Showing 63001 words to 66000 words out of 81944 words
Chapter 22 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
"A'a ban iya ba, kawai dai koya na yi, kuma iya wannan na iya"
"To Uncle in zo in ganka?"
"A'a Husna, anjima zan shigo na ganki in baki gift d'inki"
"To nagode Uncle da ka sani farin ciki"
"Bakomai my Husna Allah ya miki Albarka"
"Ameen my Uncle"
Sannan ta kashe wayan.
Yasir na tsaye kan Sadiq duk wayar da su ka yi da Husna a kunnen sa, amma Sadiq bai san ya
shigo ba, sai da ya aje wayan Yasir ya fara tafa masa.
"Da kyau Baban love, kai da waye kake waya haka harda waka?"
Harara Sadiq ya wurga masa.
"Lab'e ka koma yi ashe, to ka fita hanyata ka wani dameni da tambaya"
Murmushi Yasir ya yi.
"To mai da wuk'ar ni yau ba ranar fad'ana bane a matsayina na Ango"
Wani k'ululun bak'in ciki ne ya tokare zuciyar Sadiq sai bai tanka masa ba, Yasir ya lura da
sauyawar fuskarsa amma ya watsar ya ce.
"In ka gama nuk'u-nuk'u ka fito ga friends d'ina da abokan aikinmu sun zo, kuma saura rabin
awa a d'aura aurena dan haka ka fito, kasan kai ne jagoran komai"
Yana gama fad'ar haka bai jira mai Sadiq zai ce ba ya wuce, wani harara Sadiq ya bi shi da shi
tare da yin tsaki, mik'ewa ya yi ya d'aura babban rigarsa a saman k'aramar, farar shadda yasa
mai aiki da ash color zare, ya sanya cover shoe da hula Ash, a gogansa ma ash, ya yi matuk'ar
kyau, fuskarsa a murtuke babu yabo ba fallasa. Shima haka Yasir ya yi na shi kwalliyar, shadda
fara mai aiki brown, ya sanya hula da cover shoe brown, agogo kalar brown, ya yi kyau sosai ya
fito a angon Husna.
Sadiq yana fita harabar gidansa ya ci karo da mutane. Nan suka soma gaisawa, da yake wasu
sun san Sadiq da miskilanci bai cika fara'a ba shiyasa basu gane halin da yake ciki ba na
damuwa, Emanuel ne ya ce.
"Kai mutumina ka yi kyau kamar kai ne Ango"
Murmushi ya masa ya ce.
"Ga Ango can yana washe baki kamar gonan auduga"
"Amma fa gaskiya ka fishi had'uwa fa"
"kai Ema baka duba da kyau ba"
Nan dai suka cigaba da hira, dan dama sun saba.
A wajen k'ofar gidansu Dady an sanya tempol da yawa, motoci sun cika layin gaba d'aya dayin
ya cike da Jama'a, ga duk kan alamu lokacin d'aurin qure ya k'arato, Dady sai gaisawa yake da
mutane yana nuna musu wurin zama, da shi da Alh. Ahmad suna ta hada-hadan karb'an
Jama'a, Kawu Suleiman shima ya k'araso dana shi tawagar, nan su Dady suka tarbesu suka
gaisa tare da nuna musu masaukinsu suka zauna, Kawu Suleiman ya d'auki wayarsa ya kira
wayar Yasir bugu d'aya ya d'auka, kan ya ce wani abu Kawu ya fara magana
"Kai Yasir kuna ina ne ga wuri ya gama had'uwa saura minti biyar fa a fara d'aurawa, ya kamata
ku hanzarto ku taho"
Yasir ya ce.
"Ai Kawu gamu nan a cikin gidan Sadiq yanzu zamu fito"
"To sai kun fito"
Nan ya gimtse wayan.
B'angaren Husna ta sake kaya ta sanya wata atamfa blue color mai fulawa yallow da fari, Ruky
mai make-up ta tsantsara mata d'auri tare da gyara mata kwalliyarta, Minal ce d'auke da turare
a hannunta ta shiga fesa mata, Husna ta yi wani shegen kyau sai sheki take kamar gold, hotuna
suka shiga d'auka a yawarsu, suna cikin haka wayar Husna ta d'auki k'ara, tana dubawa taga
number Khadija ce, cike da mutuwar jiki Husnah
ta d'aga wayan tare da shiga bedroom d'in Dady, suka gaisa kana Khadija ta fara mata k'orafin
bata kiranta, Husna ta bata hak'uri ta ce.
