Showing 39001 words to 42000 words out of 81944 words

Chapter 14 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2401

shi nan ki shirya"

Sai ya barta a nan ya shiga toilet dinsa ya shiga ya gyarawa, sannan ya fesa turaren ba yi, ya
dauki pant d'in data cire yasa a bak'ar leda, sannan ya kwaso mata kayanta ya fito dasu falo,
wani babban leda ya zuba kayan sannan ya fito waje ya yarda pant d'in a bola kana ya koma
bayi ya wanke hannunsa ya fito falo.
Ya sameta zaune tana wasa da yatsun hannunta, bak'ar jallabiya ta sanya ta yane kanta da
gyalensa ta yi kyau sosai, wuri ya samu ya zauna yana kallonta fuskarta ta mau ba alamar
wasa ya fara mata bayani kamar haka.

"Husna ina so ki bani hankalinki nan da kyau"

Nan ta tattara natsuwarta gaba d'aya tana saurarensa, kanta yana a sunkuye.

"Ina so ki sani wannan jini ba mutuwa za ki yi ba na balaga ce, shi ake kira da jinin Haila wanda
mace take soma yinsa lokacin data kai balaga, a turance kuma ana kiransa da Menstruation, ko
ace period wato jini ne mace da take yinsa duk karshen wata wasu matan kuma ko fiye da
haka, sannan mace takan d'auki kawanaki tana yi kamar kwana uku, hud'u, ko fiye da haka. A
musulunce dai inya zarce kwana sha biyar to ya fita daga jinin haila ya koma na ciwo, daga nan
sai mace ta yi wanka tsarki ta cigaba da ibada ta nima magani. Dan haka yanzu Sallah, Azumi,
da sauran ibadu sun wajaba akanki, an bud'e miki kundin littafinki na rubuta lada da zunubi.
Sannan akwai sauye-sauye da zaki gani na halittarki kamar fitar gashi a al'aurenki da hammata,

canzawar murya, breast dinki za suyi girma, feelings akan namiji da sauransu wanda a hankali
zaki gane su. Sannan ina so ki sani mistake kad'an sai iya sanyawa kiyi ciki dan mahaifarki ta
fara aiki. Sannan ina gargadinki baki ba wasa da maza ko hannu karki bari namiji ya tab'a miki,
Husna dole ki aje wauta da wasa dan kin girma yanzu"
Nan dai ya yi ta koro mata bayani. Jikinta ne ya yi mugun sanyi har kwalla na fita a idonta, ji
take kamar ba ita ba dan ta tsinci kanta a sabon ya nayi na rayuwa, ya cigaba da cewa.

"yanzu daga yau da kika fara wannan jinin, ina so ki kasance kina k'irga kwanakin har ranar da
jini ya tsaya miki, sai ki zo ki yi wankan tsarki, kuma kin ga yanzu ba zaki yi sallah ba har sai ya
tsaya"

Da sauri ta dago kai tana kallonsu da rinannun idonta da suka kode, saboda kuka, Sadiq ya yi
murmushi.

"Kwarai ba zaki yi sallah ba sai ya tsaya ko baki san haka ba?"

Husna ta gyad'a masa kai alamar eh bata sani ba.

"Ai dama nasan da wuya ki sani tunda ba islamiya kike zuwa na, na tabbata da kina zuwa da ba
zan sha wuyar fahimtar dake ya jinin haila yake ba da hukuncinsa, a gaskiya zan sanya ki
makarantar islamiya dan ki fita daga duhun kai, iyayenki sun kasa sauke nauyin da Allah ya
basu wannan abu ya jima yana da muna, ina tausayin rayuwar ki Husna wannan dalilin yasa
har yanzu na kasa barin gidan nan na fi yarda dana zauna a kano fiye da kaduna cikin ahalina"

Ya kare maganar yana jan k'aramin tsaki, Husna ta cigaba da kuka mara sauti tana tausayin
kanta.

