Showing 15001 words to 18000 words out of 81944 words

Chapter 6 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2384

da maimaita kalmar.

'Zainab ta wace'

A cikin ransa. Nuhu ma yabi bayan Khalil ba tare da ya k'ara furta komai ba. Yaya Al'amin ya kai
dubansa ga Zainab cikin d'aga murya ya daka mata tsawa.

"Maza ki had'a kayanki mu tafi Kaduna do min yau sai kowa sunji wannan bak'in labarin"

A tsorace jikinta na rawa ta d'auki hand bag d'inta tana kuka ta fita, key d'in d'alin ya amsa ya
kashe duk kayan wutan d'akin ya rufe kana ya nufi motarsa tana biye da shi a baya. Haka suka
kama hangar Kaduna ba shiri, Zainab banda kuka babu abinda take yi har suka isa kaduna

********* *********

*Kaduna*

Direct gidansu ya wuce da ita ya yi sa'a duk mutanan gidan suna nan, daya ke ranar weekend
ne, har Yaya Ismail yazo da matarsa, sai Anty Binta itama da tazo yinin gida, Yaya Aliyu shima
yana gida bai fita kasuwa ba, Baffa ma haka, Umma dama da Anty Jidda kullun suna gida.

Da salama ya shiga falon ransa a b'ace duk suka amsa cikin fara'a, ganin yanda fuskarsa yake
yasa suka fara tambayar sa ko lafiya, duk hankalinsu ya tashi tunaninsu ko wani abu ne ya
samu iyayan nasa.
Wuri ya samu ya zauna ba tare da ya amsa musu tambayoyin da suka jero masa ba, sun gaisa
gaba d'aya, Yaya Aliyu ne ya ce.

"Kai wai lafiya muka ganka cikin wannan yanayin? Da fatan dai ba wani abu bane ya faru dasu
Baffa?"

Murmushi ya yi wanda yafi kuka ciwo ya ce.

"Ba komai daga Zaria nake yanzu haka ko gida banje ba nan na tawo"

Baffa ne ya ce.

"To da fatan ba Zainab d'in ba ce ba tada lafiya?"

Murmushi ya kuma yi.

"Tare da ita nake, yanzu haka tana waje taki shugowa, Ku barta in ta gama nuk'u nuk'unta zata
shigo"

Yana gama wannan bayanin yaja bakinsa ya yi shuru. Anty Jidda, Anty Binta, Anty Ameena,
mik'ewa suka yi dukansu suka nufi farfajiyar gidan suga me ya hanata shigowa.

Bayan su Anty Binta sun fita, sun sameta a zuk'unne tana kuka mara sauti hawaye kwance a
kuncinta, anty Jidda ce ta tada ta tsaye ta ce.

"Zainab lafiya meyasa baki shigoba?"

"Yar uwa lafiya? ina ganin mu shiga ciki tukunna, sai mu saurari duk kanin bayani wajen
Al'amin"

Cewar anty Ameena. Shawaran ta suka d'auka, sai suka d'unguma zuwa falo. Suna shiga suka
samu wuri duk suka zauna, Zainab kusa da Umma ta zauna sai kuka take yi, ta kai kusan minti
biyar a haka, k'aran fanka ne ke kad'awa sai kuma sautin kukanta, sannan ta tsagaita kukan ta
gaida su Baffa da sauran wanda suke falon. Yaya Aliyu ne ya kai dubansa ga Al'amin ya ce.
"Al'amin gata ta shigo kai muke saurare"

Ya yi murmushi da gyaran murya, ya fara basu labari tun daga lokacin daya fara samun sauyi
ga Zainab, har zuwa yau daya ga su da Khalil a dakinta, Duk suka fara salati. Wannan labari ba

k'aramin tada hankalinsu ya yi ba tare da mamaki, Umma ce tabce.

"Haba Zainab duk iya tarbiyar da muka baki, ki rasa wanda za kiyi abota da su sai maza, shin
ma su waye wannan rayan? wanda a sani na dake ko kawaye mata baki da su a nan balle ma
ace maza"

Baffa ne ya cab'e maganar da cewa.

