Showing 45001 words to 48000 words out of 81944 words

Chapter 16 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2391

lokaci ya ja ya rufe, ya yi shirin barci yana k'ok'arin
kwantawa ne ya jiyo ihun Husna har sau biyu, cike da tashin hankali ya fito falon, d'akinta ya
shiga yaga wayam bata ciki, dube-dube ya fara yi a falo, Momy kuwa tana jin wannan k'arar sai

ta k'ara lafewa akan gado cike da tsoro dan ba zata iya fitowa ba.

Dady gunjin kukanta yake ji daga nesa, haka ya soma bin ta in da yake jin kukan, da yake
d'akin Nura yana da ga ciki sosai, har Dady ya isa ba kin k'ofar d'akin da azama ya tura k'ofar
ya shiga da sauri, ganinta kwance a k'asa Nura yana jan k'afarta zai kai ta bisa gadonsa, wani
wawan tsafka Dady ya kai masa ya shak'o wuyansa kana ya zuba masa lafiyayyun mari har uku
yana la'antarsa, wani k'arfi Husna ta ji da sauri ta mik'e ta b'oye a bayan Dady tana kuka mai
ban tausayi, juyowa Dady ya yi ya rungumeta ya kama hannunta suka fito falo, Nura kuwa
jikinsa ne ya mutu da haushin Dady ya b'ata masa show, ga kuma zafin marin da ya yi masa,
gunguni yake yi tare da dafe kuncinsa ya biyo bayansu.

Dady ya soma masifa bakinsa har kunfa yake yi, Husna kuwa kakkarwa ne jikinta yake yi da
fitar hakawayen wahala, Momy ta ji hayani ya yi yawa ta fito falo a tsorace, mamaki ne ya maka
ta, ta shiga tambayar Alhaji abin da ya faru, nan ya ce.

"Ga shi nan ki tambaye shi"

Ya nuna in da Nura yake, cike da tsageranci Nura ya fara magana.

"Momy karki yarda dasu sharri suka kulla min, wannan yarinyar ne fa"

Ya nuna in da Husna take, ya cigaba da cewa.

"Tta ce ta biyo ni har d'aki wai in taimaketa in yi amfani da ita wai feelings ne ke damunta, ni
kuma nak'i yarda shi ne muka soma kokawa da ita, sai na gaura mata mari ta yi k'ara shi ne
Dady ya zo ya ganmu, ya mareni har sau uku yana zagina"

Kan Dady ne ya d'aure yadda Nura ya samu damar shirya wannan k'arya a cikin mintuna
kad'an, jin gina kansa ya yi da jikin kujera ya lumshe ido saboda rad'ad'in da zuciyarsa yake yi
masa.

Momy ne ta yi tsarab ta ce.

"Ai dama Alhaji na fad'a maka yarinyar nan ta dad'e da fara bin maza, wato ma iskancin bai
tsaya a waje ba sai kin zo har cikin gida kin yi da d'an uwanki, anya ma haukan nan da kike yi
ba na zina bace kawai, ko kuma kila ta zina aka haifoki, kinyo gado wurin uwarki"

Wani yunkuri Dady ya yi da k'arfi ya mik'e, lafiyayyan mari ya sakarwa Momy kuga d'aya wanda
ta kusa fad'i k'asa, yana kallonta cikin ido, bai iya furta komai ba ya finciki hannun Husna ya
kaita d'akinsa yasa key ya rufe, sai da ya dai-daita natsuwarsa sannan ya danne fushinsa dan
ya dawo ya bawa Momy hakuri, dan ya cire mata zargin har yanzu bai cikin hayacinsa.
Ta b'angaren Momy kuwa mamaki ne ya cika ta, ta fara tunanin kashinta ya bushe, dan alamu

sun nuna asiri ya karye, ya dawo ya same su a tsaye sunyi cirko-cirko, tsayawa shima ya yi ya
ce.

