Showing 72001 words to 75000 words out of 81944 words

Chapter 25 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2398

gaskiya suna farin ciki da samun siriki nagari.

Su Sadiq sun shiga mota ya yi sallama da Baba mai gadi ya ba shi dubu uku ya amsa yana
godiya, ya kunna mota suka wuce idonsa na kan gidan da ya bari wanda Yasir ya cigaba da
zama aciki, da yake kud'in hayan bai k'are ba, kamar ya kira shi ya sanar masa da tafiyansu sai
ya basar saboda baya so ya shiga cikin matsalarsa, k'ok'arin had'asu aure da ya yi da Husna
ma ya gode masa kuma a kullun yana masa addu'an fatan alkhairi. Haka suka kama anyar
kaduna.

Sun tafi baifi da rabin sa'a ba sai ga Yasir ya shiga gidan Dady domin ya karya a nan, dama
tunda aka yi auren su Sadiq, Dady ya ce ya rik'a zuwa yana cin abinci a nan, yana shiga suka
gaisa kana Dady ya tura masa kular wainar shinkafa da miyan taushe ya ce.

"Ga mutuminka yau nasa anyi mana"

Da murmushi ya jawo kulan ya shiga zubawa, ya zuba miyan ya soma ci, Dady ya ce.

"af, Yasir ga lipton na manta ko zaka fara sha ya warware maka hanji"

Yasir ya yi dariya ya ce.

"Ai Dady nasha tea d'azu wainar kawai zanci"

Baba Husain ya ce.

"Ai Khalilu rabu da shi tunda ya samu muradinsa ai baya ta tea"

Suk su ka yi dariya, yana gama cinyewa Dady ya ce

"Ashe zuwa Kaduna ya kama su Sadiq yau d'in nan, nasan ya gaya maka dan d'azu ma suka
mana sallama"

Cike da mamaki Yasir yake duban Dady ya ce.

"Wallahi bai gaya min ba, kuma fa nace masa in za shi ya sanar min dan nima ina son zuwa"

Hannu ya zare daga wainar da yake ci ya wanke, da sauri ya mik'e tsaye.

"Dady bari nabi bayansu"

Cike da mamaki Dady ya ce.

"Haba Yasir da sauri haka, ka bari mana wani lokacin sai ka tafi"

Murmushin yak'e ya yiwa Dady.

"Kumin Addu'a kawai Dady, amma dole na tafi yanzun nan"

Dady ya ba shi 10k shima yasha mai, ya amsa ya yi musu godiya da fatan alkhairi ya wuce.
Yana fita ya shiga mota ya bata wuta sai Kd, tun a hanya yake kiran Sadiq amma yaki d'agawa,
parking ya yi ya tura masa text.

_"In ka gama wulak'ancin ka turo min address d'in gidanku na Kaduna din nima ina bisa
hanya"_

A lokacin Sadiq sun kusa shiga Kaduna, duk yana jin shigowar kiran amma yak'i d'auka, yaji
shugowan text shima sai ya share.

******** *** ********

*Kaduna*

Bayan sun isa Sadiq ya yi parking a harabar gidan ya d'auki wayarsa ya duba, text kawai ya
turawa Yasir na address d'in gidan, kana ya waiga wurin Husna ya ce.

"Baby mun k'araso, yanzu ki ja mayafinki ki rufe fuskarki sannan ki natsu da kyau sai nace ki yi
magana sannan za ki yi, kuma ki toshe kunnenki da duk abin da za ki ji, ki yi hakuri komai zai

wuce kin ji"

Hudna ta gyad'a masa kai alamar ta gamsu, sannan ta ja gyalenta kamar yadda ya yi mata
umarni, fitowa suka yi ya kira mai gadi ya shigar musu da kaya cikin babban falon gidan, Sadiq
ya doshi k'ofar falon zuciyansa na dukan uku-uku, dakewa ya yi ya matse ya shiga, Husna na
biye da shi, tana ganin ya shiga ta ja ta tsaya a bakin k'ofa. Sadiq ya tadda su Baffa, Abba Aliyu
mahaifinsa sai Abba Ismail, da alama hira suke yi, da yake weekend ne ko wanne yana gida,
ganin Sadiq ne ya katse musu hiransu suka zuba masa ido harya k'araso cikin falon ya zauna a
k'asan carpet Kansa a sunkuye, duk tunaninsa Husna ta shigo sai ya waiga yaga wayam bata
shigoba, tunani ya fara yi.