"Amma Zainab kin bani kunya kuma kin bani mamaki, banyi zaton haka daga gareki ba, waye
wannan yaron da har yake ik'irarin ke tashi ce?"

Kukan Zainab ya k'aru ta ce.

"Dan Allah Baffa ku yafe min nasan na yi kuskure, amma dan Allah Karku rabani da Khalil
wallahi a yanzu shi ne zab'in zuciyata, in kuka ce zaku rabani da shi kamar zaku rabani da
rayuwa ta ce, na riga na yi sabo da shi

Kukanta nata ya sirk'eta sai ta kasa k'arasa maganar. Yaya Ismail ne ya mik'e cikin fushi ya fara
fad'a yayo kanta kamar zai mareta, da sauri Al'amin ya tare shi da cewa.

"Yaya Ismail bai kamata ka duketa ba"

Ya koma ya zauna yana huci. Anty Jidda ta ce.

"Kwarai bai kamata a ce za'a bigeta ba, ai Zainab ta wuce duka, dan haka ke muke saurare ki
bamu labarin yadda aka yi kika yi sabo da shi Khalil din"

Share hawayenta ta yi ta soma bayani tun daga farkon haduwarta da Khalil har zuwa ranar yau,
sai dai bata gaya musu cewa sunyi maganar da Anty Jidda ba, ita kanta Anty Jidda taji dad'in
yanda Zainab bata sanya ta ciki ba. Kuka ne ya sirketa ta cigaba da rerawa. Yaya Aliyu saboda
damuwa ya kasa magana haka ma Baffa, Umma ko tagumi ta rafka, su Anty Binta ko shuru
suka yi kamar ruwa ya cinye su, Al'amin kuwa sun kunyar da kai ya yi kasa zuciyar sa na masa
rad'ad'i. Yaya Ismail ne ya mike ya zare belt din dake jikinsa, ya nufota, da sauri ta mike jikinta
na rawa ta fara ja da baya tana fad'in.

"Yaya dan Allah ka yi hakuri karka bigeni ba zan sake ba na tuba"

Da taga dai dagaske yake yi sai ta arce d'akinta a guje, tana k'ok'arin rufe k'ofa ne ya banko
k'ofar ya fara zuba mata belt d'in, dukanta yake kamar zai kashe ta, da sauri su Anty Binta suka
k'araso suka ceceta.

"Isma'il ai ba duka ya kamata ayi mata ba, tunda Zainab ba yarinya bace, kamata ya yi a bi abin
a hankali"

Anty Amina ce ta ke fad'ar haka. Yana huci ya bar d'akin, kusa da ita suka zauna suna
lallashinta, A falo kuwa su Baffa suna cike da jimami, a nan dai suka tattauna maganar kana ya
ce.

"Al'amin ya sanar da Baffa Sani yana son ganinsa da daddare, da haka falon ya watse cikin da
damuwa.

*******

*ZARIA*
Khalil ne kwance cike da damuwa yana ganin kamar an raba shi da Zainab kenan, yana ta juyi
a kan gado ya dafe kansa, can sai ya barke da kuka, Nuhu ne ya ke lallashinsa.

"Haba Abokina kamar ba namiji ba, ka yi hakuri ka amsa k'addararka, mu cigaba da Addu'a, in
Zainab matar kace duk yadda zasu so rabaku in Allah yanu fa sai ka aure ta"

Idonsa ne ya dago wanda suka yi jajir saboda tashin hankali ya ce.

"Ni bana tunanin zasu iya barinmu mu cigaba da soyayya, ina ganin kamar wannan tafiyar da
suka yi da ita sunyi sanadiyyar da zasu raba mu ne, domin na lura family d'insu suna da wani
tsastsauran ra'ayi, nasan dai Zainab tana sona ina sonta, sannan shi wannan Al'amin d'in da
kake gani shi ne wanda iyayenta suka zab'a mata a matsayin mijinta, a lokacin suna musu
kallon soyayya suke yi wanda ita soyayya take masa na 'yan uwantaka saboda Zainab a kaina
ta fara sanin so, haka nima a kanta ne na fara sanin so"

Nan dai Nuhu ya cigaba da ba shi baki akan ya yi hakuri, yaso ya bita amma Nuhu ya hana shi.

