadiq ya yi mamakin yadda Husna ta iya tsara
abinci haka, duk kallon da yake mata bata gama iya komai ba yana mata kallon k'aramar
yarinya, su Yasir kuwa an saki ciki sai lodi suke yi, duk abin da ta kawo sai da suka ci. Hatta
miyar kub'ewa wanda ta yiwa Sadiq sai da suka ci shi bayan sunci miyan agushi, Yasir harda
cewa a zuba masa sauran fried rice a kula dan ya samu na dare.
A gaskiya sun yaba da kwazon Husna wajen girki wanda suka yi ta ma Abokinsu barka da
samun Husna matsayin matarsa, Sadiq yaji dad'i sosai da farin cikin Husna ta fidda shi kunya,
har Allah-Allah yake su tafi dan ya mata albishir na tukwicin farin cikin da ta sanya shi.
A nan suka yi sallan la'asar a masallacin unguwar su Sadiq, sai misalin k'arfe shidda na yamma
suka tafi, Mujaheed ya d'auki Minal a motarsa dan ya sauketa a gida, daga nan kuma soyayya
ya kullun a tsakanin su.
Bayan sallan isha'i Husna ce sanye cikin riga da wando English wears, sun kamata sosai, ta yi
mild make up, tayi kyau abin ta, falo ta fito ta zauna ta soma kallon Arewa24, Sadiq ya fito daga
d'akinsa sanye da wando tree quarter sai riga ta shan iska mai guntun hannu, k'arasowa ya yi
cikin sanda yaje ta bayan kujerar da Husna ke zaune, wanda gaba d'aya ta tattara hankalinta
tana kallon TV, hannu yasa ya rufe mata ido da k'arfi, aiko zabura ta yi ta tsandara ihu, Sadiq ya
ke ce mata da dariya har yana kyalkyatawa yana rike ciki, b'ata rai ta yi tana hararansa harya
k'araso kusa da ita ya jawota jikinsa.
"My Husna sarkin tsoro, zanga ranar da zaki girma da yin ihu"
Kukan shagwab'a ta shiga yi masa harda hawaye tana dukansa a k'irji, murmushi ya yi.
"Husna ta ki yi hak'ura ba zan sake ba"
D'ago fuskanta ya yi yana kallon kwayan idonta wanda yake cike da hawaye, murgud'a masa
baki ta yi ta kauda kai gefe.
"Ni kike murgud'a wa baki? aiko yanzu zanyi maganin sa"
Kama bakinta ya yi ya sanya hannu ya murd'e su ta saki k'ara min k'ara.
"Kai Uncle, Allah da zafi fa"
"Tom sorry My Husna, bari na ba shi magani ya daina zafi"
Kan ta yi magana ya fincikota ya fad'a bakinsu guri d'aya, sun kai tsayin minti goma kana ya
saketa suna mai da numfashi da sauri, ta mik'e ta ruga d'aki da gudu tana haki, binta ya yi da
kallo yana dariya. Shima mik'ewa ya yi ya isa d'akinsa, Alwala ya yi kana ya sauya kayansa
zuwa jallabiya milk color, ya fito ya nufi d'akin Husna wacce ita ma ta sauya kaya zuwa kayan
barci maroon color, binta ya yi da kallon sha'awa ya ce.
"My Husna zo muje d'akina in nuna miki wani abu"
D'agowa ta yi da hararen wasa.
"Ni barci zanyi"
"Haba sweet Husna, ki yi hak'uri muje in nuna miki"
Ya marairai ce fuska kamar zai yi kuka, dariya ya bata ta soma kyalkyatawa, dama burinsa
kenan ya sata dariya dan ta daina fushi da shi, yad'aukar mata zani da hijab suka wuce
d'akinsa. Alwala yasa ta ta yi, ba musu taje ta yi da yake ya sabar mata da kwanciya da alwala,
bayan ta fito taga ya shinfid'a dadduma da mamaki ta ce.
"Uncle Sallah za mu yi ne?"
"Eh Nafila za mu yi dan godiya ga Allah daya had'amu aure bisa raya sunnar Monzon Allah
S.A.W. murmushi ta yi bata kawo komai a ranta ba, ta d'aura zani tare da sanya Hijab suka tada
Sallah.
[11/3, 10:00 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 59 ~ 60_*
Bayan sun idar da Nafilar, ya yi mata nasihohi da jan hankali game da zaman takewar aure,
sannan ya dafa kanta ya karanto addu'o'i kamar yadda Manzon Rahma ya koyar damu s.a.w.
bayan sun gama sai suka mik'e duk suka k'ara shirin kwanciya suka kwanta, Sadiq ya rage
hasken fitilar d'akin. Ganin haka nima sai na yi musu fatan alkhairi na yo waje na nufi gidan
Dady.
