Showing 36001 words to 39000 words out of 81944 words

Chapter 13 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2393

yi alƙawari yau sai ta zane Husna ko da zata
bata tsoro, da mamaki sai ta yi kicibis da Dady suna kallon juna da mamaki.

"Hajiya ya na ga dakinki a rufe ta baya kuma kina ciki? harda na yi zaton ko kin fita ne"

Momy bata iya ba shi amsa ba ta fashe da kukan baƙin ciki tare da bin gefensa ta isa falo tana
kwalawa Husna kira a hargitse, Dady ya biyo bayanta yana tambayarta ko lafiya? bata amsa ba
sai da taga fitowar Husna, idon nan nata cike yake fal da barci alamun kiran Momy ce ya farkar
da ita. Momy ta zauna cike da jin haushi ta ce tana nuna Husna.
"Ka ga shegiyar data rufeni a ɗaki tun misalin ƙarfe biyun rana, har zuwa yanzu daka buɗe ni"

Ta kwashe komai ta gaya masa, Dady ya tari numfashinta.

"Anya Husna zata iya rufe mini É—aki? Du du du kwaya nawa take? Shekarunta takwas har da
zata iya aikata haka? Zo nan Mamana ki faɗa min gaskiya, Ke ce kika rufewa Mominki ƙofa?"

Husna ta matsa gaban Dady tana murza ido cike da shagwaɓa, ta girgiza kai alamar a'a, ya
cigaba da tambayarta ta tana ba shi amsa da kai taƙi ta yi magana, Dady ya kai dubansa ga
Momy.

"Hajiya sai dai in ke ce kika manta kika santa key ta baya kika rufe kanki, ya kamata ki cire
Husna a sabgarki saboda ba tada hankali, kwakwalwarta bata aiki balle harta san ta yadda zata
rufe miki É—aki"

Yana gama faɗar haka ya miƙe ya wuce ciki, Momy kamar ta ɗaura hannu a kai ta yi ihu, a yau
ta yi nadamar É—aurawa Husna cutar hauka, tunda duk abin da take yi mata ba wanda zai yarda
saboda ba tada hankali, hawaye ne ya shiga bin kuncinta tana kallon Husna kamar ta tashi ta
kasheta, sai dai babu halin yin haka, Husna ta kalleta ta yi mata gwalo tana karkaÉ—a jikinta tana
dariya, haka ta juya zuwa ɗakinta tana muguɗawa Momy ɗan ƙaramin mazaunanta. Momy ta
cije leɓe tana jin ƙuna a ranta, takaici da baƙin ciki ya gama rufeta, ta rasa ta wace hanya zata
bi ta hukunta Husna.

*******
Haka Momy ta cigaba da zama da Husna tana yi mata iskancin da ranta ya ke so, gaba É—aya ta
ji duniyar ya yi mata zafi, duk wasu dubaru kanta ya kulle baya kawo mata haske, duk a abin da
ta shiryawa Husna tofa sai ta lalata mata shi, haka rayuwa ta yiwa Momy zafi, daga ƙarshe sai
ta tattara lamarin Husna ta sanya a gefe ta dai na shiga lamarinta, abinci kuwa dole ta girka ta
kai mata har É—aki in ba haka ba a ranar sai Husna ta ja mata asara, haka rayuwa ta yi ta
gudana a wannan gidan, da daÉ—i ba daÉ—i har zuwa tsawon lokaci.