"Ka kwantar da hankalin ka, kaga yau asabar dole ta dawo gobe insha Allah, in kuma bata
dawo ba dole ta dawo Monday dan suna da lectures kuma ita ma tasani, kuma ni ina ganin ba
zasu tab'a yanke mata karatunta ba, saboda ta yi nisa tunda a yanzu muna shirin zana exam ne
na last semester"
Dole yasa Khalil ya yi hakuri ya mik'a lamarin ga Allah.

Da daddare duk sun hallara a falon gidan har dama wasu dattijai na family d'insu duka, bayan
sun gaisa ne, sai Baffa ya umarci matan dasu basu guri zasu tattauna, haka Umma ta tattara
surukanta suka koma falon d'akinta suka cigaba da hira, Zainab dai na takure ba um ba um um,
kusan kowa ya fita harkanta saboda su Anty Jidda sunyi lallashin har sun gaji taki cin abinci sai
kuka da take yi.

A falo su Baffa sun tattauna sosai wanda daga k'arshe suka yanke hukunci akan.

*Rahma ce*
[10/17, 11:19 AM] Rahma Kabir🌺: *KAƊAICI*

© *Rahma Kabir*

*Wattpad:*@rahmakabir


*_Page 13 ~ 14_*

A falo su Baffa sun tattauna sosai wanda daga k'arshe suka yanke hukunci akan cewa tunda
Zainab zata zana jarabawa to sun sanya auren ta da Al'amin nan da wata d'aya, lokacin ta
kammala jarabawa da sati d'aya za ayi bikin. Baffa ya sanya aka kira su Umma, nan ya fada
musu abin da suka yanke, sannan suka d'aura da yi mata fad'a sosai, daga k'arshe suka d'aura
da nasiha, Zainab ce ta mike cike da tashin hankali ta sanya hannu a bakinta ta rufe gudun kar
kukanta ya fito, da gudu tabar falon tana kuka mai tsuma zuciya. Haka dai taron ya watse wasu
najin dad'i wasu kuma suna cike da damuwa.

Zainab da Khalil yanda suka ga rana haka suka ga dare ba wanda ya iya runtsawa, Khalil ya
kira ta a waya yafi a k'irga amma wayar a kashe.

****** ******

*Washe gari.*
Da yamma Yaya Ismail ne cikin shirin komawa Kano tare da matarsa, sun kammala shirinsu
sannan suka taru a falo aka k'ara yiwa Zainab fad'a sosai, sannan aka bata kud'i da sauran abin
buk'ata, tare suka tafi da Yaya Ismail zasu sauketa a makarantarsu. Tun a hanya yake mata
nasiha har suka kai cikin makarantar, parking ya yi suka rakata har d'aki sannan suka juyo suka
kama haryar Kano.

Khalil yana ganin saukarsu a mota, sai ya gyara zama yana jiransu Yaya Ismail su tafi. Sai da
yaga k'ulawar motar su sannan ya nufa d'akin nata, bugu d'aya ya yiwa k'ofar ta zo ta bud'e
masa ya shiga, zama suka yi suna kallon juna, Zainab ta katse shurun ta gaida shi, ya amsa
cike da kulawa, daga bisani ta d'aura da ba shi labarin duk abin da ya faru da suka isa gida har
da dawowarta yanzu. Hawaye ne mai zafi yake fita a idon Khalil.

"Zainab kin amince zaki rabu sani?"

Cikin shasshekar kuka ta ce.

"Khalil ya zanyi kaga dole yani musu biyayya"

"Shi kenan tunda kin zab'i rabuwa dani"

Bai jira mai zata ce masa ba ya mik'e ya isa bakin k'ofa zai fita, da sauri Zainab ta je da rike
rigansa ta baya.

"Ba zan iya rabuwa da kai ba Khalil ina sonka, mafita zaka samar mana, na dank'a maka
ragamar rayuwa ta"

Fuskarsa cike da hawaye ya juyo da murmushi, hab'arta ya d'ago suna kallon juna.

