Showing 42001 words to 45000 words out of 81944 words
Chapter 15 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
dawo lafiya Dadyna"
***
Bayan Dady sun idar da Sallah zama ya yi a masallaci dan jiran sallar isha'i, abin da ya jima bai
yi ba kenan, ya shiga yin lazumi, a haka ya faÉ—a duniyar tunani mai zurfi.
'Waye wannan Uncle da Husna take fad'a? anya Allah ba zai kama ni da laifin sakaci da
tarbiyyarki ba Husna? lallai ya zama dole in bibiyi lamuranki, sannan in tashi sosai wajen niman
lafiyarta ki. Allah nagode maka daka farkar dani daga dogon barcin dana yi, Allah ka taimake ni
bisa komai, ka karemu daga duk kan shrrin shaiÉ—an, mutum da aljan
'[10/27, 5:37 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 33 ~ 34_*
Cikin dare Dady ya tashi ya zauna yana tunanin rayuwa, ya tashi ya je ya d'auro alwala ya fara
gabatar da sallar nafila, sai da ya jero raka'a shida kana ya zauna, ya yi istigfari da lazumi had'e
da salatin fiyayyen halitta s.a.w, ya d'auki kusan awa guda kana ya tashi ya koma saman gado,
kallon Momy ya yi tana ta faman sharb'an barci abin ta, ya girgiza kai ya koma ya kwanta kamar
mai barci, don idonsa k'amas babu alamar barci, ya lumshe su ya fad'a duniyar tunani, abin
mamaki sai ya fara tuno farkon dawowar sa daga kasar Manaco da duk abin da ya faru, akan
yadda ya sauya lokaci guda tunda ya shak'i turaren wuta da Momy ta sanya a falon, ga yafda
Momy ta ke galmazawa Husna akan idonsa baya iya tabuka komai, kuma shima ya daura mata
da na shi hukuncin, ya tuna da irin hantarar da yake yi mata, gaba daya duk abin suka dawo
masa kamar an sanya masa cassette yana kallo, haka ya dinga tuna komai kamar a film,
hawaye masu zafi suke sauka a kuncinsa, damuwa ne fal zuciyarsa cike da tambayar kansa.
'Menene ya same ni? anya ban samu gushewar kwakwalwa ba?'
Addu'a ya shiga jerowa da hamdala ga Allah da ya warware masa komai cikin sauk'i ya dawo
cikin hankalinsa, ya d'aura aniyar bin komai a hankali har sai ya fahimci komai da abubuwan da
suke tafiya a gidan, sai ya gyara kwanciyarsa ya kwanta, bai jima ba barci ya yi awon gaba
dashi.
*******
*Washe gari*
Sadiq ne ya fito daga gidansa ya k'araso kusa da Baba da yake zaune a kan benci a waje yana
sauraron radio, wuri ya samu ya zauna suka gaisa, Baba ya ce.
"Sadiq kamar kasan ina nemanka fa"
"Allah ko Baba, to gani, da fatan dai lafiya?"
"Lafiya lau, kai ma kasan in na ce ina nemanka to baya wuce zancen Husna, in gaya maka jiya
Alhaji yana zaune a cikin gida yana shan iska sai ga Husna ta dawo daga kamaranta ya ganta,
hmm ai in gaya maka zuciyata ta tsinke dana ji muryar Alhaji yana kira na"
Nan ya kwashe duk yadda suka yi da Alhaji ya gayawa Sadiq, wani farin ciki ne ya lullub'e shi
yana fad'in.
"Alhamdulillah! na yi farin ciki da jin wannan labari, ban yi zaton zamu kwashe da shi da sauki
haka ba, kuma Husna ta yi hankali da ba ta ce nine na sata ba"
"Kwarai wallahi ta yi tunani akai"
Cewar Baba yana kiciniyar ciro kud'in daga aljihunsa.
"Kaga kud'in ma ban aje su da nisa ba, dan nasan zamu had'u, da baka fito ba, da har gida
zaka ganni na mako maka sallama"
Ya k'arasa maganar yana yar dariya, shima Sadiq dariya ya yi.