"Hajiya ki yi hakuri ban san sanda na mare ki ba, kai kuma jeka d'aki zan d'auki mataki akan ta,
ai ban san cewa ta zama haka ba sai yau, na yi tunanin kaine ka nima b'ata mata rayuwa ashe
itace me son b'ata ka, tunda ita ta jima da lalacewa karku damu zan d'auki tsastsauren mataki a
kanta"
Farin ciki ne ya cika Momy da jin kamalansa, har wani ajiyar zuciya ta saki mai cike da murna,
hankalinta ya k'ara kwanciya ta ce a ranta.

'Boka aikin ka na kyau'

Dady yana gama jawabinsa ya wuce sashensa ya barsu nan tsaye. Ita ma Momy d'aki ta wuce
ta ce ma Nura ya je ya kwanta da safe za su yi magana. Shima ya wuce ya kulle k'ofa yana
farin cikin yadda duk suka yarda da sharrin daya kullawa Husna.

Dady yana isa falonsa ya rufe d'akin da key, in da Husna ta zauna ya nufa, cike da tsoro ta
mik'e tana kallonsa, yadda yaga ta tsorata sai ya bud'e mata hannu alamar ta je ta shiga, da
sauri ta isa ta rungume shi ta fara sabon kuka mai tsuma zuciya, shima duk dauriyarsa sai da
ya fidda kwalla, janye jikinsa ya yi ya zaunar da ita kan kujara shima ya zauna kusa da ita, ya
nima da ta fad'a masa gaskiyat abin da ya faru, haka ta labarta masa yafda suka yi tana kuka,
murmushin takaici ya yi ya ce.

"Karki damu ko kad'an ban yarda da abin da suke fad'a ba, nasan baza ki aikata haka ba, kuma
yau na tabbatar ba kida haukar komai sharri ne kawai"

Murmushin jin dad'i ta yi fuskarta kwance da hawaye, shima murmushin ya yi mata ya ce.

"Daga yau a nan d'akin zaki rik'a kwana, zan kwaso miki kayan ki gaba d'aya ki rik'a barci a
nan"

Sannan ya d'aura da yi mata fad'a da nasiha, farin ciki ya cika ta wanda har sai da ya nuna a
fuskarta.

'Yau ni ce Dady kewa nasiha, ashe dama yana sona'

Wannan zancen duk a zuciya take fad'a, a fili kuma godiya ta yi masa, Dady yana mamaki da
yawan godiyarta, ya mike ya shiga toilet ya had'a mata ruwan wanka kana ya ce ta shiga ta yi
wanka dan ta gasa jikinta. Sai ya fita ya je d'akinta ya kwaso mata kayanta duk na amfani ya
kulle k'ofan, ya dawo ya shiga jera mata a waldrop d'insa ya aje wanda suka rage a gefe cikin
jaka, mamakin kayan da take dasu ya shiga yi, gasu masu kyau da tsada kuma ya san ba shi
ne ya siya mata ba,

'To wai duk a ina ta samu wannan kayan?'

Tambaya ya kewa zuciyarsa wanda ba shi da amsar su sai in ya zurfafa bincikensa. Ko da ta
fito ta ga Dady yana ta aikin adana mata kaya sai farin ciki ya rufe ta, wasu kaya marasa nauyi
ta sanya kana ya ce ta kwanta a godonsa, ya rufe ta da bargo ya mata sai da safe. Sannan
shima ya d'auki wani extra bargonsa ya fita falonsa ya kwanta bisa doguwar kujera.
*******

*Washe gari da asuba*

Da zai fita sallar asubahi ya kulke ta a d'akin ya fito ya wuce masallaci, bayan sun idar Dady ya
samu Baba mai gadi a kan bencinsa shima ya zauna, mamaki ne ya cika Baba ya gaishe da
Alhaji shima ya amsa cikin fara'a, Baba ya ce.

"Alhaji in ce dai lafiya, dan bamu taba zama irin haka da kai ba?"

Gajeran murmushi Dady ya yi ya ce.