****** **** *******

*BAYAN SHEKARA HUD'U*

Husna ta shiga matakin secondary school tana jss 1, da yake makarantarsu akwai secondary
nan ta cigaba da karatu. Ta k'ara girma da wayo sai dai kuma zuwa yanzu surutunta ya ragu sai
ta koma shuru-shuru, saboda yanzu komai ita ke yiwa kanta tun bata iya ba har ta soma
sabawa da hakan, rayuwa ita kad'ai take yi a cikin gidan ba mai kula ta ko shiga tsabgarta, a in
da take samun kulawa daga gun Sadiq sai Baba mai gadi, a makaranta kuwa sun k'ara
shak'uwa da Khadija ajinsu yanzu ma d'aya, komai na su d'aya, da yake yanzu ta yi wayo bata
zuwa da k'azanta kullun tana k'ok'arin tsaftace jikinta, bata fiye fita yawo ba iya karta bakin gate,
kwata-kwata bata san komai game da Addini ba, Baba ke k'ok'arin koya mata shima sai ya yi
dagaske ne take iya d'aukan karatun, dan bata samu foundation mai kyau ba.

******* *******

*Kaduna*

Anty Zainab zaune suke a falo suna hira da Umma da Anty Jidda, hira suke sosai sai ga wani
yaro an aiko shi daga waje ana sallama da Zainab, cikin fushi ta ce.

"Ka je ka ce bata nan"

Yaro ya fito jiki a sab'ule.

"Haba Zainab meyasa kike haka ne, ki fita ki ga ko waye mana wulaƙanci babu kyau, kuma ai

ba zaki zauna haka ba tare da aure ba, ni bani son shirme"

Cewar Umma, Zainab ta b'ata fuska tana jin haushi.

"Umma ni dai ku yi hak'uri ba zan fita ba, ku kyale ni da zancen auren nan, ba yanzu ba"

Anty Jidda ta yi caraf ta ce.

"Aiko baki isa ba, aure wajibi ne ki yi shi, ai zama haka bai dace dake ba tunda da kuruciyarki,
ni da za ki ji shawarata ma ki amincewa Dr. Idris ya fito ku yi aure kawai, tunda kinga shi saurayi
ne yana sonki sosai, kuma auren ki biyu amma duk da haka ya ce ya amince"

Zainab lokaci d'aya ta ji zuciyarta ta dagule har hakan ya nuna a fuskarta, nan ta tuno da Khalil
da Husna abar ƙaunarta, hawaye ya fara fita a idonta, jikin Anty Jidda ya yi sanyi Umma ma
haka, Zainab ta ce cikin kuka.

"Anty Jidda a kullun aka min zancen aure ana tada min da tsohon mikin dake manne a zuciyata,
kina ganin zan iya wani aure a yanzu bayan auren Khalil da marigayi yaya Al'amin? wallahi ba
zan iya ba, in dai Khalil yana raye to ina nan ina jiransa sai dai in yaƙi karb'ata a karo na biyu,
shi ne zanyi haƙuri in auri wani"
Kuka ne ya ci k'arfinta ta mik'e da sauri tabar falon cike da k'unar zuciya

"Ikon Allah, to Allah ya kawo miki mafita Zainab, lamarinki ni yanzu har tsoro yake bani, amma
ta yaya zaki sanya ran k'ara ganin Khalil? bayan alƙawari ya yi ba shi ba gidan nan, in da zai zo
ai da tuni ya zo, Allah kad'ai yasan rayuwar da suke ciki yanzu, ohh ko wani hali takwarata take
ciki Allah kad'ai masani"
Cewar Umma, ta ji bugun zuciyarta ya k'atu, wani hawaye mai zafi ya fito daga idonta, ta kuma
cewa.

"Wallahi da Husna nake kwana nake tashi a raina, a kullun ina tunanin ya rayuwarta take ciki?
ban san cewa yarinyar ta shiga zuciyata ba sai bayan barinta gidan nan, Allah kasa tana
rayuwar jin daÉ—i"

Anty Jidda da idonta ya kawo kwalla ta amsa da Ameen.

Nan suka cigaba da hira har tsawon wani lokaci, kiran sallan la'asar ne ya tada su ko wanne ya
nufi É—akinsa.

******** ********

*Kano*

Da safe Husna ta yi shirin makaranta ta fito da sauri dan ta kusa latti, karo taci da mutum a
bakin k'ofar da zai sadata da waje, yaya Nura ne a tsaye fuskarsa tamau ba alamar annuri, ya
girma shima dan ya kai sheraka ashirin da biyu, ya ce cikin tsawa.