"Haba Baba ai ba sai ka zo ba, gani ma Allah ya jeho maka ni kamar daga sama, dan haka ka
rik'e wannan kud'in halak malak na bar baka su"
Bana ya kara washe baki yana dariya.
"Anya Sadiq ayi haka? naga kud'in da yawa fa, ko dubu biyu ka bani ya wadatar dani sai ka rik'e
sauran, nagode"
Murmushi Sadiq ya yi wanda daka gani kasan yana cike da farin ciki.
"Ai Baba ka wuce haka a guna tunda kaima kana iya k'ok'arinka wajen taimakawa Husna, dan
haka ni da kai duk munyi tarayya acikin hidimarta"
Godiya Baba ya yi masa sosai yana jin jina karamci irin na Sadiq, a cikin ransa ya ce.
'Ashe ana samun yayan masu kud'i haka wanda basa kyamar talaka, gaba d'aya rayuwar Sadiq
taa burgeni ga ilimi duk ya had'a boko dana Arabi, ga tausayi da girmama na gaba da shi, ga
kuma natsuwa da karamci, ga kyau da kud'i duk ya had'a, lallai iyayensa sun kasance mutanan
kirki, madalla da zuri'a irin tasu, Allah ka k'ara had'amu da mutanan kwarai'
Sai ya ji Sadiq na amsa masa da
"Amin Baba"
Da mamaki Baba ya kalle shi ashe zancen zuci ne ya fito fili, dariya ya yi masa suka cigaba da
hira.
Husna sun taso makaranta, haka ta gangaro gida, tana tafiya cike da natsuwa, ta samu Sadiq
a bakin gate nan ta tsaya suka gaisa, daga nan hira ta barke tsakaninsu na zancen karatunta,
yana tambayarta wasu daga cikin littafanta tana ba shi amsa, wanda bata sani ba ya gaya mata
tare da yi mata bayani.
Tun daga nesa Dady ya hango su yana Allah-Allah ya k'araso yaga da waye take magana, basu
ga zuwansa ba saboda sunyi nisa cikin hirarsu, mai gadi ne ya hango shi kafin ya k'araso ya
shiga ciki da sauri ya bud'e masa gate, da sauri Dady ya shiga da gudu ya yi parking, Husna taji
gabanta ya yi mummunar fad'uwa, duk tunaninta Dady yana cikin gida shiyasa ta sakankance
suna ta hira, yau ce rana ta farko daya fara ganinsu tare da Sadiq, Dady ya fito wajen fuskarsa
kamar anyi masa mutuwa a murtuke, shi dai Sadiq ko d'ar a zuciyarsa na fargaba bai ji ba sai
ma wani k'arfin guwa da yaji, cikin natsuwa ya risina ya ce.
"Dady ina yini"
Dady ya amsa masa dak'ile, Husna tana ganin haka hantar cikinta ya kad'a, ta bud'e baki zata
yi magana kenan, ya fara magana cikin kakkausar murya.
"Me kikeyi a nan? makarantar kenan? ko kuwa abin da aka koya miki kenan in kin dawo ki tsaya
bakin gate kina surutu?"
Husna ta sunne kai kasa ta kasa furta komai, banda hawaye da suka cika mata ido kamar zasu
subo, tsawa ya daka mata.
"Maza ki wuce ciki kafin in b'allaki"
Jiki na b'ari ta shiga cikin gida. Mugun kallo ya dannawa Sadiq kana ya nuna sa da yatsa.
"Karna sake ganinka a k'ofar gidan nan"
Bai sake furta komai ba ya wuce ciki. Sadiq ya yi murmushi ya girgiza kai, farin ciki ne fal
cikinsa domin wannan action d'in da Dady ya nuna, ya tabbata masa da ya dawo cikin
hayyacinsa, Baba ne ya matso kusa da shi yana ba shi baki.
"Kayi hakuri nasan rashin sani ne yasa shi yi maka haka, dan da ashe ya san ko kai waye ga
Husna da ba zai yi maka haka ba"
"Karka damu Baba lokaci zai bayyana haka"
Haka ya tashi suki yi sallama da Baba ya shige gida hankalinsa kwance.
