Showing 21001 words to 24000 words out of 81944 words
abinci na taron suna"
Daga Anty Jidda har Anty Binta sunyi matuk'ar mamaki, nan take suka ji suna son Khalil. Cikin
farin ciki da annashuwa suka kama haryar Kaduna, Zainab har kuka Sai da ta yi saboda bata
son ta yi nesa da Khalil, haka shima sai da ya fidda kwalla saboda damuwar rabuwa da
matarsa. Cikin farin ciki suka isa Kaduna, nan da nan dangi suka cika gida anzo ganin Zainab
da 'yarta, yadda suka ganta cikin kyawun kamala sai duk suka mai da gulmarsu. Umma ba
k'aramin farin ciki ta yi ba yadda su Anty Jidda suka bata labarin Khalil.
Ba su k'ara cinkewa da lamarin ba sai ranar suna da su Yaya Ismail suka tambaye ta sunan
yarinya, sai ta ce musu sunan Umma ce *Asma'u*. Abin ya basu mamaki amma sai suka basar,
tunda duk cikinsu ba wanda ya yiwa Umma karan sanya sunanta. Umma ko a ranar dariya da
murna take yi kamar gonar auduga. Anyi suna an watse kowa cike da mamakin yaada aka
kashe kud'i a wajen sunan, anyi taro kamar dama anyi murna da bikin nata.
******* *******
*Bayan sati biyu*
Khalil shi da Nuhu suka shirya zuwa Kaduna Dan ganin Husna, cike da fargaba da tunanin
yanda za a karb'esu suke har suka isa gidan. Suka yi parking a waje, sun gaisa da mai gadi
suka shaida masa kansu, ya shiga ciki ya sanar dasu Umma, nan take Umma ta kira Baffa a
waya ta shaida masa zuwan su Khalil d'in, ya yi mata umarnin da Zainab ta fita waje can su
gaisa yaga 'yarsa amma karsu kuskura su shiga masa cikin gida. Cikin rashin jin dad'i Umma ta
sanar da Zainab abin da Baffanta ya ce, cikin damuwa ta mik'e ta fita can kofar gidan rik'e da
Husna a hannunta, suka gaisa cikin nutsuwa kana Zainab ta ba su hakuri bisa rashin shigar
dasu cikin gidan, ta shaida musu umarni ne daga Baffa. Basu wani damuba saboda dana sunyi
tunanin hakan, farin ciki su ma sun samu ganinta. Nan suka karb'i Husna suka koma cikin mota
suka zauna Zainab na tsaye daga gefen mota suna hira sosai, suna cikin haka ne Baffa ya
dawo da sauri su Khalil suka fito suka je wurin motar Baffa sun risina suna gaishe shi ko kallon
inda suke bai yi ba balle yasan suna gurin, mai gadi ya bud'e masa k'ofa ya shiga cikin gidan da
sauri ya bud'e su da hayak'in mota, jiki ba k'arfi suka tashi suka koma cikin mota Khalil ya ciro
kud'i masu dan kauri ya bawa Zainab kana suka yiwa nuna sallama suka wuce. Zainab hawaye
taji yana saukar mata a kuncinta ta share tare da girgiza kai ta shiga cikin gida.
Baffa ta samu a cikin falon gidan yana kai kawo, Umma na zaune kan kujera ta zabga tagumi,
yadda ta gansu sai jikinta ya yi sanyi. Dago ido Baffa ya yi rai bace cikin masifa ya ce.