*******
Dady da Momy zaune suke a falo, Dady yaba zaune saman Cushing, Momy na durk'ushe a
gabansa ta gurfana kamar mai rok'an gafara, Dady ya ce.
"Habeeba a yau zaki girbi abin da kika shuka, na san zaki ga na yi miki shuru kamar abin bai
dameni ba ko? hmmm, to ina sane da komai, na bari ne in samu nutsuwa sosai kan sanin wani
hukunci ya dace na yanke miki, dan haka nagode da duk makirci da abubuwan da kika ai kata,
ni ba ki yi min komai ba kanki kika yi mawa, ki sani dai duniya fararra k'ararre ne, kuma duk abin
da ka shuka hak'ik'a zaka girbe shi imma khairan ko sharri, ni duk abin da kika min da wanda
kika wa Husna duk na yafe, amma fa ki sani zamana dake ya k'are"
Wani irin razana Momy ta yi, ta d'ago kai a firgice ta d'aura hannu bisa kai.
"Na shiga uku Alhaji kamin rai karka gutsire igiyar aurenmu, wallahi na tuba na sauya halina ba
zan sake kamanta haka ba, ka yafe min"
Kallon k'ask'anci Dady ya yi mata.
"Zan so ki tuba d'in, sannan Allah yana son mutum mai amsan laifinsa kuma da niyyar ba zai
zake saba masa ba har iya k'arshen rayuwarsa, dan haka na riga na yanke igiyar aurena dake
har guda biyu, ga takardar saki a rubuce, na sake ki saki biyu, in kin gama idda ki samu miji kiyi
aure"
Kuka Momy ta saki, ta kasa karb'an takardar, Dady ya ajiye mata a k'asa, ya cigaba da kallon
TV abin sa, kuka take kamar ranta zai fita, yau nadama ya shiga zuciyarta da dana sanin abin
da ta aikata, yau taga sharrin bin boka da tuggu, duk gasu ba su yi mata rana ba, bayan ta yi
kuka ta gaji ta sassauta kukan tare da share hawayenta ta ce cikin dishewar murya saboda
tsabar kukan da tasha.
"Alhaji ina niman ya fiya a gunka tare da alfarman zanyi zaman idda a d'akina, har zuwa lokacin
da ya cika sai in tafi"
Tana kaiwa nan ta tsaya don jin me zai ce, har azuciyarta ta yi amfani da hakan ne domin ta
samu hanyar da zata shawo kansa su shirya, kan ta gama iddan ta samu ya maidata d'akinta
domin akwai sauran igiya d'aya. Dady shuru ya yi na mintuna daga bisani ya ce.
"To shi kenan zaki iya zama ki yi idda, domin musulunci ma ya yarda da ayi hakan, dan haka ki
yi zaman idda a d'akinki, in kin gama sai ki tafi"
Yana kaiwa nan ya mik'e ya wuce part d'insa ba tare da ya k'ara waiwayen inda take ba,
hawaye masu zafi suka sauka kuncinta, tana tuno irin abin da ta yi da kuma dana sani akan
aikatasu da ta yi. Haka ta mik'e ta wuce d'akinta rik'e da takardar saki, ta fad'a kan gado ta k'ara
kecewa da sabon kuka.
Haka dai gidan Dady suka kwana ko wanne da irin damuwansa. Sab'anin gidansu Sadiq da su
ka yi kwanan farin ciki.
****** ******
*Washe gari*
Da asubahi Husna tana kwance ta k'udun dune da bargo, shi kam Sadiq yana gabatar da Sallar
asubahi, ya idar ya zauna yana lazumi, Husna na kallonsa hawaye na zuba mata na farin ciki,
hakanan taji son mijinta na ratsa duk kan b'argon jikinta, tana tuno abin da ya faru a daren jiya,
sai taji ta cintsi kanta da murmushi tare da hawaye, hak'ik'a Allah ya bata Miji d'aya tamkar da
dubu, ko da dai tasha wuya sosai amma ya rangwanta mata saboda tsananin tausayinta da ya
ke yi. Tasowa ya yi ya k'araso wurin gadon sai ta yi sauri ta runtse ido kamar mai barci,
murmushi a kan fuskansa ya fara kiran sunanta a hankali, motsawa ta yi sai taji wani azabar
zafi ya ratsata da sauri ta bud'e ido tare da fad'in wash, cikin kulawa ya ce.
"My sweet love ta shi kije ki yi wanka ki zo ki yi Sallah, kinga lokaci yana tafiya"
Shagwab'e fuska ta yi ta fara rera kuka, matsawa ta yi sosai kusa da ita wanda har tana jin
hucinsa, ya ce.
