Showing 24001 words to 27000 words out of 81944 words
tashin hankali Anty Binta
ta kwantar da ita a k'asa, ruwa suka yayyafa mata ta farfad'o amma bata cikin hayyacinta. Da
sauri suka nufa asibiti da ita. Sai da ta kwana biyu bata dawo hayyacinta ba, a kwana na uku ne
ta dawo dai dai cike da k'unci da damuwa hawaye ne ke fita idonta ba tare da sauti kuka ba, su
Baffa sunyi nadamar hukuncin da suka yanke mata a kan raba ta da Khalil, satin ta d'aya aka
sallameta tare da magunguna.
Tun daga wannan lokacin Zainab na fara rayuwar kunci da zaman *Kad'aici*. Ta fita sabgar
kowa sai abin da ya shafe ta take yi, bata magana sai ya kama, haka cin abincinta ya ragu,
walwala da dariya ya yi k'aura a rayuwarta, tun su Umma suna lalla shi da mita har sun zuba
mata ido tare da yi mata Addu'a.
*****
A b'angaren Khalil kuwa, yana hanya yana kuka har ya isa kano, direct gidan Baba Husain ya
zarce, ya iske su basa nan ashe kakarsa ce ta rasu suna gidan mahaifiyar Babanshi, cikin
damuwa ya isa gidan ya iske wannan tashin hankali, haka aka yi mata wanka tare da kaita
makwancinta.
Bayan anyi sadakar bakwai kowa ya watse, Khalil ya samu Baba Husain, ya ba shi labarin abin
da ya faru lokacin daya je Kaduna, Baba Husain bai ji dad'i ba amma sai ya ce.
"Ai sunyi dai-dai tunda dama bada yawunmu kuka yi auren ba, dan haka kaje ka cigaba da
rayuwa da 'yar taka sai ka yi k'ok'arin sama mata wata uwar wacce zata rik'e ta"
Daga wannan maganar bai sake cewa komai ba, Khalil ya yi masa godiya da sallama, d'akinsa
ya shiga ya hada kayansa gaba d'aya ya fita dasu ya sanya a mota tare da kayan Husna ya ce
masu Baba Husain zai koma gidansa, ba musu suka amince dan dama sun ce sun cire
hannunsu akansa, ya yi duk abin da ya yi ra'ayi duniya ce baza su takura masa ba.
Haka ya soma rayuwa daga shi sai Husna acikin gidan ya sata a makaranta shi yake kaita ya
d'aukota, wannan dalilin ne yasa ya fara samun sab'ani a office dinsu saboda yawan latti da
yake yi.
Wata rana ya dawo daga aiki ya shirya Husna suka tafi wajen wasan yara, sun jima agun kana
ya d'auketa suka shiga wani shopping complex dan ya yi musu siyayya, suna zagawa yana
d'aukar wanda yake so yana sawa a basket, wata mata 'yar matashiya ce ta shigo yin siyayya,
ta d'auki kwando ta soma zagawa har gurin dasu Khalil suke, abin mamaki Husna tana ganinta
ta kama mata zani, tana sonyin kuka alamar shagob'a dan ta d'auketa, matar ta kalli Husna sai
ta fincike zaninta, sai Husna ta fashe da kuka, Khalil da ya yi gaba sai ya jiyo kukanta da sauri
ya biyo layin daya bari duk tunaninsa tana biye da shi a baya, ita kuma matar ganin Khalil ya
doso su sai taji gabanta ya fad'i zuciyarta na harbawa da sauri- da sauri hakanan taji diran son
Khalil lokaci d'aya, kafin ya k'araso ta yi sauri ta d'auketa tana jijjigata, ikon Allah kuwa sai
Husna ta lafe a jikinta ta yi shuru tare ajiyar zuciya. Ko da ya k'araso mamaki ne ya cika shi bai
ce komai ba, sai sannu da ya cewa matar ya mik'a hannu zai amshe ta amma tak'i zuwa sai ta
k'ara lab'e a jikin matar, abin sai ya kuma ba shi mamaki, ya yi ya yi tazo gunsa sai ta k'i, dole
ya hakura yaje ya gama siyayyarsa ya biya kud'in sai ya kai mota kafin ya dawo ciki, dai-dai ita
ma matar ta gama nata siyayyar Khalil ya biya mata tare da yi mata godiya da rik'on Husna,
Matar ita ma godiya ta yi masa sannan suka fito tare, Khalil ya tambayeta ina zata?, Sai ta gaya
masa ya ce ta shiga ya rage mata hanya, haka ta shiga zuciyarta fari kal dan murna, zuna
hanya ba mai cewa kowa komai, harya kai ta k'ofar gida lokacin Husna ta yi barci, ta kwantar
masa da ita a sit d'in data ta shi ta d'auki siyayyarta ta yi mata godiya, sannan ta buk'aci daya
bata number sa, kamar ba zai bata ba amma daga bisani ya bata.