'Mai ya hanata shigowa?'

Baffa ne ya katse masa tunaninsa da cewa.

"Babban Mutum yau kaine a gari, na yi tunanin sai mun ciko mota mun zo har garin Kano biko"

Murmushi ne ya kubce masa ya ce.

"Baffa kusha zamanku Ku huta gani tafe da kaina, da fatan na sameku lafiya?"

"To masha Allah, lafiya lau muke"

Daga nan ya gaishe da iyayen nasa, Abba Ismail fuskansa sake ya amsa, amma Abba Aliyu
kuma fuska murtuke ya amsa ba yabo ba fallasa, falon ya d'auki shuru, Abba Aliyu ne ya d'auki
wayarsa ya kira Ammi Jidda ya ce.

"Ki zo ga d'anki ya dawo da kika matsa min dole saina kira shi, to gashi nan ya yi kiba ya samu
natsuwa hankalinsa kwance ya manta damu, amma ke kin kwallafawa ranki damuwa bai san
kina yi ba"

Yana kaiwa nan a maganarsa ya kashe wayan ba tare da ya jira mai zata ce ba, Sadiq ya d'ago
suka had'a ido da mahaifinsa sai ya harare shi ya kauda kai gefe, tunaninsa ya zai mik'e ya je
ya shigo da Husna dan ayi ta ta k'are.

Tab'angaren Husna kuma tana tsaye tana jin tsoron ya zasu amshe ta, hankalinta tashe, tana
sak'a da warwara na mafita, dole ta yanke shawarar shiga dan ba tada wata mafita illa yin
hakan, kanta a sunkuye rufe da mayafi ta k'usa kai ciki da sallama, shiganta ya yi dai-dai da
shigowar Ammi Jidda, kallone ya koma kan Husna kowa yana tunani wace bak'uwa suka yi ne
da safiyan nan, wurin da Sadiq ya zauna can ta nufa ta zauna gefen damansa, mamaki ne ya
cika fuskokin su Baffa, sun kasa furta komai sai kallonsu da suke yi, kafin wani ya jefo tambaya,
Sadiq ya risinan da kai k'asa ya ce a hankali Husna ki gaishe su, kanta na sunkuye rufe da
mayafi bata d'agoba ta gaidasu, babu wanda ya iya amsawa saima kalon-kallo da suka shiga yi

da juna, Ammi ce data shigo ta ce cikin d'aga murya.

"Sadiq wacece wannan?"

Dam dam yaji zuciyar shi ya buga, haka ma ta b'angaren Husna, sosa kai ya fara yi cikin
inda-inda ya ce.

"Matata ce"

A zabure Abba Ismail da Abba Aliyu suka mik'e tsaye, Baffa ko mai da bayansa ya yi ya jingina
da bayan Cushing da yake zaune a kai, Ammi Jidda kuwa wasu zafafan hawaye ne suka shiga
zarya a kumatunta. Da sauri ta fita ta isa sashin Umma cikin kuka ta ce mata ta isa babban falo,
Umma na tambayanta me ya faru bata iya bata amsa ba ta wuce sashin Mami Ameena nan ma
abin da ta cewa Umma shiga gaya mata, haka ta gaya wa Anty Zainab duk suka tawo falon a
sukwane. Haka duk suka tsaya cirko-cirko kamar yadda suka ga su Abba Aliyu a tsaye, mamaki
ne a fuskokinsu wanda kallo ya koma gurinsu Sadiq, Baffa ne ya yi k'arfin hali ya ce musu duk
su zauna, ba musu kowa ya samu wuri ya zauna, harda su Khadija, Baffa ya kai kallonsa ga
Sadiq ya ce.

"Yaushe kuka yi aure? kuma a ina? sannan wasu iyaye ka samu wanda suka fi maka mu?"