"Hakane, magana za mu yi, kuma ai dani da kai duk daya muke a wurin Allah face wanda yafi
wani imani"

"Kwarai kuwa Alhaji, amma wasu masu kud'i irin ka ba kowa ke da wannan fahimtar ba"

"Kowa da irin rayuwarsa, Allah dai yasa mu dace. Ameen"

Nan Baba ya tattara tsuwarsa kansa a sunkuyar alamar girmamawa ya ce.

"Alhaji ina saurarenka"

Dady ya nisa ya soma magana.

"Ina niman wata alfarma ce a gunka, Husna zata rik'a yini a gunka inna fita aiki, da safe zan aje
mata uniform d'in islamiyarta a wurinka, in ta dawo boko zan baka kud'i ka siya mata abincin da
zata ci, sannan in lokacin zuwa islamiya ya yi ta shirya ta a je na bokon a nan, in ta sawo daga
islamiya to sai ta jira ni a nan wurinka har sai na dawo sai mu shiga ciki tare"
Mamaki ne ya cika Baba amma sai ya danne, cikin fara'a ya ce.

"Ai ba damuwa Alhaji, Husna na d'auketa jika a guna, ada na yi mata haka balle yanzu"

Dady ya yi masa godiya kana ya mik'e ya shiga ciki, hamdala Baba ya yi ya ce.

"Allah ka k'ara karkato zuciyar Alhaji ya cigaba da gane gaskiya"

***

Dady ne cikin shirin fita aiki, Husna ta shirya ita ma ya ce ta jira shi a waje, ya nufi d'akin Momy,
yana isa yaji tana magana da k'arfi kamar tana fad'a, tsayawa ya yi yana sauraren abin da take
cewa, shuru yaji ta yi, har ya yi yunk'urin shiga sai yaji muryan Nura na cewa.

"Wallahi Momy sha'awarta ya dameni shiyasa har na kira ta don in aiwatar mata, kuma ko a
yanzu ban jenye ba"

"Haba Son na ce maka karka yi haka dan zaka b'ata min aiki na, saboda yanzu Alhaji zai sa ido
sosai akai, kuma kaga yadda na yi asirin rabasu ga shi yana k'ok'arin karyewa, d'an tuggu da
nake had'awa da shi, shi ne kesa asirin na dad'a tasiri a gunsa, dan haka karka sake k'ok'arin yi
mata fyade so nake tabar gidan nan, kaga sai muce haukar data ke yi ne ya yi tasiri a hanka
harta fita ba'a sani ba, ni wallahi Husnar ma tsoro take bani, ina tunanin ko na maidata gun likita
ya k'ara mata wasu maganin sanya haukar da ya bata da tana k'arama, amma ban san ya zanyi
ba dan ina tsoronta"

Nan ta cigaba da jero muguntat da ta shukawa Husna, da azaban da ta bata tun da tana
k'arama, dariyar mugunta Nura ya yi ya ce.

"Yo ai Momy kin fini mugunta wallahi, ji yadda kike ta lissafo abin da kika aika ta mata wanda
ban da labarinsu, ni fa Momy ina so ki bar min ita kawai na cigaba da shanawa da ita"

"Dan ubanka ko kunyata ba ka ji kake wannan maganar, ka fita can waje ka yi iskancinka amma
banda 'yar mazinaciyar nan"

Runshe ido Dady ya yi yana fitar da hawaye mai zafi, ji ya yi kamar ta watsa masa wuta a
zuciya da kallamar 'yar mazinaciya. Maganganunta sun firgitashi sosai, ya yi dana sanin
aurenta tare da la'antar ta a zuciyarsa.

A kankali ya jenye jikinsa ya wuce d'akinsa, sai da ya dai-daita natsuwarsa kana ya fara tunanin
ta ina zai bullowa lamarin nan, dole sai ya yi hakuri yabi abin ta yadda Momy ba zata gane yana
hayyacinsa ba gudun karta koma ta k'ara shirya masa wani sihirin, kyakkyawan tsaro zai cigaba
da bawa Husna, jin motsin an bud'e k'ofa ne ya farka firgigit daga dogon tunanin da ya yi,
Husna ce ta shigo tana yi masa murmushi ta ce.