Tun daga wannan lokacin wannan matar mai suna Habiba wacce akafi sani da Haj. Habee
tasa Khalil gaba da kira, tun yana kin d'auka har ya soma saki jiki da ita suka fara sabawa, sai
dai baya jin sonta ko kad'an a ransa, sai dai akwai fahimtar juna a tsakaninsu sosai, Habeeba ta
nace masa har sai da ya amince zai aureta amma bisa sharad'i d'aya, in zata rik'e masa 'yarsa
da amana marainiya, bai gaya mata labarinsa ba kawai dai tasan wanda ya kamata ta sani, cike
da zumud'i ta amince.
Habiba d'iya ce ga Alhaji umar wanda ya rasu da dad'ewa, ta yi karatunta digree a bannin
kasuwanci, ta yi aure da yaro daya mai suna Nura Allah ya yiwa mijinta rasuwa bisa hatsarin
mota da ya yi, ya bar mata dukiya ba laifi wanda daga nan ta shiga rayuwar zaman kanta tana
kuma kasuwancin kaya gari-gari, bayan mutuwar mijinta ta samu wasu neman amma taki yin
aure saboda tana cin duniyarta da tsiinke har zuwa yanzu da ta hadu da Khalil taji tana sonsa
kuma da aure, mutane da dama sunyi mamaki sosai da aurenta da Khalil saboda ya kasance
mata shi wasu suna ganin ma zata girme masa, kawai dai tana da jiki mai kyau da kuma k'arin
shan magani da mayuwan gyaran jiki.
Biki wata guda aka sanya har ya zo aka d'aura, ta tare a gidansa tare da d'anta Nura, daga nan
kuma kulawar Husna ya koma wurin Haj. Habee wacce suke kira da Momy, zuwanta gidan ba
dad'ewa tasa Khalil ya kawo mai gad'i da mai taya ta aikin gida Jimmai, da farko ita ke kai
Husna makaranta ta d'auko ta, daga bisani mai aikinsu jimmai ta cigaba da kaita tana d'aukota
hakan yasa Husna ta saba da mai aikinsu sosai da kuma Baba mai gadi, da farko Momy ta yi
mata riko na amana daga bidani kishi da yadda Khalil kewa Husna yasa ta fara jin haushi tare
da zugan da aminiyarta Haj. Uwani ke mata, ta fara zallawa Husna ba tare da sanin Khalil ba,
sai Nura ne d'an so ko da ya girma bata daina sangarta shi ba.
******
A Kaduna kuwa Zainab ta cigaba da rayuwar k'unshi da *kad'aici*, duk iya kulawa tana samu
amma sam tak'i komawa yadda take da, ana cikin haka ne su Baffa suka sanya ranar aurenta
da yaya Al'amin. Yaya Al'amin ya yi farin ciki sosai da haka ta bangaren Zainab kuwa fad'e ma
bata baki ne, dan bata so sai dai ta d'auki alkawarin zata yi biyayya ko dan ta gyara kuskuren
da ta yi a baya. Biki wata d'aya aka sanya, nan da nan lokaci ya yi aka d'aura auren Zainab da
Al'amin, an kai ta gidansu Inna Kulu wanda yake Malali, part d'inta daban haka suka ci amarci
cikin rashin sakin jiki da juna, Al'amin ya yi iya k'ok'arinsa amma abu ya ci tura sai dai lallab'ata
ya cigaba da yi, suna zaman hakuri duka.
