Showing 66001 words to 69000 words out of 81944 words
Chapter 23 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
matan *sirrin 'ya mace* sunata hotuna
da amarya, su *fatima demsel* harsa sanabe sai wani shigewa Husnahm take yi dan irin ace
tafi kowa murna da auren lolí ½í¸†í ½í¸š.
Husna jikinta ya yi sanyi da irin wa'azin da taji na girman kyautatawa miji, hak'ik'a ta karantu,
kuma ta d'aura d'amarar kyautatawa mijinta iya k'arfinta.
****
Da misalin k'arfe takwas da rabi, motocin d'aukar Amarya sun cika layi, matan Kawu Suleiman
da matan mak'otansu, kai harda Momyn Yasir ta taho dan Yasir yaje ya yi mata bayanin komai,
sai da ta yi masa fad'a akan abin da ya yi, daga k'arshe ta yi masa nasiha da karya sake aikata
irin haka.
"Domin iyaye ba abin wasa bane, yanzu in iyayen Sadiq su kaji aurensa ya zasu d'auka?
gaskiya karka sake kamanta irin haka, dan abin da iyaye suka k'i shi tofa ku guje shi, sai ku
d'aura da Addu'a"
Nan dai ya bata hak'uri harta sakko ta biyo 'yan d'aukar Amarya a motarta.
Dady ne zaune a falon baki in da ya kira Husna ta zo falon sanye cikin leshi brown riga da zani
rafa, ta d'aura dankwali da babban mayafi ya sauka sosai a jikinta ta rufe kanta, sai k'amshin
Amare take yi, zama ta yi akasan kafet, ba ta yi minti biyar da zama ba Sadiq ya shigo sanye
cikin shadda brown riga da malun malun, ga hula milk ya d'aura, wuri ya samu ya zauna k'asa
kan kafet gefen hannun hagun Dady ita kuma Husna gefen dama. Nan Sadiq ya gaida Dady
kana suka yi shuru na tsayin minti biyar, Dady ya nisa ya ce.
"Husnah baki ga Uncle d'inki bane?"
Kanta na sunkuye da murmushi a fuskarta.
"Uncle ina yini"
Ya amsa cike da kulawa, daga nan kuma duk su ka yi shuru kowa da abin da yake kitsawa a
ransa. Dady ya yi gyaran murya.
"Sadiq ga Husnahm nan na baka ita amana ka kula da ita kamar yadda ka kula da ita a baya, in
ta yi kuskure ka tsawatar mata, ka kula da ibadarta, yanzu nauyinta ya dawo hannunka"
"Insha Allah Dady zan kula da ita"
"Yauwa, kema Husna ga Uncle d'inki shi ne Mijin dana zaba miki, ki yi masa biyayya dan
Alajannarki yana tafin k'afarsa, in kin bi shi sauda k'afa ki shiga aljanna in kuma kika sab'a masa
ki shiga wuta, kuma ki kula da ibadarki, sannan ku d'aura niyyar za ku yi zaman aurenku bisa
Ibada ne"
Nan ya cigaba da yi musu nasiha mai ratsa zuciya wanda Husna sai kuka ta ke yi mara sauti da
tunanin sabon rayuwa da zata shiga.
"Sadiq zaka iya tafiya yanzu zan taho maka da matarka"
Sadiq ya mik'e cike da jin kunya, ya yi godiya kana ya fita. Dady ya mik'e ya kama hannun
Husna ya nufi part d'in Momy Habee.
Zaune take da wasu kawayenta su uku sunata hira da shewa, bud'e d'akin da Dady ya yi ne
yasa su yin shuru don ganin mai shigowa, ya shiga fuskarsa ta mau babu walwala ya ce.
"Gata ta zo miki sallama"
Momy jikinta a sanyaye ta mik'e ta isa wurin Husna ta ce cikin sanyin murya.
"Husna Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a na gari"
Idon Momy ya kawo kwallar nadama, ta cigaba da cewa.