"Dady zanyi latti fa"

Tashi ya yi da sauri ya ce.

"Ohh sorry my dear mu je"

Ko da suka fito falon ba kowa, Dady ya bama Baba mai gadi kayan Husna da kuma kud'i masu
kauri wanda zai rik'a siya mata abinci. Kana ya bud'e masa gate ya fita da mota, d'aukar Husna
ya yi suka je wurin cin abinci, ya yi musu take away, dan ya yi alwashin ko ruwa Momy ta ba shi
ba zai kara sha ba balle abinci. Sauketa ya yi a makaranta ta shiga kana ya wuce office cike da
damuwa.
[10/28, 6:34 PM] Rahma Kabir🌺: *_Page 37 ~ 38_*


Tun daga wannan rana Dady ya sanyawa Husna ido sosai, duk in da yake a cikin gida tofa suna
tare, in zai fita ya turavta wurin Baba mai gadi, in ya dawo kuma su shiga ciki tare, kwata-kwata
ya daina cin abincin Momy Hatta Husna ya hana ta ci, ya cika fridge d'in d'akinta da drinks da
fruits. Da safe su fita su Karya a restaurant, da rana ya ci a ofiice Husna kuma Baba ya siya
mata, da yamma kuma ya yi musu take away. Wannan sauyi da Dady ya yi yana matuk'ar
damun Momy, amma a fuska Dady bai sauya mata ba ko ta tambaye shi me yasa baya ci, ya ce
shi bai damu da cin abinci ba saboda baya jin dad'in bakinsa, ko da Husna ta daina ci bata
damu ba cewa ta yi tafi nono fari.

Momy ko ta je turakar Dady ba halin sakewa saboda Husna na ciki, haka zata yi ta mita.

"Nifa ana shiga hakk'ina tunda yanzu ka mai do mai kama da mayun nan d'akin ka to sai dai ka
rik'a kwana d'akina"

Shi dai ba um ba um-um, sai ya ce mata zai zo, dana fita ya sanya key ya rufe d'akin ya yi
kwanciyarsa a dogon kujera. Haka zata kwata tana masifa da mita ita kad'ai har barci da sace
ta. Momy ta rasa ta ina zata bullo masa, ko ta zo zata masa magana ya had'e giran sama dana
k'asa ya sha kunu, dole ta hakura ta mai da maganar ta domin yanzu ta soma shakkarsa.
Tunani ta soma na zuwa wurin boka, amma kota tambayi Dady fita sai ya hanata, inta matsa
masa ya ce a bakin aurenta, dole ta koma ta zauna tunda tana son mijinta. Kawarta Haj. Uwani
ta kira ta zayyana mata halin da take ciki nan ta ce.

"Kin ga ki lallab'ashi dan wallahi in kika bari ya kub'uce miki tofa kin rasa shi kenan, dan haka ni
zanje wurin boka ya duba mana lamarin duk abin da ya ce, ko ya bani zan kawo miki sai ki k'ara
gwada wani sa'a"

Cikin farin ciki da shawarar da ta bata suka yi sallama.

******

*Washe gari*

Sai ga Haj. Uwani ta zo, haka suka k'ule a d'aki, ta bata wani kullin magani har uku tare da
bayanin d'aya zata sanya masa a abinci d'aya kuma a ruwan sha, d'aya kuma ta yi hayaki, duka
maganin ana so a yisu a lokaci d'aya, nan Hajiya ta shiga zullumi ta ce.

"To ya zanyi ni da ya daina cin abincina, ko ruwa na ba shi sai ya ce ya gode yanzu ya sha a
d'akinsa, wallahi Khalil ya sauya fa fiye da tunaninki"

Murmushi ta yi mata ta ce.