"My sweet Husee menene kuma?"
Bata tanka shi ba ta muskuta gefe tana mai runtse ido na azaba, domin duk yadda ta motsa sai
taji zafi na ratsata, ta mik'e da kyar tare da bargon data cikwi kwiye jikinta da shi ta fara takawa
a hankali dan ta isa bayi, murmushi ya bita da shi ya mik'e cikin azama ya cimmata, d'aukarta
ya yi cak ya shige da ita bayi tana wutsil-wutsil. Da kansa ya gasata ya mata wanka, sannan
yana kallonta ta yi wankan tsarki, ya kuma d'aukarta ya dire ta a gefen gado, d'akinta yaje ya
d'auko mata jallabiya bak'a ya kawo mata, haka ta zura ta mik'e tana dingisawa ta sanya hijab
ta tada sallah, bayan ta idar ta haye kan gado dan huta gajiyar jiya.
A Ranar Sadiq ya sha shagwaba duk inda ta motsa idonsa na wuri, hatta abinci shike bata a
baki, sai wani narke masa take yi, Sallah ma a gida ya yi bai iya fita masallaci ba, shi ya ja musu
jam'i, ko nan da can bai iya motsawa suna tare, ko da Husna na jin kunyarsa, ta dan saki jiki
sun sha soyayyar su mai cike da So da K'auna. Sadiq har mamaki Husna take ba shi yadda
take da jarumta da juriya, sannan ko wani salo ya koya mata tana rik'ewa a kanta, wanda take
azamar ta yi masa dan ta sanya shi farin ciki.
***********"
*Bayan wata d'aya*
Husna ta soma sabo da rayuwar aure, wanda yanzu ta saki jiki ta k'ara fahimtar ya aure yake da
abubuwan da suke ciki, tana iya k'ok'arinta wajen farantawa mijinta rai, ta aje sunan Uncle ya
dawo sunan Miji yanzu, abinci kala-kala tana k'ok'arin yi masa, gyaran gida da duk wasu abu
tana k'ok'arin gyarawa, a b'angaren shinfid'a ma tana k'ok'ari domin ta soma sabo da sabar
rayuwa da ta tsinci kanta a ciki, kuma Sadiq yana yaba mata saboda juriyarta. Sun zama hanta
da jini, duk wani abu tare su ke yi in dai yana gida, shak'uwa mai k'arfi ya shiga tsakaninsu ko
aiki yaje suna manne da juna a waya, Soyayya suke yi sosai wanda duk wanda ya gansu zai yi
tunanun sun shekara da zama tare. Sadiq ya kanyi mamakin yanda Husna ta kware wajen yi
masa abubuwa sosai, ga ta dai da k'ank'anin shekaru amma sai kace babbar Mace. Abin da
Sadiq bai sani ba shi ne a kullun in ya fita aiki, takan saurari kaset na wa'azi kan zamantakewar
aure da yadda Mace zata tarairayi Mijinta, in ta kammla aikin gidanta kuma takan hau
WhatsApp group d'in *Anty Rahma* ta samo ilimi akan sirrin rik'e miji a wajen Matan *Sirrin 'ya
Mace group*. A wajen girki kuma tana samun ilimi sosai a group d'in *Nana diso kitchen* wajen
sarrafa abinci kayan ciye-ciye da sauran juices da drinks. Da yawaita karatun lissafan Addini na
gyaran Ibada dana gyaran jiki. Wannan sune sirrikan da Husna ta rik'e take samun ilimi wajen
faranta ran mijinta har ta kware sosai.
******* *******
*Bayan mako guda*
Ranar Juma'a, da dare su Sadiq suna falo, Husna ta d'aura kanta a kan ciyarsa yana wasa da
gashin kanta wanda yasha gyara, hira suke yi kasa-kasa na masoya wanda baka iya jiyo
hiransu. Kira ne ya shigo wayarsa wanda ya katse musu hirar, ya sanya Husna ta d'auko masa,
ganin sunan da ya bayyana a kan phone d'in yasa shi fad'uwar gaba, da sauri ya d'auka ya kara
a kunnensa ya ce.
"Abbana ina yini"
D'ayan b'angaren aka hau masifa.
"Ban sani ba, yanzu kai Sadiq ka zama mara mutunci ko? tunda aka maka fad'a kusan wata uku
kenan kak'i ka waiwayo gida ko, ka nuna mana bamu isa da kai ba ko?"
Risina wa Sadiq ya yi kamar Abban na kallonsa, ya ce.