"k'awata wallahi ina cikin matsala ne shiyasa baki ga kira na ba"
Da sauri Khadija ta tari numfashinta.
"Matsalar me? nima fa ina cike da damuwa"
Nan Khadija ta labarta mata abin da ya faru a gidansu, ta k'arasa maganar da cewa.
"Wai ni yaya Sadiq yake cewa bai so na, dan Allah Husna ya zanyi?"
Mumfashi Husna ta sauke ta ce.
"Ina ganin na ki Khadija mai sauki ne, Ni fa a yau Dady ke d'aura min aure da wanda ban sani
ba"
Ta k'arasa maganar muryanta na rawa kamar za ta yi kuka, wani ihu Khadija ta yi wanda sai da
Husna ta kauda wayar a kunnenta ta ce.
"What? Aure fa kika ce Husna? shi ne baki gaya min ba"
Nan Husna ta fara kuka ta bata labarin yadda abin ya kasance, ita ma bata sani ba sai jiya da
Dady yake gaya mata, Khadija kuka ita ma ta shiga yi, innalillahi kawai take ambata.
"Yanzu an kusa d'aura Auren?"
"Mmmm, yanzu ma za'a d'aura, dan k'arfe sha d'aya safe za'a d'aura, kuma lokacin ma ya yi"
Masu karatu bari na bar Husnah da k'awarta su cigaba da wayarsu, dan na koma wajen d'aurin
aure muga wainar da suke toyawa.
K'arfe sha d'aya da minti goma, kowa ya yi tsit ana sauraran shirye-shiryen d'aurin aure, iyaye
sun had'u, Baba Husain na zaune, Dady da Alh. Ahmad, sai Baba mai gadi daya sha shadda
brown tasha aiki, Dady ya d''inka masa tare da takalmi da hula bakak'e masu kyau, sune iyayen
amarya, sai Kawu Suleiman da Abokinsa malam Tanimu, sai k'aninsa Alh. Ghali, da sauran
tawagarsu, sune iyayen Ango. Alh. Ahmad shi ne Dady ya bama waliyyin Amarya, sai Kawu
Suleiman shi ne waliyyin Ango, nan suka fara yin sigan Aure kamar yanda Addini ya tanadar
mana da shi.
Sadiq da Yasir suna zaune a gefe nesa dasu Dady cikin tempol su da Abokansu, Sadiq ya
sunkuyar da kai ya fad'a kogin tunani, bai san abin da ake cikin ba.
Muryan marok'i suka juyo yana shela a lasifika cewar.
_"An d'aura Auren *ASMA'UL HUSNA KHALIL da ABUBAKAR SADIQ ALIYU* bisa sadaki dubu
hamsin lakadan ba ajalan ba"_
Wani irin zabura Sadiq ya yi ya kai kallonsa ga mai sanarwa, wanda ya cigaba da shela sai da
ya maimaita har sau uku, a zabure Sadiq ya mik'e.
Ta b'angaren Husna kuwa, tana waya da Khadija, tana jin wannan marok'i yana fad'ar an d'aura
mata aure da Sadiq, sai ta yi wani wawan ihu ta saki wayar a k'asa ta tarwatse.