"Husna ba kuka zaki yi ba girma ne ya kama ki, kuma tabbas sai kin je islamiya dan naga ko
sallah baki damu da ki yi ba kuma hakan babbar illace ga rayuwarki, dan na san ko abin da ake
fad'a a cikin Sallah ma baki sani ba"

Nan dai ya yi ta mata nasiha, daga k'arshe ya koma lallashinta har ta yi shuru, ya bata kayanta
gaba d'aya har da wanda ya siyo mata ya ce.

"Tashi ki tafi gida kafin animeki"

Husna ta mike tana yi masa godiya kanta a sunkuye, ta kasa hada ido da shi saboda a yau tana
jin wani sabon kunyarsa yana ratsata. Sadiq ya bita da murmushi harta fice.

Tana shiga gida d'akinta ta wuce ta shiga ba yi, pant d'in da ta cire d'azun ta d'auka ta sanya
aleda taje ta yar a bola, ta dawo ta wanke bayin kana ta fito ta gyara d'akinta ta samu guru ta
zauna ta shiga tunanin yadda rayuwarta ta saura a yau kawai, kuka ta yi mai isar ta kana ta

kwanta barci ya yi gaba da ita.

***
Yau take cike kwana hud'u da fara jinin Al'ada, tunda ta tashi bata ga alamar jini ba ta kara
jinkirtawa na wani lokaci still ba jini, agogo ta duba taga k'arfe 3 na rana tasan Uncle bai dawo
aiki ba, fita k'ofar gida ta yi ta zauna kusa da Baba a kan benci tana jiran dawowar Uncle.

Ba shi ya dawo ba sai karfe Hudu da rabi na yamma, Sadiq yana daga nesa ya hango sai ya
fara murmushi ya san zaman da ta yi shi take jira ya dawo, sai da ta bari ya shiga ya yi parking
kafin ta bi bayansa, a lokacin Baba ya shiga gida dan ya zaga bayi. Husna tana shiga falo ta
samu guri ta zauna tare da gaishe shi, Sadiq ya amsa yana kallonta.
"My Husna ya dai?"

Husna ta yi murmushi tare da sinne kai k'asa.

"Uhum dama abin ne ya dai na zuba tun safiyar yau dana ta shi daga barci ban gani ba"

"Masha Allah yau kwana nawa kenan?"

Husna ta daga kai sama tana cizon yatsarta kamar mai yin tunani.

"Ummm kwana hud'u yau"

"Yauwa kin ga kenan kwana uku ne kwanakin hailarki, yau kwana na hud'u shi ne zaki yi wankar
tsarki, sannan zaki rama sallar asuba, azahar, la'asar, tunda baki wanka da wuri ba kuma
sallolin sun hau kanki tunda jinin ya d'auke tun kafin su. Daga yanzu duk lokacin da kika gama
kina tashi da safe ki yi wankar tsarki kinga sai ki rama sallah asubahi ita kad'ai sai ki cigaba da
sauran sallah in lokacinsu ya kama. Sannan ki sani lokutan suna chanzawa wataran zai iya
daukewa da rana ko safe ko yamma ko dare kan a kwanta, dan haka sai ki zama mai lura da
kyau"

Ta yad'a masa kai alamar ta fahimta, Sadiq ya cigaba da cewa.

"Sannan pantis d'inki ki samu ruwan zafi ki jik'a su sai ki sanya musu omo da gishiri da dettol su
yi kamar minti talatin sannan ki wanke su ki shanya a rana suna bushewa, sai ki adana su ki
cigaba da amfani da su"

Husna ta d'ago kanta suka had'a ido sai ta sunne kai tana dariya k'asa-k'asa, Sadiq ya dauee
fuska.

"Dariyan me kike yi kuma ina miki magana?"

Husna ta sosa keya ta ce cikin muryar shagwaba.

"Uncle ni fa inna cire pant d'in zubar dasu nake yi had'e da always d'in, na d'auka an gama aiki
dasu duka"

Dariya ce ta kubuce masa ya shiga kyakyatawa tare da samun wuri ya zauna, dama tun dazu a
tsaye yake mata bayani, sai da ya yi mai isarsa kana ya ce.

