Showing 18001 words to 21000 words out of 81944 words
rass sai
kawai taji hawaye na bin kuncinta. Matan dake cikin gidan ne, naji suna ta gud'a suka lek'o
d'akin dasu Zainab suke ciki, tare da ran gad'a gud'a suna sanya albarka, wanda basu san
amaryan ba sai lek'ota suke yi friend d'in ta suna nuna musu ita, suma da suke d'akin suna
gud'a tare da shewar farin ciki.
Bayan komai ya lafa, da misalin k'arfe Hudu, Malam Isah mai hadisi ne da su Khalil suna zaune
gabansa cikin zauren gidan, sannan ya aika aka kira masa Zainab, ta fito sanye da lullubi
akanta, zama ta yi gefen Khalil ta gaida Malam, nan ya sanya musu albarka tare da addu'o'i na
samun zaman lafiya da zuria d'ayyiba, ya mikawa Khalil certificate d'in aurensu, sannan ya ce
"Ga nawa da kace na rike a guna, sannan zuwa bayan Sallan Magariba sai ka zo ka d'auketa,
yanzu ni na gama nawa, Allah ya muku Albarka, zaku iya tafiya"
Nan suka yiwa Malam godiya sannan Khalil ya ajiye masa kud'i a gabansa wanda shima bai
san adadinsu ba ya ce.
"Ga wannan aci goro"
Malam ya yi godiya shima, kana Zainab ta koma cikin gidan, shi kuma suka wuce da abokansu
harda matan ma suka tafi dasu cikin makaranta, Zainab kad'ai suka bari a gidan.
Bayan sun isa makaranta suka yi musu godiya suka sallami kowa. Khalil da Nuhu d'akin Zainab
suka wuce da yake key d'in na hannun sa, kayanta suka kwashe, dama ta gama shirya wanda
zata d'auka da sauran kayan kicin sai kuma kayan sawanta da littafanta, suka sanya a mota
suka bar sauran kayan a ciki suka rufe, sannan suka wuce gidan khalil suka shirya kayan ko
wanne suka sanya shi a mazauninsa, abin mamaki har da fanti ya yiwa d'akunan sai kamshi
suke yi kamar dama sun shiryawa abun, sun kai kusan karfe shida na yamma suna aikin, bayan
sun gama suka share gidan tas kana Khalil ya yi wanka ya sanya farar shadda sai walk'iya yake
yi, suka kama hanyar zuwa gidan Malam Isah mai hadisi.
Sun isa gidan dai-dai ana kiran sallar Magrib, suka gabatar da Sallah a Masallaci, sannan suka
dawo k'ofar gidan, sallama suk ayi sannan suka shiga cikin gidan, Malam ne ya amsa tare da yi
musu iso suka shiga cikin dakin da Zainab take zaune, nasiha ya yi musu sosai akan zaman
aure kana ya sallame su. Akwati naga an fito da shi mai kyau trolley mai guda biyu da kit, a
bayan motarsu aka sanya sannan Zainab ta shiga baya Khalil ya zauna gefen driver, sai Nuhu
ne ya jasu suka wuce.
Koda suka isa gidan suka shiga ciki, Nuhu ya yi musu sallama da alkawarin zai zo da safe.
Khalil ya yi masa godiya bisa ga taimakonsu da ya yi, ita ma Zainab d'in godiya ta yi masa kana
ya wuce.
Khalil da Zainab sun zama mata da miji bisa auren sunnah, sai dai dukansu suna cikin fargaba
da damuwar abin da hakan zai haifar musu a nan gaba. Zainab ta yi kuka sosai har take jin
dama bata aikata haka ba, tunanin iyayenta take yi da yadda zasu d'auki wannan lamari, haka
shima Khalil, sai dai in ya tuna yana tare da ita sai yaji natsuwa. A wannan dare a takure suka
kwana, da tunani kala-kala har barci b'arawo ya sacesu.
****** ******
*Washe gari*
Da misalin karfe tara na safe Nuhu yazo, suka gaisa kana suka yi breakfast, wata jaka na ga ya
bud'e ya ce.
"Ga photocopy din certificate dana yi, yanzu kune nake jira"
Khalil ya kalli Zainab ya ce.