_*Wak'ar Sadiq da Husna*_
í ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒ
_í ¼í¾¶Huuuusna na zama tauraruwaa, sanyin idaniyaa, ni ce zinariyaa.í ¼í¾¶_
í ½íµºí ½íµºí ½íµºí ½íµºí ½íµº
_í ¼í¾¶Husna fito Husna, Husna taho Husna, komai nabai Husnaah.í ¼í¾¶_
í ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒ
_í ¼í¾¶Nazo nagaishe ka, na amsa sunanka, so ga shi na bakaa.í ¼í¾¶_
í ½íµºí ½íµºí ½íµºí ½íµºí ½íµº
_í ¼í¾¶Na d'aga kambun soyayya, akan haka na shirya, mai hak'uri an ce mini ba shi asara, kin
saka gasa na d'auka, cikin mu samari nai zarra, a duniya an sa mini suna rimio, zo bani
soyayya, a so bani jin kunya, sunanki ne Husnaah.í ¼í¾¶_
í ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒ
_í ¼í¾¶Abin da nake So ina nan tare da shi, ko kad'an ban son in nesa da shi, bani son komai ya
tab'a mini shi, zuciyata dan ta yarda dan ta yarda dashi, juyo na kalle ka, So amshi na baka, ba
wanda zai kaikaaa.í ¼í¾¶_
í ½íµºí ½íµºí ½íµºí ½íµºí ½íµº
_í ¼í¾¶Kyauta ta ba zan baiwa kowaba, sai wacce nake So batai min So da wasa ba, inna bata a
raina nasan naci riba, zamanmu da ke Soyayya nasa mun saba, zan miki kankamba, shigata
kid'an duba, Sona na bai Husnaah.í ¼í¾¶_
í ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒ
_í ¼í¾¶Farin ciki na kai ka zamo sanadi, zuciyata murna ba a dadi, sannu-sannu sai mu jira wa'adi,
lokacin ne zanma Albishiri, zan baka Soyayya dan yanzu na shirya, Husnah ta zamo
takaaa.í ¼í¾¶_
í ¼í¾¶í ¼í¾¶í ¼í¾¶í ¼í¾¶í ¼í¾¶í ¼í¾¶
í ½íµºí ½íµºí ½íµºí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒ
[11/2, 10:02 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 55 ~ 56_*
Mik'ewan da Sadiq ya yi sai kallo ya koma wurinsa, kowa ya yi masa ca da ido, jikinsa ya yi
sanyi tare da jin kunya, hakan yasa dole ya koma ya zauna, suka had'a ido da Yasir ya galla
masa harara mai cike da tambayoyi, murmushin mugunta Yasir ya masa irin na ko a jikinsa.
Bayan an kammala d'aurin aure koya ya mik'e aka shiga hada-hada da abinci dan walima.
Sadiq cikin sauri ya isa gidansa, d'akinsa ya wuce ya zauna l gefen gado, malun-malun ya cire
tare da hula, ya shiga fifita da hulan saboda duk jikinsa ya had'a gumi, mai-maita kalmar an
d'aura masa aure da Husna ya ke yi a zuciya, d'akin d'auke yake da sanyin AC amma ko kad'an
baya shigansa sai wani sabon gumi yake yi.
Yasir ne ya shigo yana kwala masa kira sai ya yi arba da shi zaune kan gado sai fifita yake yi da
hularsa, dariya Yasir ya kwashe da shi haryana rik'e ciki, cikin dariya ya ce.
"Malam duk gumin murna ce haka? Kazo ka jirge a d'aki ga jama'a nata tambayar ina ango"
Sadiq ya yi tsaki cike da hasala ya fara magana.
"Yasir ban san kana da tab'un hankali ba sai yau, ina so ka sanar min ya haka ya kasance bacin
kaine mijin Husna, kowa ya shaida haka hatta abokanka sun san bikinka suka zo, kun sanyani a
rud'ani wallahi, gaba d'aya na gaza samun sukuni, ka warware mini yadda zan gane ba mafarki
nake yi ba?"
Murmushi Yasir ya yi masa ya samu wani farar kujera ya jawo ya zauna nesa kad'an da Sadiq
yana fuskantansa.
"Sadiq hak'ik'a kowa yasan da cewa ni ne zan auri Husna amma ban da ni da Kawu Suleiman
da Dady, kai in tak'aice maka su Kawu bani suka nimawa Auren Husnah
ba, da sunanka suka nima aurenta"
Wani razanan nan kallo Sadiq yabi Yasir da shi, kan ya yi magana Yasir ya cigaba da cewa.
"Na san dole za ka yi mamaki, yanzu haka abokaina da sauran mutane na sanar musu
gaskiyarvlamari, cewa kaine ango, dama mun b'oye hakan ne saboda wasu dalilai da bamu son
wasu su sani sai ranar aure, da haka suka gamsu yanzu haka suna chan suna cin abincin
walima"
Kallon mamaki yanzu Sadiq ya kema Yasir, yana son yin magana Yasir ya katse shi.