"Haba Haj. Habee duk kin wani susuce, ya kamata ki gwada kissarki mana, ki lallabashi ya ci,
wallahi a take a nan zaki sha mamaki"

"To shi kenan zanyi k'ok'arin haka, amma ni kwarjini yake min dama kin sanshi ba mai fara'a
bane, to yanzu ya dad'a gimtse fuska ko hira bama yi, rabon da mu kwana tare na manta"

Nan Haj. Uwani ta cigaba da bata shawarwari, har sai da Momy taji ta gamsu sannan suka yi
sallma ta tafi.

Da yamma Husna ta dawo daga islamiya ta zauna wurin Baba tare da ce masa.

"Baba bari na shiga gidan Uncle Sadiq na dawo yanzu"

"A'a fa Husna kin san Alhaji ya bani amanarki, kuma ran nan ya nuna baya so kina hurd'a da
shi, bana so ya dawo yaga baki nan, dan ya kusan dawowa, raina da naki duk zai b'aci"

"Dan Allah Baba ka bari na shiga, yau kusan sati buyu bamu had'u ba zan je na gaishe shi ne
na dawo ka ji"

Ta k'are maganar da shagwaba kamar za ta yi kuka.

"To 'yar Baba dan Allah kar ki dad'e ki dawo yanzu"

"To Baba"

Ta ce cike da murna ta mik'e da sauri ta shige gidan, ta yi sa'a gate d'in a bud'e yake, haka ta
kutsa kai cikin falonsa shima a bud'e ta samu, ta shiga kwada sallama amma ba Wanda ya
amsa, sai kawai ta wuce bedroom dan ta duba shi, a nan ta same shi yana kwance bisa
gadonsa cikin bargo, da sauri ta k'arasa bakin gadon ta zauna ta ce. "Laaa Uncle barci kake yi? ka tashi na zo gaishe ka"

Shuru taji ba amsa, sai ta fara tunanin ya za ta yi ta tashe shi, shi ko Sadiq yana jinta lumshe
ido ya yi saboda zazzabin dake damunsa, kusa da fuskarta ta matsa ta shiga kiran sunansa a
hankali.

"Uncle, Uncle, Uncle"

Ta kira shi har sau uku, a hankali ya bud'e idonsa cikin sarkewan murya tsan k'asa ya ce.

"My Husnaaa"

Ji ta yi tsigar jikinta ya ta shi, nan da nan ta ji bak'on yanayi a jikinta, kallon kallo suka yi na
tsayin minti uku, ta bud'e baki za ta yi magana ya tashi da kyar ya zauna yana fad'ar.

"Wash Allah na"

"Uncle me yake damunsa kamar ba kada lafiya ko?"

Murmushin k'arfi hali ya yi mata ya ce.

"Kaina ke min ciwo da d'an zazzab'i"

"subhanallahi! Sannu uncle"

Ta ce kamar zata yi kuka.

"Kar ki zubar da hawayenki naji sauki, yanzu ta shi ki shiga bayi ki had'a min ruwan wanka, kila
in na yi zan ji k'arfi a jiki"

Kan ya rufe baki har ta mike ta isa bayi ba tare da ta ce masa komai ba, ruwa ta had'a masa
mai zafi kana ta fito ta same shi tsaye daga ci sai gajeran wando da singilet dama a haka ya
kwanta, kallo d'aya ta masa taji cigar jikinta yana ta shi da sauri ta kauda kai ta ce.

"Ga ruwan can na had'a maka"

To kawai ya ce mata ya shiga bayi, bakin Waldrop d'insa ta tsaya ta bud'e, kananan kaya ta ciro
masa ta aje kan gafen miro, gadonsa ta kakkab'e ta gyara kana ta share d'akin ta sanya turaren
wuta a bona, dan Sadiq gaskiya yana da tsafta ga son kamshi shiyasa gidansa kullun tsaf
kamar mai mata, ta fita falo shima ta gyara ko ina.
Sadiq ya fito sanye da kayan da ta fito masa dasu, sai ya ga ta gyara ko ina, motsinta yaji a
kitchen a she ruwan tea take dafa masa, can ya isketa ya tsaya yana kallonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login