"Dan ubanki baki gani ne zaki bangaje ni, mahaukaciyar banza dana wofi"

Husna ta murgud'a masa baki.

"Eh d'in ba kai bane ka tsaya a anya kuma ni ba mahaukaciya ba ce"

"Ni kike gayawa haka?"

Sai ya d'aga hannu zai gaura mata mari, Husna gaba d'aya ta runtse ido ta k'ank'ame tana jiran
saukar marin, Nura ya tuna wani abu sai ya girgiza kai ya sauke hannunsa ya fasa marinta yana
murmushin mugunta.

"Soon zan yi maganin ki"

Ya yi kwafa sannan ya matsa ta wuce tana masa gwalo, dariya ta ba shi ya ce.

"Zaki shigo hannuna wallahi sai na rufe bakin rashin kunyar nan"

Ya fara k'issima abin da yake shiryawa a kanta, ya yi dariya kana ya wuce cikin d'akinsa ya
kwanta, saboda yau baya sha'awar zuwa makaranta dan shi karatun baya gabansa sai
shaye-shaye da biye-biyen 'yan mata.

Husna ta isa makaranta suka had'u da Khadija suna hira.

"Husna in mun yi hutun makaranta a Kaduna zanyi hutuna gurin kakanni na, in gaya miki akwai
wata ƙanuwar Abbana mai kirki inna je d'akinta nake sauka tana siyo min kayan dad'i da yawa
kuma har office d'inta tana zuwa dani, yaron ta little Al'amin mai kyau wallahi in ta wasa da shi"

Husnah ta yi rau-rau da ido kamar zata yi kuka.

"Kin ji dad'i, ni Dadina bai tab'a kai ni ko ina ba kullun ina gida, da Dady zai yarda dana biki mu
yi hutun tare"

"Aiko dana ji dad'i, kin ga sai Anty Zainab ta rik'a fita damu tana siya mana kayan dad'i, kuma
wallahi zata so ki saboda tana da son yara sosai"

"Uhum ai Dady ba zai bari ba, baya siya min komai yanzu bana ganin shi sai weekend kuma ya
dai na wasa dani, yanzu Uncle kad'ai yake so na sai Baba mai gadi"

Ta k'arasa maganar kwalla na fitowa daga idonta, Khadija ta jinjina maganar duk jikinta ya yi
sanyi.

"Ki daina kuka ai Allah zai saka miki, nima kin ga yaya Sadiq d'inmu wallahi ina son shi saboda
yana siyo min kayan dad'i da kayan wasa, a nan Kano yake aiki, duk weekend yana zuwa
gidanmu"

Nan dai su kai ta hiransu gwanin sha'awa har aka tashe su makaranta.


******** *********

Bayan sun gama exam din k'arshen zangon jss 1, su Khadija suka tafi Hutu Kaduna, Husna
taso ta bisu amma bata ga fuska gun Dady ba balle ta masa maganar, ga shi Uncle Sadiq d'inta
shima ya tafi hutu wurin iyayensa a Kaduna, kuma sai ya yi sati biyu zai dawo, haka ta cigaba
da zama shuru ko wurin Baba bata fitowa, daga falo sai kitchen kullun tana d'aki, wani lokaci ta
yi kuka mai isar ta, wani lokacin kuma ta rik'a yin surutu ita kad'ai kamar mahaukaciyar gaske
har barci ya sace ta saboda ƙuncin *KAƊAICI.*