"Sadiq duk wani nuku-nuku da kake yi wallahi nasan kana son Husna, ka sani har ga Allah ba
zan iya zama da Husna a matsayin mata ba, bacin nasan kana sonta, tun lokacin daka bani
labarinka tare dana Husna na fuskanci akwai soyayyar Husna a zuciyarka. Shiyasa na yi wasa
da zuciyarka na nuna maka ni zan aureta domin in samu damar da zan had'aku, matsalar
iyayenka mai sauki ne Sadiq, nan gaba Insha Allah zasu fahimci komai. Sannan a ganina
Husna bata dace da ko wani namiji ba face kai, Sadiq kaine silar farin cikinta harta samu 'yanci,
hakan ne yasa Dady ya maka ta yin Aurenta dan ya san in ba kai ba da wuya Husna ta samu
miji kamanka, na san kuma ya yi duba da haka ne domin kyawawan halayyar ka, bana tunanin
inda ace su Kawu sun je da zancen ni ne zan aureta to babu shakka da wuya ya yarda, domin
na san ba zai tab'a amincewa ba, dan yaushe ma ya waye ni da zai bani 'yarsa wacce yafi so a
duniya, Sadiq kaima inda ka yi tunanin haka tofa kasan bamai yuwuwa bane, dan haka ka tashi
kawai ka fito ka warware my friend mu cigaba da shagalin biki"
Sadiq wani nannauyan ajiyan zuciya ya saki tare da dafe kansa, yana tunanin tabbas abin da
Yasir ya fad'a gaskiya ne, ya d'ago kai suka had'a ido da Yasir, cikin raunin murya ya ce.
Yasir ya zanyi da Iyayena in suka ji na yi Aure bada izininsu ba, duk bayanin da zan musu ba
zasu yarda ba saboda tunda na baro Kaduna ranar da abin nan ya faru ban sake komawa ba,
kana ganin ya zanyi dan sune damuwana yanzu?"
Yasir ya yi ajiyan zuciya tare da matsowa ya dafa Sadiq.
"Abokina ka zama Namiji mana, ka kauda wannan damuwar ka yi shagalin bikinka, Insha Allah
komai zai yi dai-dai, na yi alkawari tare zamu Kaduna domin in warware musu komai su gane
ba kada laifi ni ne mai laifi"
Sadiq ya yi shuru yana nazarin maganan Yasir can ya nisa.
"Ba damuwa, bari na watsa ruwa na canza kaya"
Yasir ya yi masa murmuahi.
"Good My friend, bari naje na cigaba da karb'an mutane sai ka fito"
Bai jira mai zai ce ba ya fice. Sadiq yana binsa da kallon kauna ya ce a fili.
"Alhamdulillah da samun aboki nagari"
Kana ya mik'e ya shiga wanka.
Ta b'angaren Husna kuwa, ihun data saki yasa su Minal shiga bedroom d'in da gudu har suna
bige juma ita da Kausar, sun sameta a tsaye kikam ta runshe idonta, tare da k'ank'ame jikinta,
hak'ik'a tana cikin shock, da sauri Minal ta kira sunanta da k'arfi.
"Husna lafiya? meya sameki?"
Haka ta jero mata tambaya wanda babu amsa, bud'e ido ta yi a hankali ta soma kallonsu ba um
ba um-um, Kausar ta zuk'unna ta dauki wayar Husna da ta watse a k'asa ta had'a tare da
dubawa taga harta tsage kad'an daga sama, ta ce.
"Anty Minal ko zamu kira Momy ce?"
Da sauri Husna ta ce.
"Karku kira kowa babu komai, wai dagaske an d'aura min aure da Sadiq?"
Minal cikin sauri ta ce.
"Eh ba ki ji bane ai anata sanarwa, mu dai ki gaya mana meya baki tsoro kika yi k'ara da k'arfi
haka?"
Hawaye ne ya shiga zarya a kan kuncinta.
"Ba komai, kawai dai rud'ani na shiga da wanda na ji ya zama Mijina, ni Uncle Sadiq kawai na
sani, kuma ina zargin ko shi ne mijin da Dady ya zab'a min?"
Minal ta ce.
"Ayya 'yar uwa ki yi hak'uri, Dady ba zai had'aki da mutumin banza ba Insha Allah, zaki ji dad'in
zama da shi"
Murmushi Husna ta yi mai cike da ma'anoni da yawa.