"Husna ki yafe min duk abin da na miki, hak'ik'a nasan na azabtar da ke na yi nadamar abin da
na yi miki, kaicona! ban san ina son ki ba sai da naga dagaske gidan zaki bari"
Ta fashe da kuka sosai, Husna zuwa ta yi ta rungumeta ta ce.
"Momy na yafe miki, nima ki yafe min wasu abubuwan dana yi miki"
Nan suka had'u suna kuka Dady ne ya yi gyaran murya ya ce.
"Husnah ta shi mutafi"
Momy ta ce.
"Bari mu taho tare sai mu wuce"
Dady ya k'ara daure fuska.
"Ki yi zamanki ni zan kaita, bana son ganin k'afarki a gidan ta"
Yana gama fad'ar haka ya kamawa Husna hannu suka tafi suka bar Momy a tsaye cike da jin
zafin abin da Dady ya ce mata. Jiki a sanyaye ta koma ta zauna, ta rafka ta gumi, sai yau take
jin son Husna na ratsa zuciyarta a dai dai lokacin da zasu rabu, nadama ya ratsata, wata
k'awarta ce ta da fata ta ce.
"Hajiya ki yi hak'uri, ki yi k'ok'arin amfani da shawarar da muka baki har ki jawo hankalin mijinki
gareki, ki watsar da shirman da kika aikata a baya kuma ki rabu da Haj. Uwani dan wallahi ita
ce ta sanyaki hanyar halaka"
Momy ta nisa ta ce.
"Kwarai Haj. Uwani ta taka muhimmiyar rawa wajen bani mugayen sharawa, zan gyara
halayyata kafin Alhaji ya yanke min hukunci har Allah yasa in shawo kansa"
***
Dady suna fita ya wuce da ita part d'in su Inna, nan ma fad'an suka mata kana suka rankaya
waje, Dady ya sanya Husna a seat d'in bayan motarsa shima ya shiga sai Sadiq ya zauna gefen
Dady suka sanya shi a tsakiya, sai Minal ta shiga gaban mota Yasir ya tuk'asu. Sauran motocin
suka kwashi mutane, Momy Halima ta d'auki su Kausar a motarta da su Inna, haka aka rankaya
kai Amarya gidanta.
Yasir ya yi parking a haraban gidan, da yake har sun samu mai yi musu gadi, duk suka fito Dady
ya kama hannun Husna ya isa da ita bakin K'ofar d'akin ta, dama ya gaya mata wasu Addu'o'i
da zata karanta tun a mota in sun k'araso, nan ta karantosu sannan Dady ya bud'e d'akin ta
shiga da k'afar dama, suka shiga cikin falon sauran mutane na biye dasu a baya, Dady ya
zaunar da Husnahm a kujera, kana ya ce kowa ya shiga yaga d'aki ya bada minti sha biyar, aiko
nan matan da suka rako amarya suka shiga d'akuna suna kallon irin dukiyar da aka zuba a
gidan, lungu da sak'o na cikin falon sun lek'a dan kashe kwarkwatar ido, wasu na fita wasu na
shiga har suka kammala, sannan suka yiwa Amarya sai da safe suka fita, kowa ya koma motar
daya kawoshi suka zauna.
Dady ya kira Yasir da su shigo da Ango sannan ya fita ya basu wuri. Abokan Ango suka gama
gaisawa su Minal kawayen Amarya, suka yi siyan baki sannan suka mik'e dan tafiya, a nan ne
Husna ta fara kuka kamar ranta zai fita ita a dole sai ta bisu, cike da tausayawa Sadiq ya rik'eta
har suka tafi. Kana ya sanya mai gadi ya rufe gidan.
Dady yana zaune a mota Yasir yana tukasu, sai Minal da take kusa da Yasir suna hira
k'asa-k'asa, Dady hawaye yaji yana saukar masa ji yake kamar ya koma ya d'auko Husna,
tausayinta yake ji amma dole ya yi hak'uri dan auren shi ne mafita a gareta, yanada tabbacin
Sadiq zai kula da ita fiye dashi ma, tunanin Zainab ya dawo masa sabo, yana tuno ranar
aurensu da irin soyayyan da suka sha, ji yake kamar yaje Kaduna dan jin halin da take ciki,
amma ina hakan ba zai yuwu ba saboda korarvkare da 'yan uwanta suka yi masa, da wannan
tunanin a ransa har suka isa gida.
