Showing 81001 words to 81944 words out of 81944 words
Chapter 28 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
d'aya ne, Khadija taji dad'in ganin su suka sha hira, sannan ta nunawa Husna yadda gidan nasu
yake, sai dare suka koma gidansu.
*******
Su Husna an cigaba da karatu ga yaransu sun k'ara girma da wayo, soyayya tsakaninta da
mijinta kuwa sai abin da ya yi gaba.
Ta bangaren Dady kuwa ya yi retire ya soma business d'in motoci inda ya bude sabon company
mai suna Al'amin motor's limited, yana shigowa dasu daga k'asashen waje, arziki yaci uban na
da. babban Pharmacy ya bud'ewa Momy Zee mai suna Zainab pharmacy, wanda suke sarar da
magani ga k'ananan 'yan kasuwa, tana zuwa aikinta su Hassan sun yi wayo sosai, wajen su
Inna take barinsu, haka Husna pharmacy dake Kaduna su Baffa suna ta kula mata da shi sai
hab'aka yake.
Dady ya siyawa Baba mai gadi gida nan kusa dasu ya dawo da iyalinsa suna zumunci, sannan
ya sanya shi cikin harkan company sa, sai suka samu sabon mai gadi ya cigaba da aikin Baba.
*******
Husna da Sadiq suna kallon tashar Sunnah TV, Sadiq na zaune kan kafet Husna ta d'aura kanta
a bisa cinyarsa yana wasa da gashin kanta, Amir da Amira suna ta wasa, da yake sun fara
zama har k'ok'arin ta shi suke yi yanzu, Sadiq ya ce.
"Sweet baby ina so in d'auki hutu na wata d'aya domin mu zaga k'asar waje dan shakatawa,
amma me kika gani saboda karatunki?"
Cike da murna ta ce.
"Haskena, ka bari mu gama exam tun da mun kusa farawa, da mun samu Hutu sai mu tafi,
amma ni nafi son mu tafi k'asa mai tsarki mu yi Umarah"
"Eh gaskiya kin kawo shawara mai kyau, to ya za mu yi dasu Amir?"
"Sai mu tafi dasu tare da Anty Jimmai"
Murmushi ya yi na gefen baki.
"Na so ki yayesu kawai mu tafi mu biyu, amma tunda kin ce mu je dasu ba matsala"
"Wai, ai Uncle ba zan iya tafiya ba dasu ba dan basu isa iyaye ba"
"Uhum ni ko gani na yi ya dace a samo musu kwanuwa dan sun girma"
Husna ta zaro ido cike da tsoro.
"Haba dai Uncle wallahi tsoro nake ji dan haihuwa akwai wahala, ni su Amira ma sun ishe ni"
"Kai my Hussy, bafa wahala nishi d'aya za ki yi ki haihu, dan haka ina son yara da yawa sai ki
shirya amsarsu"
Husna ta shagwab'e fuska.
"Ni fa bana so Uncle"
Yatsansa ya sanya akan lips d'inta.
"kar ki sake kira na da Uncle kin gane"
"Uncle tuna baya na yi"
Ya lakace mata hanci.
"Na sani, tsokana ce kawai irin naki"
Kafin ta yi magana ya rufe mata baki da na shi, suka tsunduma kogin masoya, cikin tak'aitaccen
lokaci sun mance duniyar da suke ciki, kukan Amir suka ji kamar daga sama, a firgice ya saketa
ya isa gunsa da sauri ya shiga liliya masa kansa in da ya buge, ya soma lallashinsa sannan ya
yi shuru, Husna ta mik'e tana hamma ta d'auki Amira ta ce.
"Uncle"
Da sauri ta rufe bakinta tana fad'in.
"Au sorry baby, sweet hubby zance"
Murmushi ya yi ya ce.
"Zan kamaki ai, mu je mu kaisu gun Mama Jimmai, naga kin soma hamma da alama barci kike
ji"
"Kamar kuwa ka sani"
Sun kai yaran wajen Anty Jimmai suka dawo part d'in Sadiq, suna shiga ta fad'a kan gado tare
da gyara kwanciya.
"Me kike nufi? kima ta shi dan ba zaki yi barci yanzu ba sai kin min tausa"
"Kai hubby, barci nake ji fa"
Ta ce cikin shagwaba.
"Eh, za ki yi barci, amma fa zai mun kai ziyara k'asar masoya"
Dariya ta kwashe da shi, kan ta yi aune ya fad'a kan gadon ya tsafkota.
"Wa ki kewa dariya?"
Sai ta k'unshe sauran dariyan a bakinta, tama kasa magana, cakul kuli ya soma yi mata tana
kwasar dariya, da kyar ta iya kwace kanta ta wurga masa pillow, daga nan kuma wasa ya sauya
salo, tuni na fito d'akin na rufe musu k'ofa, to Sadiq da Husna a hau jirgin masoya lafiya.✈
*Karshe*
_Matasa mu sani duk kuskuren da muka aikata ya yin aure, tofa mu sani fa bamu kad'ai zaiwa
illa ba hatta 'ya'yanmu zai shafa, mu rika aiki da tunanin abin da zai je ya dawo, kar so ya rufe
mana ido mu tafka kuskure_
*Kuma Iyaye ku sani auren dole babu kyau a musulunci, in yaro ya ce bai so ga zabinsa, tofa
mu tsaya mu duba muga shin wanda take so yana da nagarta da dabi'a mai kyau? in yana da
shi sai a bata in kuma bai da shi sai a lallasheta a nuna mata illolinsa cikin lumana ba tare da
takurawa ba, dan matsawa da takurawa shi ke haifar da tuburewar yaranmu suk'i yi mana
biyayya. Allah yasa mu dace, Ameen.*
*A nan na kawo karashen wannan littafi mai Suna KAD'AICI. Allah ya bamu ikon ammani da
abin da mukaranta dake ciki, ya kuma yafe mana bisa kuskuren dake ciki. Allah ya karemu da
bata bayan shiriya. Sai kun jini a sabon buk dina mai suna SO SANADI❤*
Kamar yadda na sanar muku tsohon littafi ne na sabunta muku shi., shima so sanadi nayi shi da
jimawa.
*Na sadaukar*
*_Da wanannan littafa ga group dina SIRRIN 'YA MACE_*
*_Gai suwa da ban girma ga masoya wannan littafin KAD'AICI, Allah ya saka da alkhairi yabar
zumunci._*