"Mai ya kawo wannan 'yan iskan gidana? bana gargad'e ki akan kar naga k'afarsu a gidan nan
ba, to bari kiji yadda na tsanesu haka na tsani mutuwa ta, dan haka ai kin isa da kanki, maza ki
had'a kayanki ki koma inda kika fito tunda munyi miki gatan da ya kamata muyi miki kuma kin
gama wanka karashe ne dama"
Kuka ta fara yi tana ba shi hakuri amma fir yak'i, Umma na zaune ta kasa cewa komai saboda
ita ya fara zazzagawa masifar dan ta ba shi hakuri dole yasa ta k'i cewa komai. Tsawa ya daka
mata mai k'arfi wanda sai da hanjin cikinta ya kad'a, hatta Husna dake barci sai da ta farko da
gigitaccen kuka, jikin ta na rawa ta shiga d'akinta. Waya ta d'auka ta shiga kiran Khalil, bugu
d'aya ya d'auka cikin kuka sosai take masa magana, hankalinsa ya yi matuk'ar tashi ya fara
tambayar ta ko lafiya? Cikin kukan ta gaya masa abin da take ciki, katse wayar ya yi ya juya
cikin Kunar zuciya ya cewa Nuhu daya juya kan motar zuwa gidan su Zainab, cike da damuwa
Nuhu ya juya wanda a lokacin sun kusa fita cikin garin Kaduna, Khalil ya gaya masa halin da
ake ciki, haka suka koma jugum jugum kamar anyi musu mutuwa.
Ko da suka isa sun sameta a waje ta fito da kayanta duka, Husna tana bayanta, Anty Jidda ce a
gefen ta tana bata hakuri da maganganu masu dad'i, sun gaida da Anty Jidda kana suka sanya
kayan a mota, Zainab ta shiga gida ta yi sallama da Umma. Umma ta yi mata nasiha da Addu'a
da kuma shawarwari a kan yadda zata kula da kanta da 'yarta, da kuka suka rabu sannan ta fito
ta shiga mota sai Zaria.
Haka rayuwa ya cigaba da guda na da dad'i ba dad'i har tsawon wani lokaci...
******
Husna na da shekara d'aya wanda a lokacin tana tafiya har Zainab ta yaye ta saboda karatu,
Khalil ya samo mata wata tsohuwa tana taya ta kula da Husba yana biyanta, lokacin shi kuma
ya kammala karatunsa an turashi service a garin Gombe, ba yadda ya so ba dole ya tafi ya
barsu, Zainab ta masha masa zata koma cikin makaranta saboda karatunsu ya yi zafi dan tana
matakin Karshe, haka ya barta ta koma tare da duk kayan da take buk'ata ba yadda yaso ba,
sai ya rufe gidan nasu.
*****
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah Khalil ya kammala service d'insa wanda a dai-dai wannan
lokacin Zainab sun kammala exam na k'arshe har sun gama project da komai, jiran sakamako
suke tare da shirin zuwa service. Khalil ya koma Kano ya gyara gidansa na gado wanda
iyayensa suka bar masa da niyyar zai sanya Zainab a ciki su cigaba da rayuwa. Kwatsam sai
ga Yaya Aliyu da Anty Binta da kuma Anty Jidda sun zo cikin makarantar da babbar mota na
kwashe kaya, dama suna waya da ita sun san ta gama karatun gaba d'aya, Baffa ne ya aiko su
dasu tafi da ita. Zainab ta yi farin ciki sosai da ganinsu amma da taji sakon Baffa sai ta fara kuka
ita sam ba zata bisu ba, su barta da mijinta tunda ai Baffa da kansa ne ya koreta.
Nan su Anty Jidda suka shiga lallashinta da yake Yaya Aliyu yana jiransu a waje bai san wainar
da suke toyawa ba, da kyar suka shawo kanta ta yarda amma da sharad'in sai mijinta ya yarda.
Nan suka amince da batunta ko a zuciyarsu sun san Khalil ba zai ki ta tafi gida ba, tana kiransa
bugu d'aya ya d'auka ta shaida masa abin da ke faruwa, cikin damuwa ya amince ba yadda zai
yi dan yana kyautata zaton da wuya iyayenta basu raba musu auren ba, cikin rashin jin dad'i
dukansu suka yi sallama. Nan ta shaida musu ya amince, ba tare da bata lokaci ba suka
kwashe mata kayanta duka sannan suka kama hanyan Kaduna.
A gida Baffa yasa an gyara mata d'akinta, ko da suka isa a nan suka dire mata kayanta, taga
tarba mai kyau fiye da zuwanta lokacin data haihu, kowa ya sakin mata fuska a nata haba-haba
da ita, hatta Husna kowa yana sonta saboda akwaita da surutu da kuma wayau dan lokacin
tana da shekara biyu da watanni.