Ba k'aramin kad'uwa su Umma suka yi ba kanma Anty Zainab da take da tabo akan haka. Gumi
Sadiq yake yi wanda duk sanyin falon baya jinsa, kansa sunkuye ya ce.

"A Kano aka d'aura, wata d'aya kenan da kusan sati biyu, a can na samu iyaye da suka yi min
wakilci akan auren"

Zabura Abba Aliyu ya yi yana huci.

"Kai har kana da bakin bayani ko sha-sha-sha, wallahi tun kafin in ta shi in yi k'asa-k'asa daku
ku fice a gidan nan, na tsameka daga zura'armu, bamu ba kai kaje can wurin iyayen daka sake"

Hawaye mai zafi ya fito ma Sadiq ya ce.

"Abba kuyi hak'uri ku yafe min, wallahi akwai dalilin da yasa na yi wannan auren, kaddara ce"

Ammi Jidda ta ce cikin muryan kuka.

"Rufe mana baki wallahi, Sadiq ka bani mamaki, maza tashi ku koma in da kuka fito"

Ai Husna kuka ta b'arke da shi, ta matsa kusa da Sadiq ta rik'e hannunsa tana cewa.

"Uncle tashi mu tafi kafin su dukemu"

Zan iya cewa Sadiq ne kad'ai ya iya sanin me take cewa, Abba Ismail ya ce.

"Ko baka ji abin da aka ce maka bane? ta shi kabar gidan nan maza, tun kan raina ya gama
b'aci"

Mami Amina ta ce.

"Dan Allah ku barsu mu ji abin da yasa hakan ya faru, bai kamata a yanke hukunci cikin fushi ba
kuma..."

Wani mugun kallo ne da Abba Ismail ya wurga mata wanda yasa dole ta yi shuru ba tare da ta
gama fad'an abin da ke bakinta ba, Umma kuwa ta kasa magana banda rafka tagumi da ta yi,
Anty Zainab kuwa kuka take yi sosai tana kaicon abin da ta aikata, da bak'in cikin k'addarar da
bai tsaya kanta ita kad'ai ba.
'Wannan wace irin k'addara ce?'

Khadija ko lafewa ta yi jikin Maminta tana kukan bak'in ciki da abin da masoyinta ya yi, Sadiq ya
kama hannun Husna ya mik'e bai iya furta komai ba face hawaye dake gudana daga idonsa,
har sun isa bakin k'ofar fita, Anty Zainab ta ruga da gudu ta kama hannun Sadiq cikin kuka ta ce

"Ba in da zasu dole ne su zauna a gidan nan, sannan ma bakwa tunanin abin da ya faru ne a
baya? in har aka kori Sadiq to ba ayi adalci ba, tunda nima ba a koreni ba, kuma dole ne a
gyara wannan kuskuren gudun kar gaba ya kuma faruwa. Ai Allah ya nuna mana ishara ce akan
irin hukuncin da kuka zartar a kaina a baya, kuka rabani da masoyina akan k'addarar da
ubangiji ya rubuta akanmu, dan haka dole ne yanzu mu amsheta mu yi imani da hakan, ko Allah
zaisa wannan ya zama k'addara ta karshe a garemu, ko kun manta Allah ya ce muyi imani da
k'addara mai kyau ko mara kyau"

Ta k'arasa maganar da kuka, jikinsu ne duk ya yi sanyi hak'ik'a maganar Anty Zainab ya yi tasiri
a zuciyoyinsu, Baffa ne ya nisa ya ce.

"Sadiq Ku dawo ku zauna"

Ba musu suka dawo suka zauna, Anty Zainab ma ta koma ta zauna duk suka yi shuru.

Yasir ya shigo Kaduna yana tabin address d'in da Sadiq ya tura masa, harya zo dai-dai gate d'in
gidan, suka gaisa da mai gadi ya ce

"Malam, dan Allah ina ne gidan Alhaji Ahmad Mai Kanti?"

mai gadin ya yi murmushi ya ce.

"Ai ka zo gidan, dan nan ne"

Cikin sauri ya bud'e mota ya fito.

"Sadiq na ciki?"

"Eh, basu jima da zuwa ba, yana ciki"

Key motar Yasir ya bama mai gadi.