"Sweet Zee ga shi ya kawo, Amma bamu rubuta letter ba"
Ta yi guntun murmushi da bai kai ciki ba ta ce.
"To bari na rubuta nawa
Nuhu ya mika mata farar peper da bairo, ta karba ta fara rubutu kamar haka.
*_ASSALAMU ALAIKUM_*
*_"Baffa da Umma da kuma sauran 'yan uwana ina miko gaisuwa gare ku tare da fatan alkhairi.
Na zama mai babban laifi agareku, ku yafe min hakika nasan ban kyauta muku ba, amma gaba
daya na d'auke shi k'addarata ce. Wannan sako da na yi muku nasan zai girgizaku amma ku
yafemin. A jiya Ranar Juma'a aka d'aura min Aure da Khalil bisa sadaki dubu Hamsin, kuma ya
ba ni tare da kud'in gaisuwa da kayan sa rana dubu Hamsin duka dubu d'ari, sai akwati biyu da
kit ya zuba kaya iya k'arfinsa, sannan ya kama mana haya a nan cikin Zaria. Malam Isah mai
hadisi shi ne ya yi min waliyyi shi kuma na'ibinsa ne ya yiwa Khalil waliyyi._*
Nan ta rubuta musu labarin yanda iyayen Khalil suma suka ki amincewa da k'udurinsu, sannan
ta d'aura da cewa.
*_"Mun yanke wannan hukuncin ne saboda mu gujewa sab'on Allah sannan bazamu iya
guduwa ba, shiyasa muka ni mawa kanmu mafita saboda in bamu aure junan mu ba to tabbas
za a iya rasa d'aya daga cikin mu, Allah shi ne ya had'a wannan soyayya, kuma munyi soyayya
mai tsafta da k'aunar juna cikin Aminci, mun gujewa sab'on Allah ne shiyasa muka yanke
hukuncin muyi aure dan cikar burinmu. Sannan kar kuga laifin Malam Isah mai hadisi akan ya
d'aura mana aure, saboda bamu sanar masa da ainihin labarinmu ba. Tun lokacin da muka
sanar ma juna rashin amin cewarku muka shiga damuwa, daga karshe muka yanke hukuncin
mu yi aure, tun daga wannan lokacin ne Khalil ya bukaci kudi masu tsoka a gun iyayensa, kuma
sun ba shi ne bisa dalilin ya ce zai yi amfani dasu ne wajen hidimar karatunsa, wannan ne yasa
muka isa wurin Malam da tai makon Abokinsa Nuhu shi ya yi mana hanya, muka je a matsayin
Khalil maraya ne ya rasa iyayensa shi ke rik'e da kansa, sai kuma ni a matsayin na musulunta
ne kuma nabar iyayena saboda sun mini barzanar kashe ni. Da wannan bayani muka je gareshi
harya d'aura mana aure dan mu gujewa aikin shaid'an. Dan haka ina mai rok'anku gafara
wallahi So ne yasa muka aikata haka, Ku yafe mana gwiwowinmu a k'asa. Har abada ba zan
daina kuka ba har sai kun yafe min laifin dana muku. Ina son ku iyayena da 'yan uwa na, har
abada ni taku ce. Insha Allah zan dawo gareku nan ba dad'ewa ba, amma sai na tabbatar da
zuciyarku ya yi sanyi bisa ga laifin da muka aikata_*
_Nice 'yarku_
*Zainab Ahmad Tanko Mai Kanti*
Khalil ne ya karb'a ya karanta sai da kwalla ya zubo masa ya girgiza kai, kana ya mik'awa Nuhu
ya amsa shima ya karanta damuwa ne a fuskarsa, haka ya nad'e letter tare da certificate d'in ya
sanya a wata jaka. Shi ma Khalil ya amsa ya rubuta nashi letter kamar yanda Zainab ta rubuta,
sai dai shi ya bambanta wasu wuraren, yana gamawa ya ninke ta ya bama Nuhu.