"My Husna sarkin shirme, ko da yake 'yar fari ce ke ban ganin laifinki"

Husna ta yamutse fuska kamar zata fashe da kuka

"Ni fa Allah na d'auka zubarwa ake yi"

"A'a ba zubarwa ake yi ba, cire always d'in zaki yi sai ki ajiye pant d'in ko ki wanke shi a take in
kin cire, sai ki shanya ba sai kin gama tarawa ba kice zaki wanke"

Sai ta mik'e dasauri zata tafi.

"A'a ina zaki kuma? Ai bamu gama magana ba"

"Uncle zan je in ciresu a bola ne tunda ba'a kwashe shararba sai na wanke"

"A'a ki barsu kawai zan siya miki wasu sabbi"

Sai ta dawo ta zauna, nan ya fara mata bayanin yadda ake wankan tsarki kama daga niyya har
zuwa karshe, yana yi tana gyad'a kai alamar gamsuwa, ta shi ya yi ya shiga toilet d'insa ya
had'a mata ruwa a bokiti kana ya ce ta shiga ta yi.

Minti kusan ashirin ta d'auka tana wanka kafin ta fito ta mai da kayan data cire ta fito falon.

"Ki je gida ki chanza kaya sannan duk ki rama sallar dana gaya miki, gobe in Allah ya kaimu zan
siya miki pantis d'in, sannan ki zama cikin shiri inna dawo aiki da yamma zan kai ki makarantar
Ahmad Islamic Academy in yi miki register islamiya ki fara zuwa"

Cewar Sadiq yana kallonta, Husna cike da murna ta yi masa godiya ta wuce gida.

*
Washe gari da misalin k'arfe hudu na yamma Sadiq ya kai Husna Ahmad Islamic Academy, ya
yi mata register ya biya komai, da yake suna da uniform nan suka gwadata aka bata dai-dai
nata har kala biyu, da littafai da komai daya shafi karatunta, yaso ta fara daga aji d'aya amma
Malaman suka ce ta yi girma sai dai zasu sanya ta a aji biyu, lokacin zuwa daga ranar asabar
zuwa laraba da k'arfe hud'u na yamma zuwa k'arfe shiga a tashi. Nan ya musu sallama suka

koma gida.

Wannan shi ne mafarin komawar Husna makarantar Islamiya, ta maida hankali sosai dan ita ma
tana son ta yi karatu sosai. Haka b'angaren boko sun koma hutu ta cigaba da ss1 science class,
nan ma ta mai da hankali saboda kullun Uncle Sadiq d'inta yana mata fad'a da nasiha akan ta
maida hankali domin karatun da take yi shi ne kadai gatanta.

_Sadiq ya zamewa Husna Uba da Uwa😰_
[10/26, 7:38 PM] Rahma Kabir🌺: *_Page 31 ~ 32_*


*Bayan Mako guda*

Da fara zuwan Husna makarantar islamiya. Tun misalin ƙarfe biyar na yamma Dady yake zaune
a farfagiyar gidan bisa kujera yana shan iska tare da karanta jarida, kasantuwar ranar ya kama
weekend, ya yi zurfi a cikin karatunsa har garin ya soma duhu alaman sallar magriba ya kawo
jiki. Sallamar Husna yaji kamar daga sama, da sauri ya jenye jaridar yana duban inda ya jiyo
muryanta, da murmushi a fuskarta ta ƙaraso wurin Dady.

"Dady sannu da hutawa"

Dady ya bita da kallon mamaki, sanye take cikin uniform dÆŠin islamiya, bai amsa mata ba sai
ya je fa mata tambaya.

"Ke yaushe kika fara zuwa islamiya? kuma waye ya sanya ki?"

Husna taji gabanta ya fad'i, ta manta shaf Dady bai san da zancen zuwanta ismaliyya ba, ko
Momy ma ganinta ta yi da uniform ta fita bata ce mata komai ba, tunda yanzu ko ta gaisheta
bata amsawa. Ta dawo daga gajeran tunani ta sosai kai tana sunne kai ƙasa, nan take dubara
ta fad'o mata cikin inda-inda ta ce.
"Ummm Baba mai gadi ne ya sani a islamiyar Ahmad academy"

Mamaki ya kuma bayyana a fuskar Dady.