"Dagaske kin yarda in samo mana mafita?"

"Eh na amince"

Murmushi ya yi ya cire farin hankacif ya guge mata hawayenta sannan ya goge nashi, ya kama
hannunta ya kaita har zuwa bakin gado ya zaunar da ita, ya zuk'unna a gabanta, ya shiga bata
magana mai kwantar da hankali, cikin kankanin lokaci ya fara sanya ta dariya har ta soma
mancewa da damuwar da take ciki, ganin hakane yasa ya mike ya ce.
"Zan tafi kano yanzu ki sanya ni a Addu'a"

"Meyasa zaka tafi?"

"Saboda ke zan tafi, zan sanar ma iyayena domin su zo su nima min auren ki"

Cike da jin dadi ta k'arfafa masa gwiwa da maganganu masu dad'i, kana ta yi masa Addu'a ya
wuce.

****** ******

*KANO*

Sai bayan magarib Khalil ya isa Kano, direct gidansu ya wuce yaje ya samu Baba Husain da
Inna, ya yi musu bayanin maganar daya kawo shi, cike da mamaki Baba Husain ya kalle shi
saboda bai taba tsammanin zancen aure daga bakin Khalil ba, fad'a ya fara yi masa sannan ya
nuna rashin amincewarsa, haka Inna ma fad'an ta yi masa ta goyi bayan Baba Husain, Khalil na
kuka yana musu magiya amma fir suka k'i amincewa k'arshe ma Baba Husain kuka ya sanya
yana cewa.

"Saboda kaga bamu muka haifeka ba shiyasa zaka k'i bin umarnin mu ko, na d'auke ka d'an ciki
na amma kai ka nuna mana bamu isa da kai ba"

Cike da tashin hankali Khalil ya fara basu hakuri da amincewar ya janye maganar kuma ba zai
sake yi musu shi ba, Baba Husain yaji dad'in haka, dama ya yi masa kukan ne saboda ya janye,

lallashinsa suka yi tare da nasiha, ya mik'e ya yi musu godiya. D'akinsa ya shiga ya zauna, kuka
ya k'are masa sai ajiyar zuciya, tunani yake yi shin ta ina zai bullowa lamarin? Mikewa ya yi a
zabure ya lek'o, sai da ya tabbatar ba kowa a tsakar gidan ya lallab'a ya fita saboda karsu hana
shi komawa Zaria a ranar, tasha yaje ya hau motar Zaria, basu suka isa ba sai goma da rabi na
dare.

Direct makaranta ya nufa, harta kwanta taji ana buga mata kofa, da kamar baza ta bud'e ba sai
ta mik'e ta isa bakin kofar ta ce

"Waye ne?"

Cikin dishewar murya ya ce mata.

"Khalil d'inki ne"

Da sauri ta bud'e k'ofar ya shigo, binsa da kallo ta yi cike da mamaki.

"Baka samu zuwa Kano din bane?"

guntun murmushi ya yi.

"Naje yanzu na dawo ko gida ban isa ba nan na duro"

Kallon mamaki ta bishi da shi, wuri suka zamu suka zauna, cike da damuwa ya fara bata labarin
zuwansa Kano da yadda suka kwashe da iyayensa, kuka ne ya kubce musu baji ba gani, da
kyar Khalil ya iya lallashin kansa sannan ya rik'a lallashinta da kalamai masu dad'i, Nuhu ne ya
buga kofar d'akin, Khalil ya mik'e ya bud'e masa. Kafin ya yi masa magana ya ce.
"Haba Khalil tun d'azu ina nimanka ashe kana nan, cewa na yi bari nazo na duba ka ko kana
nan"

Murmushi ya yi masa sannan ya c.

"Zauna abokina yi hakuri wallahi bana cikin nutsuwa ne"

Zama suka yi Khalil ya bashi labarin halin da suke ciki, damuwa ne ya bayyana a fuskan Nuhu
ya shiga basu hakuri, sannan ya ce.