******
Sako ya isa Kaduna, mai gadi ya shiga falon Umma da sallama ya samu Anty Jidda tana
yankan alayyaho, Umma kuma tana zaune suna hira, sun amsa masa sallamarsa ya gaida su,
sannan ya karaso kusa da Anty Jidda ya mik'a mata sakon Zainab, ta amsa cike da mamaki, sai
ya fita, kiciniyar bud'e jakan take yi sai ga Yaya Aliyu ya shigo falon...
*Rahma ce*
[10/19, 9:53 AM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KAÆŠAICI*
© *Rahma Kabir*
*Wattpad:*@rahmakabir
*_Page 15 ~ 16_*
Ta ciro abin da ke cikin jakan sai taga paper guda d'aya da certificate, a lokacin yaya Aliyu yana
magana da Umma, salati a tsorace suka ji Anty Jidda ta saki, jikinta na rawa ta mik'e tana fad'in.
"Baban Sadiq kalla ka gani sak'o ne Zainab ta aiko da shi"
Cikin hanzari ya karb'a, abin da ya gani shima ya girgiza shi, zufa ne yaji yana keto masa,
bugun zuciyarsa ya k'aru.
"Anya wannan sakon Zainab ta yi shi kuwa? muga dai dayan paper"
Ta mik'a masa ya amsa ya fara karanta wasik'ar da k'arfi su Umma suna saurare, Umma ta
kagara akai karshen labarin dan ta tambayesu akan shin anya Zainab ce kuwa? kan ya gama
karantawa zufa ya lullub'eshi, Anty Jidda kuwa kuka ta fara yi, Umma kuma saboda tsabar
bak'in ciki ta kasa magana sai kukan zuci. Duk suka zauna jugum-jugum kamar anyi musu
mutuwa, suna cikin wannan halin ne sai ga Baffa ya shigo, ganin su da ya yi cikin wannan
yanayi sai ya shiga tambayarsu.
"Lafiya na ganku a haka?"
"Lafiya lau Baffa zauna tukunna"
Cewar yaya Aliyu, Baffa ya saki guri ya zauna, nan take Yaya Aliyu ya shiga karanta masa
sak'on Zainab, bayan ya gama ya nuna masa certificate d'in auren nata, Baffa yaji kansa ya
sara zufa na keto masa, ya shiga jero salati yana ta'ajibin lamarin, sai a lokacin Umma ta samu
halin yin kuka mara sauti kamar anyi mutuwa, basu tab'a tsammanin haka daga Zainab ba.
Yaya Aliyu ya kira Ismail ya fara sanar masa abin da ke faruwa, shima salatin ya yi ya ce gasu
nan zuwa sai ya kwashe wayar. Ya kuma kiran Al'amin ya shai da masa, kana ya kira Binta ita
ma ya fada mata, dukansu sunyi mamakin lamarin mai cike da tsantsar damuwa.
********
*A KANO*
Nuhu da kansa yaje ya kai sakon Khalil, ya bama wani yaro ya kai cikin gidan su Khalil d'in, kan
yaro ya fito ya shiga mota ya juyo zuwa Zaria.
Baba Husain yana zaune a baranda shi da Inna suna hira, da yake ya tashi da ciwon kai
shiyasa bai samu zuwa kasuwa ba, yaron ya shiga da sallama ya gaishe su kana ya mik'a masa
sak'on da Nuhu ya ba shi.
"Gashi wani mutum ya bani a waje wai Khalil ya ce a kawo maka"
Baba ya amsa.
"Sannu yaro mu je daga ko waye ya aiko"
Ko da suka fita ba alamar mutum a wajen, sai zanen tayar mota wanda ya nuna mota ta tsaya a
gun, Baba ya sallami yaron, ya shiga gida cike da mamaki yana labartawa Inna, ya zauna ya
bude jakar ya ciro abin da ke ciki ya bud'e wasikar ya shiga karantawa a fili Inna tana
saurarensa, mamaki ne ya bayyana a fuskansu har ya gama karantawa, salati suka shiga yi
Inna harda tafa hannu tana rik'e hab'a, murmushi ya yi ya girgiza kai.
"Ka haifi da baka haifi halinka ba yaran zamani kenan, ban tab'a tunanin haka daga gareka ba
Khalil"
"Ai Malam ya ga dan bamu muka haife shi ba shiyasa"
"A'a karki ce haka, yau ko da Hassan na raye da Halima tabbas haka zai yi, bana zargin dan
bamu muka haife shi ba, kawai dai son zuciya ne da kuma kuruciya"
Inna ta yi murmushin takaici.