"Ok, shiga ciki ina zuwa"

Jikinta a sanyaye ta shiga ciki tana tunanin yadda Dady zai kwashe da Baba? Addu'a ta shiga yi
Allah yasa Baba ya ce shi ne ya sata.

Tana wucewa Dady yaji kansa ya yi masa nauyi yaji ciwon kai yana ratsa kwanyarsa, da k'arfi
ya rik'e kan da hannu biyu, bakinsa na furta.

_"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, la'ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minaz zalumin,
Allahumma laa sahla illa maa ja'allatahu sahla wa anta taj Alhul husza izaa shi'ita sahlan,
astagfirullah wa a dubu ilaiy "_

Ya cigaba da jero duk addu'an da ya zo bakinsa, a hankali yaji ciwon kan na raguwa yana jin
sassauci, ya kai kusan minti goma kafin yaji ciwon kan kamar an É—auke masa ya daina ciwo, ya
sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, ya ji jikinsa kamar an cire masa abu mai nauyi, tunanin
abin da ya faru ya shiga yi, cikin k'ank'anin lokaci ya tuna, da sauri ya d'aga murya ya kira Baba
mai gadi, cikin hanzari da sassarfa ya k'araso tare da risinawa.

"Alhaji ga ni"

"Husna ta ce kaine ka sanya ta a islamiya, hakane?"

Baba mai gadi yaji zufa ya fara tsastsafo masa, hantar cikinsa ya kaÉ—a, sai da ya had'iye miyau
da k'arfi kana ya tattaro natsuwarsa ya ce cike da tsoro.

"Eh Alhaji, ka yi haƙuri na yi laifi, ba komai yasa na sanya ta ba, gani na yi tana da raunin sani
game da addini shiyasa, kuma da ina koya mata to yanzu gani na yi ta girma shi ne na ce
gwara islamiya za tafi mai da hankali, Alhaji ka min aikin gafara haka ba zai sake faruwa ba"

Nan yaja bakinsa ya yi shuru yana sauraren hukuncin da Dady zai yanke masa. Dady ya sauke
ajiyar zuciya, ya ce cike da matsananciyar damuwa.

"Nawa ka kashe?"

"Alhaji ba zan iya tuna nawa na kashe ba domin har uniform su suka bata dan ina ga zai yi dubu
goma"

Nan take Dady ya sanya hannu a aljihunsa ya ciro rafar kud'i 'yan dubu-dubu, ya k'irga dubu
goma ya mik'a masa, jikin Baba na rawa ya amsa domin duk tunaninsa yau ya bar aiki a gidan
kenan, Dady zai kore shi, amma da mamaki sai yaji ya ce.

"Baba nagode da wannan tunani da ka yi daka sanya ta a makaranta, ni ya kamata na yi mata
haka amma na kasa, kuma duk banyi wannan tunanin ba, Allah ya saka da alkhairi, sai dai duk
lokacin da wani abu ya taso to ka fara sanar min kafin ka aikata shi, zaka iya tafiya"

Cike da farin ciki Baba ya yiwa Alhaji godiya kana ya tafi yana jinjina maganarsa, a farkon
saninsa da Alhaji haka yake da kirki da fahimtar mutum, amma daga bisani ya zama mafad'aci
mara fara'a, ya shiga tambayar kansa.

'Anya Hajiya bata yi wani mugun abu a kansa ba kuwa?'

Nan dai ya k'arasa bakin gate yana ta zancen zuci.

Haka nan Dady yaji zuciyarsa na yi masa zafi akan rashin bawa Husna kulawarsa, tunani ya
shiga yi yana tambayar kansa.

'Yaushe na sauya haka? Ni da nafi kowa k'aunar Husna ta yi karatu amma yanzu na zama mai
wofantar da ita, wai ina tunani na yaje ne?'