Dady yana kutsa kai cikin falo ya shiga kwalawa Husna kira, tun daga d'aki ta b'arke da kuka
jikinta na rawa domin yau ta sadak'ar zata sha d'an banzan dukan data dad'e bata sha ba, haka
ta fito kamar kwai ya fashe mata a ciki, Dady ji ya yi duk tausayinta ya kamashi amma sai ya
danne ya fara mata fad'a ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, cikin sauri Momy ta fito falon
dan ganin me ke faruwa.
"Alhaji lafiya? me ya faru ne?"
Cewar Momy. Dady ya ce cikin fada.
"Ta dawo daga makaranta mai makon ta shiga gida sai ta tsaya a waje tana magana da wani
yaro"
Momy taja tsaki.
"Dama a kan wannan sha-sha-shar kake tada jijiyoyin wuya, ai in dai wannan ce zata ai kata
abin da yafi haka, makarantar munafunci take zuwa ai, wacce take da hauka taya zata fahimci
karatu"
Mamaki ne fal zuciyan Dady yana kallon Momy, amma sai ya dake bai nuna ba, ta cigaba da
cewa.
"Ai Kaine baka sani ba, haukan nata iskanci ya sanya mata na bin maza, yanzu haka in ka
shure k'afa ka fita da safe itama fita take yi sai lokacin da taga dama take dawowa"
Dady yaji Zuciyarsa ta yi masa nauyi, saboda jin zafin furucin Momy akan Husna, sai ya fara kai
kawo bugun zuciyarsa ya fara bugawa da sauri da sauri, tuni idanun sa suka yi ja kamar jan
karwashi, tashin hankali ne ya ziyarceshi lokacin da Momy take aibata masa 'ya tare da
karairayi da mugun sharri da takewa Husnaht, mummunar tsanar Momy yaji a ransa, ya dafe
kansa ya samu guri ya zauna ba tare da ya furta komai, ba saboda azabar da zuciyarsa yake
masa a wannan lokacin.
Ai Momy sai ta samu damar k'ara zugashi dan a tunaninta tuggun da ta had'awa Husna ya
samu gurbi a zuciyarbDady, dan tas an asirin da ta yi masa yana nan a jikinsa, kukan Husna ya
k'aru tana fad'in.
"Wallahi Dady ni ba mahaukaciya ba ce da hankali na, sannan ni bana yawo ban bin maza,
Momy sharri take min, wallahi ban aikata komai ba, Dady ka yarda dani"
Ta k'arasa maganar tana zubda hawaye mai rad'ad'i, nan take Husna taji ta k'ara tsanar Momy,
duk tunanin ta k'iyayyar da Momy ke yi mata bai kai haka ba, har yanzu Dady bai iya cewa
komai ba, Momy ce ta yi tsarab ta ce.
"Rufe min baki mahaukaciya, ni zaki gayawa ina miki sharri, yaushe kika fara girma da zaki min
rashin kunya, lallai na yarda bin maza da kika fara idonki ya bud'e"
Dady ya runshe idonsa yana jin wani yaji mai rad'ad'i a ciki, da kyar ya iya had'iye miyan ya
furta.
"Hajiya ya isa haka, rabu da ita zan d'auki mataki"
Yayi hakan ne domin kar ya nunawa Momy yana cikin hayyacinsa don yaji dad'in gano gaskiya,
tunda ya furta haka ya mik'e cike da sanyin jiki ya wuce falonsa. Momy ta yi dariyar mugunta.
"Dad'an kika gani, ba kin ce ke mara kunya ba, wallahi sai na zama ajalinki shinanniya kawai"
Ai bata k'arasa rufe baki ba Husna ta yi super ta shak'o wuyanta, idonta kamar zasu yo waje
cikin kakkausar muyar mai firgitarwa Husna ta ce.