*********
Bayan shekara 3 Zainab na d'auke da juna biyu haihuwa yau ko gobe, wata rana tafiya ya kama
Al'amin garin Enugu kan aikinsa, ya yi sallama da kowa ya tafi. Tun safe da tafiyarsa Zainab
take nak'uda sai yamma ta haihu Yaro Namiji mai kama da ubansa sak, dangi da abokan arziki
ana ta zuwa musu barka da yake bata dawo gida ba.
Cikin tsakiyar dare aka yiwa Abba Iro waya ya d'auka, mummunar sako aka isar masa bai
k'arasa saurare ba ya saki salati, nan da nan cikin daren Abba ya fara kiran 'yan uwa, cike da
tashin hankali kan asubahi gidan ya soma taruwa da dangi makusanta, Zainab na sashinta tare
da Anty Binta basu san wainar da ake toyawa ba sunata barci. Bayan sallar Asuba gida ya cika
da 'yan uwa da abokan arziki, kuma dai-dai lokacin an shigo da gawar yaya Al'amin wanda duk
jini ya lullube fuskarsa nan gida ya hautsine da koke koke, hayaniya ya soma yawa Anty Binta
tana daki bisa dadduma ta idar da sallah ta mik'e cikin sauri dan ganin ko a cikin gidan ne ake
hayaniyar, koda ta fita ta yi arba da mumunar tashin hankali da kuka ta koma part din Zainab, a
hargishe Zainab ta tashi tana tambayar lafiya? kuka ne yaci k'arfinta, Anty Jidda ce ta shigo a
guje tana rusar kuka ita ma, Zainab kamar an tsikareta ta mik'e, fita harabar kigan ta yi taga
cikowar maza sosai a gidan bata damu da rashin mayafi a jikinta ba ta doshi inda suke, lokacin
an gama masa sutura fuskarsa ne bude an fito da shi babban falon gidan mata da maza zagaye
da gawarsa sai kuka mara sauti da suke yi tare da yi mata Addu'a, haka Zainab ta kusa cikin
falon abin da ta gani ne ya razanata, baya ta yi a sume da sauri wanda suke kusa da ita suka
tare ta. Aka yayyafa mata ruwa ta farfad'o, kallon kowa take d'ai d'ai cike da tashin hankali,
idonta akan gawar Al'amin ya tsaya, hakan ya tabbata ba mafarki take yi ba ta matsa kusa da
shi ta k'urawa fuskarsa ido, Addu'a ta shiga jero masa wanda a lokacin ta bawa kowa mamaki,
bayan ta gama iyaye dama sunyi masa Addu'a aka d'auke shi sai makwancinsa.
Zainab ta nima kuka ta rasa sai dai bin mutune da take da ido sai ajiyar zuciya take yi, ashe ma
kuka _Rahma ce_ domin kuwa Zainab ta shaida haka a wannan lokaci, ta zama tamka kurma
kamar gunki bata iya motsi mai k'arfi, domin a tsorace take bata iya cewa uffan bata san tasha
ruwa ba balle abinci, da kyar ake matsa mata ta kurba ruwa wani ma sai an kamata an mata
d'ure.
Tana cikin wannan yanayin har tsawon mako d'aya da rasuwar Al'amin kuma ya yi dai-dai da
kwanan yaronsu a duniya, a kayi sadakar bakwai tare da rad'in sunan yaro suka sanya masa
Muhammad Al'amin, yaci sunan babansa. Al'amin ya tafi ga kuma sabon Al'amin.
*********
*Bayan sadakan arba'in*
Iyayen Zainab suka tafi da ita gida, aka gyara mata d'akinta ta cigaba da zama a nan tare da
renon yaronta, sai a yanzu ne take iya kuka, kowa sai ya kwanta amma banda ita domin kwana
take tana sallah da kuka, barci b'arawo ke sace ta. Duk ta lalace ta yi duhu, bata iya cin abinci
sosai, duk family suna tausaya mata, sam ba ta yi rayuwar auren jin dad'i ba, na farko sai a
hankali wannan ma gashi ya rasu. A wannan lokacin su Baffa da Yaya Ismail da Aliyu suka yi
dana sanin rabata da Khalil, a yanzu suna matuk'ar tausayinta kuma suna son suga sunyi mata
abin da zai sanya ta farin ciki.