Da kyar Sadiq ya lallasheta ta yi shuru, mik'ar da ita ya yi ya kama mata hannu ya kaita d'akinta
ya ce.
"Nan ne d'akin ki, yanzu ki samu ki natsa bari naje d'akina na watsa ruwa"
Shagwab'e fuska ta yi ta ce
"Uhum ni Uncle tsoro nake ji ba zan zauna ni kad'ai ba"
"Husna ina fa cikin gidan ba fita zanyi ba, ki yi hak'uri ki zauna naje da dawo kinji".
Gyada masa kai ta yi alamar to, nan ya fita ya barta a tsaye, Waldrop d'inta ta bud'e taga an
jera mata kaya a ciki, dubawa ta yi ta ciro wani doguwar rigar barci mai hannun bes tsayinta ya
kai k'aurinta, ta tub'e kayanta ta sanya wannan rigar ta k'ulle gashinta ta sanya hulan barci ta
d'auki gyalenta ta yafa a jikinta, kwanciya ta yi kan gado tana sauke numfashi, bata wuce minti
biyar da kwanciya ba sai ga shi ya shigo rik'e da tire a hannunsa da leda akai, sanye yake cikin
farar jallabiya mai guntun hannu na barci, ya ce.
"Husna ba dai kin kwanta ba? tashi muci abinci, dan na san da wuya in kin ci abincin kirki yau"
Da sauri ta ta shi ta zauna ta ce
"Wallahi ni Uncle k'ishin ruwa ma na ke ji"
"Ok, ta shi ki je kicin yana nan a fridge saiki d'auko mana drink da ruwa"
Ido ta zaro ta ce.
"Uncle ni fa tsoro nake ji"
"kai Husna yaushe kika fara jin tsoro ne haka? nan fa gidanki ne dole ki koyi zama ke kad'ai
saboda wata ran zan fita aiki nabarki ke kad'ai a ciki har sai na dawo, yanzu dai yi huk'uri ki je ki
d'auko mana babu abin da zai kama min ke"
Cikin sanyin jiki ta fita, kicin d'in ta isa ta d'auko ruwan da drinks d'in, gyalenta ne ya zame mata
akai sai ta ji kamar motsin mutum a bayanta, da gudu ta arce ta fad'a d'akinta tana haki ta saki
drinks da ruwan a k'asa ta k'ank'ame Sadiq tana maida numfashi, gyalen ma ya zame mata
yana falo, wani irin shock Sadiq yaji gaba d'aya ya shiga wani yanayi, duk kan gab'ob'insa sai
da suka amsa da bak'on al'amari, nan da nan idonsa sun sauya sun d'an yi ja tare da
k'ank'ancewa, d'ago fuskarta ya yi cikin sanyin murya ya ce.
"Husna meye ya baki tsoro?"
A hankali ta bud'e ido suka sauka kan na shi, sun d'auki kusan minti uku suna kallon juna, take
nan ta ji ya saukar mata da kasala ta yi saurin kauda idonta ta mai da su suna kallon k'irjinsa,
cikin sark'ewar murya ta ce.
"Uncle motsi naji a bayana kamar na mutum, shi ne na rugo da gudu, Allah ni fa tsoron gidan
nan na ke yi, ka maidani gidan Dady"
Ta k'arasa maganar cikin shagwab'a, murmushi ya yi mata ya ce
"Ke dai kin cika tsoro, kuma ba in da zan kai ki kin zo kenan, dan aurenmu babu saki yarinya,
sakeni karki sa na fad'i ba shiri"
Ya karasa maganar da zolaya yana jan hancinta, cikin shagwaba ta ce
"Uhum ni ban da Karfin da zan kayar da kai, dafa har goyani kake yi fa"
"To na ji, yanzu muci abinci kin ga dare yanayi"
Ba musu ta sake shi cike dajin kunya, sai yanzu ta tuna da irin shigar dake jikinta ga gyalenta
yana falo, nan suka yi ciye ciyensu da Yasir ya siyan musu da sauran drunk, tun tana
nuk'u-nuk'u har ta saki ji, suka ci suka k'oshi. Husna ta shiga bayi ta wanke baki ta dawo ta
zauna bakin gadonta, Sadiq ya mik'e ya kai kayan kicin ya wuce d'akinsa, ya wanke baki ya
zauna bakin gado yana tunanin ya kwanta a nan ne ko yaje dakin Husnah?.