"Ko ki zama ajalina ko ni na zama ajakinki, sai na sabautaki na nakasaki tunda kike zalunta ta,
wallahil Azeem sai kin wulakanta a rayuwarki, kuma sai na zama silar ajalin yaronki, Azzaluma
mashirkiya, duk abin da kike yi muna biye dake saura k'iris mu fallasaki"
Momy k'ara ta saki mai k'arfi amma ina babu mai jin ta, haka take ta gurnani tana niman
kwacewa amma ina Husna tak'i sakinta, sai da ta fara kakari shirin mutuwa kana ta saketa taja
baya, Husna d'akinta ta wuce ba tare da ta juyowa ba, da gudu Momy ta fad'a d'akinta tare da
sanya key tana mai da numfashi da kyar, idon nan nata kamar zasu fad'o kasa saboda tsoro.
Shi ko Dady bai san abin da ke faruwa ba saboda ya lula duniyar tunani, tsanar Momy ne ke kai
komo a zuciyarsa, duk maganganun ta ba wanda ya yi tasiri a zuciyarsa face k'aryata ta da
yake yi kan sharrin da ta d'aurawa Husna, kiran sallar Magrib ne ya dawo da shi daga duniyar
tunanin da ya lula, cikin azama ya shiga bayi ya d'auro alwala kana ya fita zuwa masallaci.
A b'angaren Husna kuwa, kwanciya ta yi kamar mai barci sai da ta yi minti goma kana ta tashi
zaune tana k'ok'arin tuna abin da ya faru, jikinta duk ya mata nauyi, ga ciwon kai da take ji, tashi
ta yi da kyar ta fad'a bayi ta d'auro alwala kana ta fito ta gabatar da sallah.
Momy kuwa ta kasa fitowa ko falo, Dady bai dawo ba sai da suka yi sallar Isha'i, ya dawo rik'e
da leda a hannunsa, kafin ya shigo sai da ya biya wani shop na ostrich dake bakin titi ya siyo
meat pie da burger tare da yoghurt, d'akin Husna ya ya fara isa ya tura ya ganta zaune kan
sallaya tana karatun Al'Qurni, farin ciki ne ya ziyarce shi sai ya yi mata sallama ta amsa a nutse
tare da dago kai, leda ya mik'a mata ta amaa tare da yi masa godiya, ya ce.
"Ki ci yanzu sannan in zaki kwanta ki rufe d'aki ki kashe fitila, sai da safe"
Cikin ladabi ta ce.
"To Dady Allah ya samu alkhairi"
"Ameen"
Ya wuce sashensa bai bi ta kan Momy ba, yana shiga ya sanya key a kofarsa, wuri ya samu ya
zauna sai da ya ci meat pie da yoghurt d'in kafin ya hau kan system ya fara aikin sa. Momy
kuwa ko da taji Dady shuru bata damu ba sai ma gado data kwanta tana tunanin ta ina zata
bullowa Husna, domin tana kara bata tsorata.
Husna ta kammala komai ta yi shirin barci, ta sanya doguwar riga mai guntun hannu tsayinta ya
kawo mata gwiwa, ta sanya hula tare da kakkab'e shinfid'arta ta gyara, ji ta yi anyi nocking
k'ofarta, cikin sauri ta isa ta bud'e duk tunanin ta ko Dady ne, sai taga Yaya Nura ne, cikin
d'aure fuska ta ce.
"Malam lafiya?"
Murmushi ya yi mata wanda bai kai zuciya ba.
"Kalau"
Ya ce yana binta da kallo yana had'iye yawu tare da kafawa kirjinta ido, ganin ya ta sata a gaba
yana kallonta sai ta ja tsaki zata rufe k'ofa, dakatar da ita ya yi.
"Husna na dawo a gajiye ne, dan Allah ki dafa min pipton da kayan kamshi ki kawo min d'aki,
yunwa nake ji, kuma na duba abincin da Momy ta dafa ba zan iya ci ba"
Husna taja tsaki ta ja.
"Ai dole ka rage min murya, in kuma rashin mutumcinka ya tashi ka karta min baka nuna ka
sanni"
"My sis ki yi hakuri duk wasa ne ai, ki je ki had'a min ina jiran ki"
To kawai ta ce masa ta wuce kitchen fuska daure, Nura ya bita da kallo yana lashe lebensa na
kasa, tare da kashe ido daya yana wani shu'umin dariya ya juya zuwa dakinsa.