Bayan wata biyu da zuwanta gida ta fara service d'inta a Kaduna wanda da taimakon su Yaya
Ismail ne ta samu a nan saboda basu son ta yi nesa da gida. Hakan ya sanya ta farin ciki, sai
dai inta tuna da mijinta tana kewarsa cike da burin son ganinsa, sauk'in ta a kullun suna waya,
wanda a lokacin ya samu aiki a wani banki a nan cikin Kano yana ta gudanar da aikinsa cikin
lumana da kewar matarsa.
******
Bayan shekara d'aya Zainab da Khalil basu sanya juna a ido ba yana son zuwa amma yana
shakkar abin da 'yan uwanta za suyi masa, sai dai duk k'arshen wata yana turo mata kud'i ta
account tare da aika mata surutu dana Husna.
Husna ta kara wayo da magana sosai wanda a lokacin Zainab ta fara yiwa Khalil maganar a
sanya ta a makaranta, sai dai ya ce ta kara hakuri ta bari sai ya zo tukunna sai suyi maganar.
A wata ranar Azabar Khalil ya kira Zainab ya shaida mata gashi nan zuwa, farin cikin a gunta
baya misaltuwa a wannan rana, ta shiga kicin ta soma girke-girke na tarbansa mai aikinsu tana
taya ta, Anty Jidda harda mata tsiya, dan tun dawowarta ba wanda ya koma damuwa da zancen
mijinta hakan ne yasa ta saki jiki take ganin duk sun huce akan fushin da suka d'auka a kansu,
dan duk suna d'aukar Husna harma su fita da ita don suyi mata siyayya, suna nuna mata
kulawa da soyayya.
Khalil ya kira Nuhu danya rakashi zuwa kaduna amma ya shaida masa baya gari yana Bauchi,
da yake can ya koma ya samu aiki a wani company. Khalil bai ji dadi ba haka dai ya tunkari
Kaduna shi kad'ai cike da fargaba da damuwa.
Ko da ya isa, Zainab ta fito suka gaisa cike da farin cikin ganin junansu tare da tsantsan kauna
mai cike da kewa, tace ya jirata a waje zata dawo, Khalil dai cike yake da fargaba a ganinsa kila
ma yau Baffa ya hana ta shiga da shi cikin gidan. Bayan mintuna sai gata rik'e da Husna a
hannunta ta mata kwalliya ta sanya mata kaya 'yan kanti riga da dogon wando, ga kitso da aka
yi mata wanda yasha bit da yake Husnah akwai suma, da sauri ya amsheta cike da farin ciki
wanda har hak'oransa sai da suka bayyana dan murna, ya shiga yi mata wasa amma taki sakin
jiki, amma daya bata sweet tuni ta saki jiki yana mata wasa har da kyalkyata dariya.
*Rahma ce*
[10/19, 7:36 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KAÆŠAICI*
© *Rahma Kabir*
*Wattpad:*@rahmakabir
*_Page 17 ~ 18_*
Zainab tana kallonsu cike da murna tana taya su dariyar, ta ce su shiga ciki ba musu suka shiga
yana biye da ita a baya, wani falo ta kai shi ba komai a ciki sai babban dadduma da aka shinfida
da wasu k'ananan kujeru a chan gefe, sai tv da sauran kayan kallo, da alama dai d'akin saukar
bak'i ne, abinci ne a jere kala-kala a kan daddumar, suka ya zauna suka shiga hirar yaushe
gamo, ta zuba masa abinci a plate ya fara ci tare da santi tana masa dariya, haka ya ci tare da
Husna ita ma Zainab tana taya su ci. Inka gansu sai sun baka sha'awa kasantuwar suna cikin
farin ciki da annashuwa, ga shi ko wannan su cikin ado.