[11/3, 8:08 AM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 57 ~ 58_*
Yanke shawara ya yi bari ya kwanta a binsa in taji shuru ta yi barci. Ya kashe fitila ya yi Addu'a
ya kwanta cike da tunani barkatai. Husna tana zaune tana ta jiran dawowar Sadiq amma taji
shuru, komawa ta yi ta kwanta ta rufa da barko, runtse ido ta yi ko kila barci zai kwasheta,
amma ina tsoro ya hana ta barci sai juyi take yi, ko fitilan d'akin ta kasa kashewa, har kusan
misalin k'arfe 12am na dare barci bai d'auketa ba, cikin jin tsoro ta mik'e ta bud'e d'akin a
hankali tana waige-waige cikin sand'a take taku harta isa d'akin Sadiq ta murd'a k'ofar ta yi sa'a
a bud'e yake, sai dai akwai duhu, haka ta shiga tana zare ido tana lalube harta isa bakin
gadonsa, a hankali take kiran sunan shi amma taji shuru yak'i amsa mata, kuma shima bai
samu yin barcin ba saboda tunanin daya zurfafa a ciki, yana jin lokacin data bud'e d'akin nasa,
tana lalube har hannunta ya kai kan k'afansa, ta tab'a shi amma ya yi mata shuru kamar yana
barci, kuka ta fara yi a hankali, sannan ta hau gadon gefensa ta kwanta, ta k'udundune kamar
mai jin sanyi, Sadiq yana jin nishin kukanta bud'e ido ya yi ya juyo gefen data kwanta sai ya
mirgino ya jawota jikinsa da k'arfi ya rungumeta, wata 'yar k'ara ta saki, sautin kukanta ya k'aru,
cikin muryan barci Sadiq ya ce.
"Husna me yake da munki ne? ashe baki yi barci ba? mema ya kawoki d'akina?"
Ya jero mata wannan tambayoyi, cikin kuka ta ce.
"Uncle tsoro nake ji"
K'ara matseta ya yi jikinsa har suna iya jin bugun zuciyan juna.
"Ok, shi ne kuma zaki zo nan ki hanani barci ko?"
Shuru ta yi tana shakar kamshin turarensa. Hannu yasa ya d'ago fuskar ta, ko da suna cikin
duhu Husna ta san fuskarta yake kallo, suna shakar numfashin juna, bugun zuciyarta ne ya
k'aru da kuma jin wani bak'on al'amari, harshensa yasa ya soma bin hawayen fuskarta yana
gogewa, wani irin yanayi suka cinki kansu wanda suke fidda numashi da sauri, sai da ya goge
mata tas sannan ta sauke wani gwauran numfashi, a hankali Sadiq ya kira sunanta sai ta b'oye
kanta a jirjinsa tana mai da ajiyar zuciya a hankali, murmushi Sadiq ya yi domin ya gano Husna
ba zata yi masa wuyar juyawa ba, d'ago fuskarta ya yi ya had'e bakinsu, tsawon minti goma
kana ya saketa. wani iron kuka ne Husna ta b'arke da shi wanda bata san dalilin yinsa ba, shin
na farin cikin ne ko kuma na bak'on al'amari da Uncle yazo mata da shi. Yana rungume da ita ya
yi ta lallashi har barci ya yi a won gaba dasu.