"Akwai mafita d'aya da zan baku kuma ita ce dama ta k'arshe da zaku yi amfani da shi, amma
fa sai kunyi min alkawarin kun daina kuka, kun cire damuwa akai sannan kun mai da hankali
akan karatunku har mu kammala exam, sannan kuma ku dage da Addu'a"

Cikin sauri dukansu suka ce sun amince da hakan, Nuhu yayi murmushi ya ce.

"Ku matso kuji"

Nan suka matsa ya yi musu bayanin komai, bayan ya gama, murmushi ne ya ziyarci fuskokinsu
da alama dai sun gansu da bayaninsa.

*******
Tun daga wannan rana Khalil da Zainab suka saki jiki, sun mai da hankali sosai wajen
karatunsu. A bangaren Kaduna kuwa shirye-shiryen biki suka yi ba kama hannun yaro. Ta
bangaren Kano kuwa su Baba Husain sun saki jiki da tunanin Khalil ya hakura da zancen auren,
tunda suka ji shuru kuma suna waya bai sake d'auko musu zancen ba.

*****
Ranar Juma'a ya kama ranar ne su Khalil suke kammala exam d'insu, sun fito paper da misalin
11 na safe Zainab tana d'akin ta, da yake ita tun ranar labara ta gama nata exam d'in, zaman
jiran su Khalil take su kammala nasu. Khalil ne ya shigo d'akin cikin shigar manyan kaya shadda
sky blue yasha aiki tare da sanya hula bak'ar dara da takalmi bak'i, agogo golden ash, yayi kyau
sosai. Ya zamu Zainab ita ma zaune tana zaman jiransu, sanye take da less sky blue mai zanen
fulawa fari, ta sanya babban gyale bak'i da takalmi da jaka farare, sai kamshi take yi kamar
Amarya, ta yi kwalliya sosai ta yi ta kyau. Khalil kafeta ya yi da ido yana k'are mata kallo gaba
daya hankalinsa baya jikinsa, a ransa yana yaba kyau da Allah ya yi mata, Nuhu ne ya lek'o
yana cewa.

"Haba Khalil kun barni tun dazu sai jiranku nake yi a cikin mota ku fito mu tafi mana"

"Gamu nan zuwa"

Khalil yace yana yar dariya. Bayan sun fito mota suka shiga suka fita daga cikin makarantar,
motoci ne na dalibai maza da mata suke biye dasu a baya, har zuwa cikin Zaria city.

Sun yi parking a k'ofar wani gida inda Khalil ya fito shi da Nuhu, suna k'ok'arin yin sallama a
gidan sai ga wani Dattijo ya fito daga cikin gidan sanye da manyan kaya da alkebba, suka
tauguna suka kwashi gaisuwa, yanda Malamin ya amsa da alama ya san su, ya ce.

"Khalilu har kun iso?"

"Eh Malam mun iso"

"To masha Allah, Ina ita yarinyar take?"

Nuhu ya ce.

"Tana cikin mota"

"Madallah, to sai ta fito ta shiga cikin gidan ko"

Cikin hanzari Nuhu ya kirata tare da sauran students mata da suka rakosu, suka gaida Malam
sannan suka shiga cikin gidan, sun samu mutane a ciki ba laifi yara nata wasa, wasu nata cin
abinci da alama dai wani k'aramin shagali a ke yi, sun gaisa da matan gidan aka ware musu
d'aki na musamman suka shiga ciki, abinci ne aka kawo musu.
A waje kuwa Malam Isah mai hadisi ne da tawagarsa, suka tsallaka babban masallacin dake
kallan gidansa, mutane sun fara taruwa don gabatar da sallar Juma'a, suma su Khalil duka
shiga ciki. A haka dai jama'a suka taru sosai har a wajen masallaci kana aka gabatar da sallar
Juma'a.
Su Zainab suna ciki, banda fad'uwar gaba babu abin da take yi sai Addu'a da tasbihi, hakanan
taji hankalinta ya tashi, sauran friends d'in ta ne suka ci abinci suna ta hira amma ita ta kasa cin
komai sai kallonsu take yi. Tana cikin wannan yanayi ne, suka ji sanarwar an d'aura auren
Zainab da Khalil bisa sadaki dubu Hamsin lakadan ba ajalan ba. Gabanta ne taji ya fadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login