Bayan sun d'auki dogon lokaci a haka kafin nan suka kammala cin abincin duk sun koshi sosai,
suka cigaba da hira na rabin sa'a tare da tsantsar soyayya, dan Husna ta b'ingire ta yi barci, sun
motsa sha'awarsu sosai da tsantsar buk'atar juna, jin kwankwasa kofar falon ne yasa suka
dawo hayyacinsu, da sauri Zainab ta isa k'ofar ta bud'e, abin da Khalil ya iya ji shi ne.
"Kuzo falo Baffa na magana"
Nan take taji gabanta ya fad'i tare da amsawa da to, ta dawo jikinta a sanyaye, ta shaida masa,
shi ma fad'uwa gabansa ya yi amma sai ya boye damuwarsa da cewa su tafi kiran Baffa.
Abin da basu sani ba tun lokacin da Zainab ta shaidawa su Anty Jidda zuwan Khalil, Yaya Aliyu
ya kira 'yan uwansa ya shaida musu, duk suka d'auki damarar zuwa gidan a ranar da Khalil zai
zo, bayan zuwan Khalil ba dad'ewa da shigarsu falo Yaya Ismail yazo shigo kaduna ba tare da
iyalinsa ba, Anty Binta ma tazo duk sun had'u a falo.
Da isarsu Zainab falo suka yi sallama a tare suka shiga, bugun zuciyarsu ne ya k'aru lokacin da
suka ga duk family sun had'u, kallon juna suka yi tare da ajiyar zuciya suka isa cikin felon suka
zauna a k'asa daga gefe, Khalil cikin girmamawa kansa a k'asa ya gaishesu, suka amsa kamar
ba wani abu a ransu, hakan ya yiwa Khalil da Zainab dad'i har suka k'ara gyara zama, Baffa ne
ya yi gyaran murya ya fara magana.
"To abin da ya had'amu a nan shi ne kan batun auren su Zainab, wanda aka d'aura musu shi a
makaranta shekara uku kenan daya wuce, to ba wai ina son mu maimaita maganar bane domin
kowa a nan yasan da faruwar hakan, ga Zainab a gida ta kammala karatunta sannan ga igiyar
aure akan ta, yanzu kai wannan yaro meya makomar auren ku?"
Cikin mutuwar jiki da tsoro mai had'e da damuwa Khalil ya fara magana cikin rawar murya.
"Baffa na zo da niyyar tafiya da su gidana ne da iyaye na suka bar min yana Kano, dan a yanzu
na samu aiki a nan shi ne dalilin zuwa na"
Falon ya yi tsit na wani lokaci daga k'arar fanka sai k'aran bugun zuciyarsu, Baffa ya ce.
"Ka zo d'aukar Husna ne ko me kake nufi?"
Khalil cikin mutuwar jiki ya ce.
"Zainab da Husna na zo d'auka"
Baffa ya yi murmushin takaici yana kallonsa.
"To yaro bari kaji, a yau zan nuna maka iyakarka, Zainab dai jini na ce sannan kuma bada
miyauna kuka yi auren nan ba, dan haka yau nake so kafin kabar gidan nan ka rubuta mata
takardan saki, dan auren da kuka yi na makaranta kuma ya k'are tunda kun gama karatun,
yanzu ina so ta yi rayuwa a kan ikona saboda a gidana take"
Cikin tashin hankali Khalil ya dago kai yana kallon Baffa haka ita ma Zainab, kuka ta soma yi
mara sauti wanda shi kuma Khalil ya shiga magiya da bada hakuri, nan Baffa ya k'ara shaida
musu maganarsa tare da mik'ewa ya bar falon, Yaya Ismail ne da Yaya Aliyu suka d'aura kan
inda Baffa ya tsaya, ta inda suke shiga ba tanan suke fita ba, Anty Binta da Jidda kuwa kamar
ruwa ya cinyesu suna gudun su yi magana su Aliyu su rufesu da masifa. Umma ma bin bayan
Baffa ta yi cike da damuwa tabar falon. Khalil sunkuyar da kai ya yi k'asa hawaye mai zafi yana
fita a idonsa, cin mutunci babu wanda su Yaya Ismail ba su yi masa ba, Zainab tun tana kuka
mara sauti har sai da ya fito fili, Yaya Ismail yavyi kanta kamar zai bigeta, da gudu ta fad'a
d'akinta tana gunjin kuka, takarda da bairo Yaya Aliyu ya mik'a masa da gargad'in in basu rabu
a nan ba to kotu zai raba su, cikin kuka mai k'una Khalil ya amsa ya rubuta mata saki d'aya, ya
mika masa ya amsa tare da fadan.