"Hakane, mu je wurinsu Momy"
Cike da natsuwa suka rankaya cikin gida. Husna tana tunani barkatai akan in Sadiq ne mijinta
wani irin zama za su yi ita da take masa kallon Uncle d'inta.
***
Yasir ya lek'o bedroom d'in Sadiq ya ce.
"Kai Malam kanata b'ata lokaci ya kamata ka gama shiri yanzu ai"
"To ai na gama"
Farin material na maza ya sanya mai shara-shara ana ganin singilet d'insa, bak'in hula yasa da
bak'in takalmi ya yi matuk'ar kyau, ya sanya agogo bak'i ya feshe jikinsa da turaruka masu
dad'in kamshi, ya fito a ango sosai, Yasir binsa ya yi da kallo mai cike da burgewa.
"Kai Sadiq kafa yi kyau ka fito a Ango sak"
Dariya Sadiq ya saki wanda ya bayyana fararen hak'oransa.
"Ban son sharri fa"
"Ba wani sharri, in da baka yi kyau ba ai ba zan tanka ba"
Sadiq ya k'araso kusa da Yasir ya kamo hannunsa.
"Yasir ban da bakin gode maka, face in maka Addu'a Allah ya baka Mata tagari ya saka maka
da gidan Aljanna. Ka samar min da farin ciki, yau hak'ik'a na k'ara tabbatar da kai Aminin kwarai
ne kana min soyayya na gaskiya, ina alfahari da Abotar mu"
Nan ya yi ta kwararo masa maganganu masu dad'i, ai ko saboda murna Yasir ya jawo shi ya
rungume shi.
"Karka damu kai dan uwana ne, haka na d'auke ka tun farkon had'uwar mu. Allah ya barmu tare
ya bar zumunci"
Duk suka Amsa da Ameen. Sadiq ya zame jikinsa yana kallon Yasir idonsa cike da hawaye ya
ce.
"Kamin komai Yasir, wallahi da ace ban auri Husna ba da samun farin ciki yaye a zuciyata,
domin na rasa farin ciki na kenan har abada, kai ne mutum na biyu da ka fuskanci son da
nakewa Husna sai Dady, domin Dady ya hango hakan ne ya nima had'amu aure. Matsala d'aya
yadda zan fuskanci Husna a matsayin miji, bayan ta d'auke ni a matsayin Uncle d'inta"
Murmushi Yasir ya yi.
"Ni kam ina ganin shawo kanta ba zai baka wuya ba domin ai kun saba sosai, kawai sauya
akala zaka yi zuwa nuna mata soyayya cikin saban salo, dan ina ganin ita kanta Husna akwai
k'amshin sonka a tare da ita, kurciya ce kawai ba zaisa ta fahimta ba"
"Kai abokina ya a kai ka gane haka?"
"Hhhhh an gaya maka ni na wasa?"
"Hakane fa, domin kai baban soyayya ne makaranta kawai zaka bud'e wa matasa a kan karatun
soyayya"
Dariya sosai dukansu suka yi Sadiq ya ce.
"Insha Allah zan koyawa Husna sona, kan muyi wani mu'amalan aure, kamar nan da shekara
biyu lokacin ta k'ara girma da hankali, dan yanzu ni raino aka bani fa"
Dariya Yasir ya yi harda tafa hannu.
"Abokina kar nan da 9 months mu zo shan suna fa?"
"Kai haba dai ai Husna yarinya ce da sauranta"
"Uhum mu dai je zuwa Malam Allah yasa ka iya kaiwa 2month"
"Zan baka mamaki fa Yasir"
"To me na ce, ai na zuba ido kawai, nan zaka so kana bani labari Malam"
Nan dai suka fita suna hira cikin nishad'i har suka isa wurin abokansu, suka cigaba da shagalin
biki.
An cigaba da shagalin biki har zuwa yamma, an shirya walima a nan harabar gidan Dady, wata
Malama aka gayyato Malama Aisha Muhammad dan ta yi bayani akan zaman takewar aure, an
shirya filin gidan da fararen kujeru, in da mata zuka baje sunata kwasar garab'asar sirrin rik'e
miki a bakin Malama Aisha, sunsha wa'azi daga bisani k'arfe shida da kwata aka rufe taro da
Addu'a tare da raba abubuwa na walima. Can na hango