[10/28, 6:31 AM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 35 ~ 36_*
Bayan ta gama dafawa d'akinta ta koma ta sanya hijab kana ta d'auki jug d'in data zuba Lipton
din ta wuce d'akin da sauri dan ta fara jin barci.
Tura k'ofar ta yi ta shiga da sallama, ganinsa ta yi daga shi sai gajeren wando da singilet, kauda
kai ta yi ta ajiye akan karamin wani table.
"Gashi nan sai da safe"
"Tsaya na gama sha mana Husna"
Ta isa wurin k'ofa ta ce.
"Banda lokacin tsayawa"
"Kai my sis, to bari na baki wani abu dana siya miki"
Sai ya mik'e ya d'auko wani akwatin sarkan d'an kunne ya mik'a mata, ta kawo hannu zata
amsa sai ya tsafke hannun tare da jawota da k'arfi ta fad'a k'irjinsa, zaro ido ta yi alamar tsoro,
cikin masifa ta ce.
"Meye haka yaya Nura?"
Ya k'ank'ameta ya fara shafa mata baya, kiciniyar kwacewa take yi amma ya rik'e ta da duk iya
k'arfinsa, sai ya jefata kan gadonsa ya fad'a kanta, kuka ta soma tana fad'ar.
"Me zaka min? wallahi ka sake ni, na shiga uku na, Dady ka zo ka ceceni karya kashe ni"
Bakinta ya toshe da hannu d'aya yana fad'in.
"Tun kina k'arama nake hak'onki, ina ta jiran rana irin ta yau da zan mallaki jikinki, shiyasa nake
sassautawa da cin zalinki, saboda in jaki a jikina yadda zaki yarda dani, dan haka yau zan
d'auke abin da za ki yiwa wani d'a namiji tak'ama da shi nan gaba"
Kuka take yi mai tsanani tana son cire hannunsa dake kan bakinta, ta samu sa'ar ganna masa
cizo a yatsarsa, da sauri ya cire hannunsa yana yarfewa.
"Ni kika ciza wallahi yau saina rama ta in da ba k ida k'arfin ramawa"
Ya cire mata hijab, tare da hular kanta, damben kwace kanta ta soma yi, ta mamaye shi ta kuma
ganna masa cizo a damtsensa, wani k'aramin k'ara ya saki tare da rik'e wurin, wani k'arfi taji ya
zo mata ta hankad'a shi ya fad'i ta baya ya bige kansa, da sauri ta mik'e tana k'ok'arin isa k'ofa
ta fita, k'afarta ya kama ya jawota da k'arfi ta fad'i a k'asa ta bige kanta da wani table da yake
gefe, wani wawan k'ara ta saki mai k'arfi har sau biyu.
B'angaren Sadiq kuwa, yana kwance bisa gadonsa ji ya yi duniyan ya yi masa k'unci, gaba
d'aya yaji hankalinsa a tashe, mik'ewa ya yi daga kwancen da yake ya fito falo, kai komo yake yi
ya rasa meke masa dad'i, Husna ce ta fad'o masa arai sai yaji gabansa ya fad'i, Addu'a yake
jerowa na niman tsari daga duk abin k'i, sai ya zauna ya tashi ya rasa sukuni, har fita farfajiyan
gidansa ya yi yana k'ok'arin ya fita waje, sai ya tuna yanzu wurin sha d'ayan dare ba kowa a
waje, yana k'ok'arin shiga falonsa ne yaji wannan k'arar da Husna ta yi har sau biyu, gabansa
ne ya cigaba da fad'uwa yana sauraren ko zai kuma jin k'arar da sanin ta ina ya fito, minti biyar
ya k'ara yaji shuru sai ya wuce d'akinsa ya koma ya kwanta cike da damuwa cunkushe a
zuciyarsa, yana karanto Addu'o'i har barci ya yi gaba da shi.
Dady yana aikinsa bisa system ganin