"Alhamdulillahi! zaka iya tashi ka kama gabanka sha-sha-sha"
Khalil ya d'ago jajayen idonsa ya ce.
"Nagode amma ba zan iya tafiya ba tare da 'yata ba"
Wani dogon tsaki Yaya Ismail yaja tare da cewa.
"Aikin banza dama ai bamu buk'atar ta ka d'auketa Ku tafi mutumin banza"
Yana gama fadin haka ya wuce d'akin Zainab a fusace, ya sameta kwance bisa gado tana kuka,
ko kallonta baiyi ba ya d'auki Husna da take barci ya fito, da sauri Zainab tabi bayansa tana
kuka da k'arfi tare da surutun karsu rabata da 'yarta, yana isa kusa da Khalil ya mik'a masa
Husna ya amsa tare da kukan bak'in ciki, Anty Binta ne ta koma Zainab da take ta tirje-tirje
zuwa amso 'yarta, wani wawan mari Yaya Aliyu ya sauke mata tare da daka mata tsawa, dole
yasa ta shiga nutsuwarta tare da gungunin kuka, Anty Jidda saboda bak'in ciki barin falon ta yi
tana kuka mai cika da tashin hankali, Anty Binta ita ma kuka take yi mara sauti tare da lallashin
Zainab.
Khalil ya ce.
"Nagode sosai da duk kanin abin da kuka yi min, sannan ban zargeku da komai ba face dama
nasan akwai rana irin ta yau da zata faru, dan tabbas laifi nane kuma na d'auka amma Ku sani
k'addara ce"
Ya kai dubansa ga Zainab ya cigaba da cewa.
"Ki daina kuka in sun raba mu a zahiri a bad'ini bamu rabu ba saboda zuciyarmu tana tare, ko
kad'an banji raguwar sonki a raina ba, ki cigaba da hakuri wannan ma wata jarabawa ce, a
yanzu da hankali ya shige ni ba zan iya sanya ki ki bujirewa iyayanki ba sai ma k'ara miki k'arfin
gwiwa da zanyi kan ki yi musu biyayya, na barki har abada, kar kiyi tunanin zaki sake ganina ko
k'afata a cikin gidanku, sai dai ba zan iya cire miki tunanina ba, da zan iya da na goge miki
shafin tunani na a kwakwalwarki yadda zaki yi rayuwar jin dad'i nan gaba, kash amma ba zan
iya hakan ba dan wannan yin Allah ne ban isa na canza shi ba, ki sanya a ranki kin barni har
abada domin dama rabon Husna ce ya had'a aurenmu, kuma Alhamdulillahi mun sameta ta
hanyar halal ba ta hanyar zina ba, na tafi Allah ya hada fuskokinmu a aljanna"
Ya fita rungume da Husna ba tare da ya kuma juyowa ba, Anty Binta ta bi bayansa da kayan
Husna tana hawaye, ya shiga mota tare da ajiye Husna kujerar kusa da shi, ya kwantar da sit
d'in yadda zata ji dad'in barci, dama barci take duk hayaniyar da aka yi bata farka ba, Anty Binta
ta sanya masa kayan a sit d'in baya ta yi masa fatan alkhairi ta shiga gida. Shiganta ke da wuya
Zainab ta yi kukan kura zata fita da gudu saboda taji tashin motar Khalil ya wuce, Anty Binta ta
tare ta, wani ihu ta saki mai k'ara wanda duk gidan sai da suka ji shi, su Yaya Ismail kuwa sun
firgita sosai, sank'arewa ta yi jikin Anty Binta alamar ta suma, cike da