"Shiyasa ya karb'i kud'i da yawa a she ga abin da zai aikata, ni dama na yi mamakin kud'in da
ya tambayeka, na ce wani irin karatu ne haka mai cin kud'i, a she da walakin goro a miya"
Nan dai suka cigaba da tattaunawa cike da alhini, Baba hassan ya mik'e ya ce zai je ya sanar
da Mahaifiyarsu halin da ake ciki.
*******
*KADUNA*
Bayan sallah la'asar falon gidan cike yake da wannan dangi, na nesa duk sun zo, Baffa ne ya
umarci Yaya Aliyu daya karanto sak'on da Zainab ta yi, cikin nutsuwa ya fara karantowa, tun
kan ya gama falon ya hargitse da salati, Anty Binta sai kuka ita da Anty Ameena, ya nuna musu
certificate d'in aure wanda hakan yasa dole suka gasgata lamarin. Shuru ne ya ratsa falon na
tsawon minti biyar sai karar fanka ke tashi. Yaya Al'amin ne ya barke da kuka yana fad'an.
"Haba Zainab da nasan zaki iya aikata haka dana hakura kin aure shi, yanzu kin kyautata mana
kenan kin rabu da danginki kin kama namiji da baki san asalinsa ba..."
Kukan ne ya sirk'e shi ya kasa karasa maganar, yaya Ismail kuwa ya fara masifa kamar zai ari
baki ya tsine maya, nan dai Abba Iro ya ce ya yi shuru ba lokacin fad'a bane tunda ta riga ta
aikata, ya cigaba da cewa.
"Yanzu abin da za ayi kai Aliyu da Ismail da kai Al'amin Ku tashi kuje Zaria Ku bincika cikin
makarantar, tunda an kira wayarta a kashe sai...."
Bai k'arasa maganar ba Baffa ya katse shi da cewa.
"Malam Sani ai ko sunje ba zasu gansu ba a yanzu dan sun gama jarabawa, ina ganin muyi
hakuri mu amshi k'addarar daya samemu, sai mu d'aura da yi mata Addu'a, Allah ya shirye su
gaba d'aya, yasa su gane sun tafka kuskure"
"Hakane, ka kawo shawara mai kyau zamu sanya ta a Addu'a Allah ya mai do da hankalinta
gida, a ganina kamar da asiri a cikin lamarin kamar yaron nan bai barta haka ba"
Cewar Abba Iro.
"Yaya Iro son zuciya ce kawai, amma bana tsammanin da asiri, ai jiki magayi"
Cewar Umma. Yaya Ismail ne ya gyaran murya ya ce.
"Baffa ni kam ba zan barshi ba wallahi sai ya san ya aikata mana haka"
"Ismail meye na d'aukar zafi? ai kar kaga laifin yaron, ance nake shi ke bada kai, dan haka laifin
na gun 'yar uwarka, daga yau na rufe wannan maganar kowa ya cigaba da al'amuransa"
Nan dai suka cigaba da tattaunawa, daga k'arshe suka rufe taron da Addu'a.
Tun daga wannan rana suka bar zancen Zainab kowa ya cigaba da harkansa, Anty Jidda da
Umma suke wayan kiranta a waya basa damu, sunyi har sun gaji sun hakura sai lokaci lokaci
suke nimanta ko zasu dace. Wannan zuri'a Haka suke kwana su tashi cikin wannan bak'in ciki.
Al'amin har rashin lafiya ya yi haka dai ya gama jinya ya warke amma sonta yana nan a
zuciyarsa.
********
Su Zainab sun angwance cikin damuwa da fargaba, Khalil mutum ne mai barkwanci da hakane
ya samu har Zainab ta saki jiki da shi, sai dai in ta tuna da 'yan uwanta sai ta yi kuka mai isarta
daga karshe ta yi hakuri dan kanta. Rayuwar kad'aici har ya bi jikinsu, duk lokacin da suka yi
hutun makaranta basa iya zuwa gida a nan gidansu suke hutunsu har ya k'are su koma, sai dai
suna waya da 'yan uwansu. Haka suka cigaba da rayuwa da dad'i ba dad'i har tsawon wani
lokaci.