"Abba ka yi hak'uri wallahi aiki ne yasa ban zo ba, amma Insha Allah zan zo"
"Rufe min baki sakaran banza kawai, to ina so ka sani gobe-goben nan in Allah ya kaimu ka
taho Kaduna, mutumin wofi"
Gaban Sadiq ya shiga fad'uwa ya ce cikin rawar murya.
"Abba ayi min hak'uri zuwa mako mai zuwa insha Allah zan zo"
"Naki na bari mako mai zuwa d'in, Allah ka kiyaye ni fa tunkan musa k'afan wando d'aya da kai,
in Allah ya kaimu gobe na ce ka zo, in ba haka ba wallahi ranka sai ya yi mummunar b'aci"
Ya kashe wayar ba tare da jin amsar da Sadiq zai ba shi ba. Gumi ne ya ketowa Sadiq gaba
d'aya zuciyansa ya dagule, yana tunanin ta ina zai fara, Husna duk tana jin maganar da suka yi,
da yake Abban na magana da k'arfi, matsawa ta yi kusa da shi ta dafa shi ta ce
"Sweet hubby me yake faruwa ne?"
Nan Sadiq ya goge zufan da ya karyo masa a goshi.
"Sweet Husee, Abbana ne ya kira ni, ai kin ji maganar da mu ka yi da shi?"
Ta gyad'a masa kai alamar eh ta ce.
"To Baby muje mana, ashe dama ba a nan Kano suke ba? wallahi ni har na ji dad'i zamu
Kaduna, dama ban tab'a tafiya mai nisa ba, kullun ina Kano"
Ta karasa maganar cikin shagwab'a, murmushi ya yi wanda ya tsaya iya kan leb'e ya ce.
"Husna ba zaki gane ba, akwai babban matsala ne"
Husna ta zaro ido kamar zasu yo waje.
"Matsala kuma?"
Ya gyad'a mata kai, nan ya jawota jikinsa ya shiga bata labarin shi da asalinsa, da duk abin da
ya faru har ya zuwa aurensu, hak'ik'a Husna ta razana da wannan labari, d'ago ido ta yi wanda
suke zubar hawaye.
"Yanzu uncle rabamu za su yi ko?"
Sadiq ya k'ara matseta a jikinsa.
"Ina, babu wanda ya isa ya rabamu sai Allah, ki kwantar da hankalinki komai zai yi dai-dai."
K'ank'ame shi ta yi tana kuka a hankali mai kashe zuciya. Sadiq ya sumbaci kanta yana lalla
shi, a ransa ya na jin, ko kashe shi za su yi wallahi ba zai iya rabu da matarsa ba domin ita ce
rayuwansa.
[11/4, 7:01 AM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 61 ~ 62_*
Washe gari da sassafe suka ta shi suka shirya, babban trolley biyu suka sanya kayansu a ciki,
sunyi wanka sun shirya Husna ta sanya a tamfa dark blue mai kwalliya yallow, fari da baki, riga
da siket d'inkin fitted, ta sanya farin gyale da bak'in takalmi da jaka, sai sarka da dan kunne
silver color, ta d'aura bakin agogo a hannunta, ta yi kyau sosai ko da ba wani kwalliya ta yi sosai
ba. Sadiq shi kuma ya sanya yadi sky blue ya sanya hula da takalmi bak'i sai agogo ash color,
ya yi kyau shima sosai. K'arfe takwas na safe da 'yan mintuna suka fito, sallama suka yi da mai
gadi kana suka kulle part d'insu suka wuce gidan Dady.
Bayan sun isa, ya yi parking mota a k'ofar gida suka shiga cikin gidan, sun gaisa da Baba mai
gadi sannan suka k'arasa cikin gidan, sun hango Dady da Baba Husain zaune bisa babban
dadduma a wata 'yar baranda dake cikin gidan, da murmushi a fiskokinsu suka isa wajensu,
zama su ka yi kana suka gaisa Dady ya k'urawa Husna ido saboda wani girma da kyau data
k'ara, dan tunda aka yi auren ya hana Sadiq ya kawota wai sai ta yi 2 months, yanzu ma ya yi
mamakin ganinsu da safe haka, su Sadiq suka wuce part d'in Inna suka gaisa kana suka fito,
nan ya zayyana masu Dady tafiya ce ta kamasu zuwa Kaduna sati d'aya zasu yi su dawo, su
Dady suka yi musu Addu'a kana ya k'ara yi musu nasiha sannan ya ciro bandir d'in kud'i na
dubu ashirin ya bama Sadiq da su sha mai a mota, ya amsa cikin girmamawa ya yi godiya kana
suka yi sallama suka tafi cike da farin ciki. Baba Husain yana yaba natsuwar Sadiq da
kyawawan halayyarsa,