*Rahma ce*
[10/20, 11:10 AM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KAÆŠAICI*
© *Rahma Kabir*
*Wattpad:*@rahmakabir
*_Page 19 ~ 20_*
*A Kano*
Husna har ta saba da rayuwar *kad'aici* da k'unci, a makaranta kullun ita ce cikin k'azanta ana
kyararta, gata da k'ok'ari amma bata samu mai tallafa mata ba, kullun Khalil yana fama da aiki,
kuma a yadda Momy take nuna masa Husna bata kukan maraici.
*****
*Sadiq Aliyu mai kanti*
Ya kammala karatunsa daya fita kasar India b'angaren engineering, ya dawo gida Nigeria cike
da zumud'in ginin iyayensa. Ko da ya sauka a gida a part d'in Umma ya dira wato kakarsa, nan
da nan gida ya hautsine da murna sai farin cikin dawowarsa su ke yi har zuwa dare, Sadiq yana
zaune gefen Umma yake cewa.
"Umma ni banga Anty Zainab bane? Ga shi har Anty Binta tazo, ita kuma taki zuwa kuma nasan
uncle Al'amin ba zai hanata zuwa ba"
Umma murmushi ta yi ta ce.
"Kaje d'akinta tana ciki tasan ka dawo ai"
Mamaki ne ya mamaye shi. "Umma dagaske kike yi? wai ko dai tsufa ne ya saki makuwa"
Hawaye yaga ya gangaro mata ta ce. "Allah ya yiwa Al'amin rasuwa wata biyu da suka wuce"
Zmmbur ya mik'e kafin ya kai ga jefa mata wani tambayar ta mik'e ta shige d'akinta. Tashin
hankali ne ya ziyarce shi, d'akin Anty Zainab ya nufa ya iske ta kan sallaya zaune tana jan carbi,
da sauri ya isa gareta yana mai zubda kwalla, rungumeta ya yi yana fitar da hawaye mai zafi, ita
ma nan ta b'arke da nata kukan sun kai lokaci mai tsawo a haka, Anty Jidda ce ta shigo rik'e da
little Al'amin a hannunta yayi barci, tsayawa ta yi tana kallonsu cike da tausayawa ta yi gyaran
murya.
"Kai Sadiq tashi ka wuce d'akinka dare ya yi"
Juyawa ya yi da jajayen idonsa. "Ummi dama ashe uncle Al'amin ya rasu shi ne baku gaya min
ba?"
K'arasowa ta yi ciki ta kwantar da little Al'amin sannan ta dawo kuwa da Sadiq ta dafa kansa,
lallashinsa ta yi da nasiha mai kwantar da zuciya kana ta umarce shi daya wuce d'akinsa, ba
musu ya wuce cike da tunanin uncle d'insa da irin shakuwar da suka yi.
Ta koma wurin Zainab ta bata baki sosai har ta lallabata ta kwanta kana ta jawo mata k'ofa ta
rufe sannan ta wuce part d'insu.
Tun daga wannan rana Sadiq yake zama d'akin Anty Zee da haka ne ta d'an saki jiki suyi hira,
su Umma sunji dad'i sosai da sauyawar Zainab tunda har falo tana fitowa ko da ba hira take yi
ba sai dai ta zauna shuru, in kuwa ta yi magana tofa da Sadiq ne, Da wowarsa ya sauya gidan
gaba daya. Sadiq bai san cewa Zainab ta auri Khalil ba balle harda yarinya tsakaninsu, a
saninsa dai cewa Al'amin ne farkon Mijinta kasantuwar body's school ya yi a secondary sannan
daga dawowarsa Abbansa ya turashi k'asar India can ya yi digree d'insa.