****** ******
*BAYAN SHEKARA D'AYA*
Lokacin Zainab tana da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, tana zaune a d'akinta da yake sunyi
hutun makaranta, wayarta ne ta soma ringing bugu biyu ta d'auka Anty Jidda ce ta kirata, ta
sanar mata da haihuwar Anty Ameena ta samu d'iya mace ranar labaraba, hawaye taji yana
gangaro mata, ta fara shasshekar kuka, Anty Jidda ta ce.
"Dad'i na dake in an kira ki a waya sai kin wa mutum kuka, ni dai ki yi hakuri insha Allah nan da
kwana biyu zamu je Kano"
"Shi kenan Anty in kunje ki gaidata"
"Zata ji insha Allah, ya naki jikin?"
"Da sauki, k'afa ta ce dai ta kunbura"
"To Allah ya kara sauki ya rabaku lafiya"
"Ameen nagode"
Sai suka yi sallama. Nan take Zainab ta kira Umma ta gaisheta ta yi mata barka, haka ta kuma
kiran ita Anty Ameena ta yi mata barka.
A ranar suna yarinya taci sunan Nana Khadija, haka suka ci suna suka gama babu Zainab, a
ranar taci kukan kewar 'yan uwanta, ta san da tana gida da da ita za'a yi wannan suna, da kyar
Khalil ya lallasheta.
******
Ranar Juma'a da misalin k'arfe tara na dare ta fara nak'uda gadan-gadan, cikin tashin hankali
Khalil ya d'auketa sai asibiti, nan suka kaita d'akin haihuwa da misalin sha d'ayan dare ta haifo
'yarta mace kyakkyawa mai kama da ita, Khalil ba k'aramar murna ya yi ba. Haka suka kwana a
asibiti, da sassafe Zainab ta kira Anty Jidda ta gaya mata cike da murna taje ta sanarwasu
Umma, ba yabo ba fallasa haka dai suka ce Allah ya raya, Anty Jidda hakan bai mata dad'i ba
jiki a sab'ule tabar falon, haka ta shiga kiran dangi tana sanar musu, kowa dai da irin yadda ya
nuna murnarsa, wasu sunyi Addu'a wasu ko ajikinsu. Anty Ameena ce da Anty Binta ne kawai
suka danyi murna sosai da Inna Kulu. Umma ta kira Zainab ta ce ta shirya kayanta gasu Anty
Jidda nan a kan hanya zasu dawo da ita gida, ba musu ta aminci. Khalil haka bai masa dad'i ba
amma amma yadda suka nuna kamar sun hakura ne, bai mai dasu gida ba ya barsu a asibiti,
yaje gida ya had'a mata kayanta dana Baby ya kwaso su, ya kawo asibiti dan yasan da wuya
suce zasu gidan lsu. Ya kira gida ya sanar da su Baba Husain, sun yi murna suma ba yabo ba
fallasa sannan suka yiwa yarinya Addu'a.
Da misalin k'arfe goma na safe su Anty Binta sun iso, Khalil ya yi musu iso har d'akin da Zainab
take, yaji dad'in yanda suka amsa masa gaisuwarsa, nan suka had'a kayanta driver ya sanya a
mota, Zainab sai murna take yi yau taga 'yan uwanta, Khalil ya amsa yarinyar ya yi mata
hud'uba da suna *ASMA'UL USNAH*, hakan ba k'aramin dad'i Zainab taji ba, bata yi tsammanin
zai sanya sunsn Mahaifiyarta ba, haka ta bangaren su Anty Jidda sunyi farin ciki sosai, a iya
yau da suka ga Khalil sunji sun aminta da shi a yadda suka ga yana bama Zainab kulawa cikin
so da kauna. Haka ya ciro kud'i dubu saba'in ya bawa Anty Jidda ya ce.
"Dubu talatin na ragon suna su siya a can, a bawa Zainab dubu sha biyar na hidimar da zata yi,
dubu Ashirin da biyar kuma a siya kayan