"Ka iya mota?"

"Eh"

"Ok, shigo min da ita ciki"

Bai jira mai zai ce ba ya shi. A falo Baffa ne ya ce.

"Sadiq ka gaya mana ya wannan auren ya kasance? sannan meye dalilin ka na yinsa ba tare da
sanin muba?"

Yasir ya shiga falon a dai-dai Baffa yana wa Sadiq wannan tambayar, caraf Yasir ya amsa da
cewa.

"Nine na had'a auren, Sadiq bai da laifi, nine nan mai laifi"

Ya nuna kansa, ai kallo sai ya koma wurin Yasir, mamaki ya rufe su Baffa, gashi dai bak'on
fuska ne basu waye sa ba.

*Cakwakiyar tana nan*
[11/4, 7:20 PM] Rahma Kabir🌺: *_Page 63 ~ 64_*


Baffa ya ce.

"Bawan Allah k'araso ciki ka mana bayani dan bamu wayeka ba"

Cikin sauri Yasir ya k'arasa kusa da Sadiq gefen damansa ya zauna, yabi 'yan falon da kallo
wanda suma kallonsa suke yi, daya kai kallonsa ga Anty Zainab sai ya kura mata ido cike da
mamaki a fuskarsa, kamar Husna ya hango a fuskarta, abin da ya yi banbanci Husna ta fita
haske sannan tafi yarinta sosai amma da ka gansu kasan akwai had'uwar jini a tsakaninsu.
Baffa ne ya katse masa tunaninsa da cewa.

"Kai yaro muna sauraron ka"

Nan Yasir ya gabatar musu da kansa da kuma yadda suka had'u da Sadiq har suka k'ulla abota,
kana ya yi musu bayanin yadda aka yi Sadiq ya auri Husna da yadda ya had'a auren, cike da
mamaki mutanan falon suke kallon Yasir, bayan ya gama ya cigaba da cewa.

"Sauran bayani yana gun Sadiq"

Sadiq ya d'ago suka kalli juna kana.

"Ai ka gama gaya musu abin da ya faru"

Yasir ya yi murmushi.

"Sadiq ya zama dole yau ka sanar da iyayenka yadda ka had'u da Husna, domin b'oye-b'oye bai
da wani amfani"

Anty Zainab na jin an ambaci Husna taji gabanta ya yi mummunar fad'uwa, wanda ita kad'ai ta
iya tunawa da 'yarta Husna a cikin wannan yanayin. Abba Ismail ya nisa ya ce.

"Kai Sadiq maganar b'oye-b'oye ya k'are ka gaya mana asalin yadda ka had'u da wannan
yarinya, hakan shi ne zai sa mu gamsu da duk kan bayanin da abokinka ya yi mana yanzu"

Sadiq ya risinar da kai.

"To Abba"

Ya ce tare da gyara zama ya cigaba da cewa.

"Na had'u da Husna tun tana k'arama wato tana da shakara bakwai zuwa takwas a lokacin"

Daga nan ya cigaba da basu labarinta wanda ya sani da wanda ya samu labari wajen Baba mai
gadi, da duk irin wahalar da ta yi na rayuwar k'unci da *kad'aici*, da azabar da Momy ta gana
mata har haukan data d'aura mata, da asirin da ta yi ta raba ta da Dadynta harya zuwa tonuwar
asirinta, da karyewar asirin da ta yiwa Dady, har zuwa had'asu aure da Dady ya yi da komai ya
zayyana musu. Ai tambayoyi ne cike a zuk'atan su Baffa bama ga Anty Zainab wanda kuka ya
wanke mata fuska, su Ammi Jidda, Mami Amina Umma dama Khadija duk hawaye suke yi da
tausayin irin wahalar da Husna ta sha, Abba Ismail da Abba Aliyu duk jikinsu ya yi sanyi, falon
ya yi shuru na mintuna bayan Sadiq ya yi shuru, shashshekar kukan Husna ce kawai ke tashi a
falon, sun zauna jugum-jugum kamar wanda aka yi musu mutuwa, Baffa ne ya yi gyaran murya
cikin sanyin jiki ya ce.