***
Bayan dawowarsa da wata hud'u ya fara service garin Kano a ma'aikatar matatan man fetur. Ya
had'a kayansa gaba d'aya ya wuce Kano ya sauka gidan Yaya Ismail, ya samu tarba mai kyau
da kulawa wajen Anty Ameena, ya fara zuwa aiki sai yamma yake dawowa. Kasantuwar shi
mutum ne daya saba rayuwan *kad'aici* tun tasowarsa, sam bai jin dad'in zama a gidan, tuni ya
sanya a fara masa cigiyar gida a wani area, aiko aka yi sa'a ya samu gida plat shi kad'ai mai
kyau, ya kira mahaifinsa ya sanar da shi amma fir yak'i saboda bavzai raba musu zumunci ba,
sai dai dole ya cigaba da zama a gidan Yaya Ismail d'in tunda yana gamawa gida zai dawo, bai
so haka ba ya kira mahaifiyarsa Anty Jidda ya sanar mata ita ma bata so haka ba amma da ya
dinga mata magayi ta amince zata shawo kan Abban nasa.
Shuru shuru sunyi banza da shi akan maganar, aiko ya bugo sammako sai Kaduna part din
Umma ya dira ya kai kukansa wurinta kasantuwar Umma mai son jikokinta ne aiko ta amince,
nan da nan ta kira Aliyu ta shaida masa a yiwa Sadiq abin da yake so, dole ba musu ya yarda
ya tura masa kud'i masu yawa ta account dinsa. Kafin ya tafi sai da ya kwana d'aya ya gana da
Anty Zainab da little Al'amin.
Washe gari da sassafe ya wuce Kano cike da farin ciki, ko da ya isa gidan daya kama haya ya
fara zuwa ya sanya aka yi masa fenti da gyare gyare sai yamma lis ya isa gidan Yaya Ismail a
gajiye, Anty Ameena ta tarbeshi da abinci kala-kala, ya sanar mata da zai koma wani gida, ta
nuna masa ai Umma ta kirasu ta sanar musu, Ta cigaba da cewa.
"Haba Sadiq kamar munyi maka laifi, meyasa ka zab'i ka zauna kai kad'ai, ga 'yan uwanka
Khadija da Kamal, kuma kasan Khadija ba zata ji dad'i ba yadda kuka saba"
_Da yake ta kara haihuwa yaro namiji aka sanya masa Kamal shekarunsa biyu kenan._
"Anty karki damu insha Allah zan rik'a zuwa akai-akai, ni baku min komai ba, tun farkon tashina
da rayuwar *kad'aici* na taso tun daga jss har zuwa digree d'ina, dan haka ba komai Allah"
Nan dai suka cigaba da tattaunawa.
Bayan kwana biyu ya tattara inasa inasa ya koma sharad'a da zama, ba yanda su Yaya Ismail
suka yi sai hakuri.
Koma wansa sharad'a yaji dad'in area saboda unguwar ba hayaniya ba cikowar mutane,
kwanan sa biyu da komawa ya yi arba da lamarin Husna, wata rana yana zaune a harabar
gidan yana shan iskar hantsi, yana danna wayarsa da alama chart yake yi, ihun kuka ya soma ji
gabansa ne ya fad'i, ya toshe kunnuwansa saboda kukan ya yi yawa ya tashi ya leka waje ko a
can kukan yake zuwa gunsa, ko da ya leka ba kowa, ya dawo ya zauna naya sauraren kukan
da haka ne har ya shaida mak'otansa ne kukan yake zuwa gunsa, ya yi tsaki.
"Wannan wani irin kuka ne sai kace ana yanka shi"
Duk sai yaji zaman gurin ya gundureshi, tashi ya yi ya wuce cikin d'akinsa cike da k'unan rai.
A b'angaren Momy kuwa, Husna ta kwana da zazzab'i wanda hakan ya haifar mata yin fitsarin
kwance, da yake Dady baya nan ya yi wani tafiya shiyasa ta samu damar dukanta, lokacin data
tsandara ihu ashe ruwan sanyi ta kwara mata a jiki, sannan tabi ta da duka da wayar wuta, sai
da ta gaji dan kanta kana ta rabu da ita, jikinta na rawa da bakinta abin tausayi, kukan ma sai
hawaye take yi da fidda nishi mai k'arfi, d'aki ta korata ta shiga sannan ta sanya mai aikinta ta
wanke kayan fitsarin. Baba