*******
Haka Sadiq ya yi ta koyawa Husna abubuwa masu wuyan fassarawa, na yau daban na gobe
daban, Husna ko tsananin jin kunyarsa take yi wanda bata iya had'a ido da shi. Cikin k'ank'anin
lokaci ya kowa mata yadda zata saba da shi, shak'uwa mai k'arfi ya kullu a tsakanin su a cikin
tawon kwana bakwai, kullun Sadiq yana gida masallaci kawai ke fidda shi waje, da yake ya
samu hutu na 2weeks a gun aiki, kullun daga gidan Dady ake aiko musu da abinci, Yasir ne mai
jigilan kawo musu.
*****
*Bayan kwana goma sha biyu*
Yau ya kama Friday kwana goma sha biyu da auren su, tun da suka wayi gari Husna ta fad'a
kicin domin ranar ne zata fara girki kuma ranar ne Abokan Ango zasu zo cin girkin Amarya, da
misalin k'arfe 9am na safe, sai ga Minal ta shigo gidan nasu domin dama tun jiya Husna ta kira
ta akan tazo ta taya ta aiki, dama Sadiq tun safe ya fita, haka suka duk'ufa girki, tunwon
shinkafa da miyan agushi, sai miyan kib'ewa danya da Uncle Sadiq ya ce yana so, sai fried rice
da suka yi, peppe chicken, sai sultan chips mai had'e da kayan cikin sa, cikin k'ank'anin lokaci
gida ya gauraye da k'amshi, Minal sai ta zama 'yar kallo domin ita bata iya girki sosai ba, iya ka
ta taya Husna yanke-yanke da kuma hira, juice d'in kankana ta yi da soya milk juice. Ta sanya a
fridge, Minal da ta d'an d'ana sai santi take yi.
Da misalin k'arfe 1pm Husna ta kammala komai harta zubasu a masubi, a falo ta shirya kulolin a
carpet, juices d'in ne bata fito da suba suna fridge, wanka ta yi ta sanya wata purple atamfa mai
d'auke da fulawowi fari da yalo, d'inkin fitted riga da siket ta yi kyau sosai, ta yi d'auri mai kyau
kamar gwagwaro, turaruka ta fesa kana ta fito bayan ta yi sallah. Minal binta ta yi da kallo tana
ya ba kyau da Husna ta yi, murmushi ta sakar mata ta ce.
"Malama ya da kallo kamar baki sanni ba"
Ita ma murmushin ta mayar mata.
"Kalau sisi, kawai na ga Amarcin ya amsheki ne, gaskiya uncle ya iya kiwo"
K'arasowa ta yi da sauri wurinta, ta kai mata dukan wasa sannan ta zauna tana cewa.
"Kai sis bana son sharri, dama can haka nake"
Nan dai Minal ta cigaba da zaulayarta suna hira da barkwanci. Kallo suke yi har misalin k'arfe
biyu da minti goma na rana, sai ga sallaman Sadiq ya shigo, cikin nutsuwa Husna ta mik'e ta isa
wurinsa, daskarewa ya yi a tsaye yana kallonta domin wani bala'in kyau ta yi masa, murmushi
ta sakar masa ta amshi ledan hannunsa tare da yi masa sannu da zuwa, shima murmushin ya
mayar mata da cewa.
"Yauwa, ya aiki? dan nasan yau kin gaji"
"Aiki Alhamdulillah Uncle, dan ba wani yawa ma Minal kuma ta taya ni wasu ai"
K'arasawa suka yi cikin falon ya zauna suka gaisa da Minal nan ta shiga kicin ta ajiye abin da
Uncle ya siyo, kayan miya ne da sauran abin buk'ata. D'akinsa ta wuce shima ya bita a baya
suna shiga ya rungumeta ta baya yana shak'ar k'amshin turarenta ya ce.
"Kai my Husna wannan kyau haka da kika yi, sai ki sanya na kasa fita ko nan da can"
Dariya ta yi.
"kai Uncle ai ina yi kullun fa"
"Eh, amma yau dai kwalliyar taki tasha bamban dana kullun"
"Tom Uncle nagode, yanzu ka shiga ka yi wanka"
"No ba zanyi wanka yanzu ba, domin su Yasir suna hanya"
"Ok, anjima sai ka yi ai".
Falo suka koma, bayan minti biyar sai ga kiran