"Sadiq meyasa tun farko baka yi mana bayanin halin da yarinya nan take ciki ba? Ai ina ganin
da mun ji duk wannan bayanin ba mai hanaka aurenta, yanzu ma shin shi mahaifinta ya san
cewa ba mune muka nima maka aurenta ba mu da muke ainahin iyayenka?"

Sadiq ya ce.

"Gaskiya bai sani ba saboda duk wannan aikin Yasir ne, Kawunsa ya nima auren kamar yadda
ya muku bayani"

"To yanzu ya za'ayi mahaifinta yasan da mune iyayenka, sannan mu ba shi hak'uri mu nuna
masa kuskurenmu tunda tun farko mune muka jawo faruwan haka, saboda k'in amincewar mu"

"In mun koma zanje na yi masa bayanin komai, in ya so sai na kiraku a waya yaji daga bakinku"

"To shi kenan, ya sunan mahaifin nata inya so sai ka bani numbern sa, in kun koma sai na kira
shi, domin kuwa mune ya kamata mu fara nimansa"

"Sunansa Alh. Khalil"

Ai kan ya rufe baki Anty Zainab ta zabura ta mik'e tsaye tana nuna Husna da yatsa, su Umma
shock suka ji wanda hatta Baffa sai da yaji gabansa ya fad'i, Abba Ismail da Abba Aliyu
mutuwae zaune suka yi suna tunanin faruwar wani abu, kallo ne ya koma wanjen Anty Zainab
ta isa wurin Husna da sauri ta fincike gyalen da ta rufa da shi, tuni tsoro ya ziyarci Husna ta
tsandara ihu ta k'ank'ame Sadiq, tunaninta ko dukanta zasu yi, ai mutuwar tsaye Zainab ta yi
tana bin Husna da kallo tare da fitan zafafan hawaye ta waiga tana kallonsu Anty Jidda ta ce da
k'arfi.

"Anty Jidda wallahi Husnata ce,wallahi 'yata ce, ita ce Allah"

Sadiq ya zaro ido kamar zasu fad'o waje ya ce cikin tsoro.

"Anty ban gane ba wai meke faruwa ne?"

Yasir ya yi murmushi ya ce.

"Sadiq ka natsu yanzu zamu gane komai"

Anty Jidda da sauri ta taho wurin Husna ta fincikota jikin Sadiq da k'arfi, ta daka mata tsawa
saboda taki tsayawa, cikin tsoro Husna ta tsaya cak tana kallon mutanan falon idonta wanke da
hawaye, Khadija ta mik'e da sauri ta ce.

"Husna dama ke ce? Mami wallahi ita ce k'awata da kullun nake baki labarinta, wallahi Husna
ce"

Itama Husna bin Khadija ta yi da kallon mamaki, ai tuni salati da salallami ya cika falon kowa na
fad'an albarkacin bakinsa, Baffa ko jikinsa mutuwa ya yi yana kallon wani ikon Allah.

"Ameena a shekarun baya na taba gaya miki wata mata ta kawo min wata yarinya asibiti, dan
na bata maganin da zai haukatata, tabbas wannan yarinyar ita ce, innalillahi wa inna ilaihir
raji'un! Kaiconmu! Rashin sani, ashe d'iyata ce, Allah ya kiyaye ban bata ba"

Cewar Abba Isma'il ya dafe kansa cike da jimamai.

"Kwarai Abban Khadija na tuna, wannan shi ne ikon Allah mai yin yadda ya so"

Cewar Mami Ameena, Ammi Jidda ta ce.

"Husna a she dama zamu sake tozali da ke?"

Sai ta rungume ta ta saki kuka, Sadiq ya kuma rud'ewa ya ce.

"Dan Allah ku min bayani, karku sanya na zauce"

Cikin kid'ima yake magana, Abba Aliyu ne ya yi gyaran murya ya ce.

"Ke Jidda samu wuri ku zauna domin a samu fahimta"

Ba musu suka zauna taja hannu Husna, aiko tak'i yarda dole ta koma wurin mijinta Sadiq, ta
d'aura kanta a kafad'arsa tana kuka, ita kanta ta gaza gane komai sai rud'ani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login