Hankalinsa ya kuma tashi, wani hawaye mai zafi da rad'ad'i ya fito a idonsa, tunawa da ya yi da
Zainab ne yaji gabansa ya yi mummunan fad'uwa, dasauri ya tashi ya shiga cikin falon.

Ko da ya shiga ba kowa a falon d'akin Husna ya shiga ya sameta ta cire uniform ta sanya wani
doguwar riga na shadda, tana karanta k'arin da aka yi musu na littafin fiqhu, ta d'ago da sauri
dan ganin wanda ya shigo, ganin Dady ne yasa ta washe baki.

"Dady"

Ta ce, sai ya amsa mata fuskarsa cike da fara'a, ya shiga duba d'akin yadda duk komai ya tsofe
ba wani canji tun tana k'arama, damuwarsa ce ya k'aru ya shiga tambayar kansa.

'Ina Husna ta samu kayan da take sawa? waye yake siya mata littafai na makaranta? waye
yake kula da karatunta?'

Dady ganin yadda k'irjinta suka cicciko da dukiyar fulani, yaji wani mummunar faÉ—uwan gaba.

'Husna ta girma, wato kenan ta fara jinin al'ada, innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Waye ya
sanyata akan hanya na sanin menene wannan jinin? ya zata tsarkake jikinta? yaya take gabatar
da ibadunta? shin ya take kula da lafiyarta?'

Wannan tambayoyin fal suke a zuciyarsa ya rasa ta ina zai zamu amsar su.

'Wai wani irin sakaci na yi da na wofantar da É—iyata mai daraja haka? tunda likita ya ce Husna ta
samu matsalar kwakwalwa, nasan ba wani kulawa zata samu a gun Habeeba ba, to wai ko ta
warke ne? tun da gashi yadda take a yanzu babu wata alama na hauka'

Husna dai tana ta kallonsa, ya zame mata sabon mutum kamar ba shi ba, dan ta san rabonsa
da ya shigo d'akinta tun tana k'arama daya dawo daga wani tafiya, tabbas ba zata manta da
wannan ranar ba, mik'ewa ta yi ta matsa kusa da shi ta kama hannunsa, wani irin ajiyar zuciya
ya saki yana kallonta cike da tausayawa. Husna ta ce cikin sanyin murya.
"Dady in na yi maka laifi ka yafe min, ba zan k'ara zuwa makarantar ba tunda baka so?"

Ta k'arasa maganar tana matsar kwalla, cikin zafin nama ya jawota jikinsa ya rungumeta da
k'arfi kamar zai mai da ta cikinsa yana fad'ar.

"A'a Husna ni ne zan nima gafara a gurinki, Æ´ata ki yafe min, hak'ik'a a baya na tafka babban
kuskure wanda ban san ta yaya na aikata miki haka ba"

Husna ta ƙara fashewa da sabon kuka, kiran sallar magrib ne ya dawo dasu cikin natsuwarsu,
Dady ya sake ta ya zaunar da ita gefen gado.

"Ki cigaba da mai da hankalinki ki yi karatu sosai, ba zaki daina zuwa ba nima na yi kuskuren
rashin sanya ki a makarantar, ki yi haƙuri kin ji. Babanki yana sonki sosai"

Ya k'arasa maganar yana murmushi, ita ma murmushin ta yi.

"Ni Dady baka min komai ba, kullun Uncle yana ce min in rik'a yi maka addu'a, kuma Dady ina
yi, dan Allah kar ka ƙara nesa dani ka ji"

Dady ya katse mata magana da jefa mata tambaya.

"Waye Uncle?"

Husna ta dafe bakinta da sauri, fargaba ne ya taso mata kan sub'ul da bakan da ta yi, murmushi
Dady ya yi mata saboda ya lura da yadda yana yin ta ya sauya, sai ya tashi ba tare da ya nuna
mata damuwar sa ba ya ce.

"Ki tashi ki yi sallah, ni zan tafi masallaci sai na dawo"

Cike da farinciki ta ta shi.

"Ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login