**********

*Kaduna*

Khadija sun fara Hutu mai cike da jin dad'i da farin ciki, duk suna falo gaba d'aya banda
iyayensu maza, Khadija ta soma basu labarin k'awarta Husna da ta so ta biyo su, nan da nan
Zainab ta ji zuciyarta ya harba da k'arfi, a'uzubillahi ta rik'a karantawa a zuciyar ta, Khadija ta
cigaba da basu labarin yadda Husna ke wahala a gidansu. A duk hutun da zasu zo Kaduna
Khadija sai ta yi hiran Husna, sai dai abin mamaki takan yi hirarta ba tare da ambaton sunanta
ba, sai dai ta ce k'awata sunan da take kiranta kenan, kuma ikon Allah ba wanda ya damu da
yaji sunan ƙawarta ta a tunaninsu duk shirmen Khadija ce, haka take surutunta ba mai kulata
har ta gaji ta yi shuru, lokacin barci ya yi kowa ya kama gabansa.

Zainab ce kwance a kan gado tana ta juyi damuwa ce fal a zuciyarta, ta tashi ta zauna ta duba
gefenta na dama Khadija ce kwanta sai barci take yi, gefen hagunta little Al'amin ne da Kamal
k'anin Khadija, d'aga kanta ta yi sama hawaye mai zafi yana fitowa da idonta tana zancen zuci.

'Ko wani hali Husna take ciki? Allah kad'ai ya sani, Khalil meyasa zaka min haka, ban tab'a
tunanin zaka yi nesa dani irin haka ba, ka tafi ka barni da guba azuciyata wanda har yau ban
samu ganinta ba. Allah ka bayyana min su na yi tozali da su kafin nabar duniya'

Ta shafa a fuskarta tare da mik'ewa ta shiga toilet ta d'auro alwala, ta fito ta shiga gabatar da

sallar nafila har gabanin sallan Asuba, ana kira ta mike ta gabatar da sallar Asuba, ta yi Addu'a
ta mik'e ta hau gado, nan take wani nannauyar barci ya d'auketa mai dad'i.
[10/26, 8:01 AM] Rahma Kabir🌺: *_Page 29 ~ 30_*


*Bayan Shekara biyu*

Shekaru sun ja kwanaki sun shud'e, haka Husna ta cigaba da zama a cikin wannan rayuwa na
*Kad'aici*, karatunsu ya yi nisa, a yanzu sun kammala final exam na jss 3 zasu shiga ss1,
shekararta sha hud'u a duniya, ta kara tsawo da girma sosai, sai kuma ta kara wayo, kyawunta
ya dad'a fitowa sosai, ta soma k'irgen dangi natsuwa ya shigeta, duk wani tsalle-tsalle yanzu
bata yin shi, shuru shurun ta ya k'aru, magana sai ya zama dole take yinsa, amma kuma ikon
Allah in dai da Uncle Sadiq ne, hira take da shi sosai kamar ba ita ba, shakuwar su ya k'aru
sosai duk wani abin da ya shafeta shi yake mata.

Da safe tana kwance bisa gado, barci take mai cike da mafarkai barkatai, fitsari ya matseta ya
k'ulle mata mara sosai, da sauri ta farka ta fad'a bayi, ta tsuguna ta yi da tsarki, mik'ewar da
zata yi sai taga jini baje a k'asa, ido ta zaro waje kamar zasu fad'o k'asa saboda tsananin tsoro,
pant d'inta ta duba sai ta ga ya jike da jini, a razane ta cire shi ta jefar gefe, ta fito ta sanya wani
pant d'in, ta fito falo cikin sauri ta tadda Momy zaune tana karanta wani littafi, jikinta yana rawa
ta isa gun Momy, ta ce cikin rawar murya.

"Momy, Momy jini a jikina"

Ta fara kiciniyar d'aga siket dinta dan ta nanuwa Momy pant d'inta da shima ya k'ara baci da jini,
wani mugun kallo Momy ta bita da shi.

"Dan ubanki ni sa'ar yinki ce, to ba jini ba ko da tsokar jikinki ne bai shafeni ba, kima mutu mana
sai me, tsakani na dake bamu sulhu har abada, idan kin mance wahalar da kika bani a baya to
ni ban mance ba. Husna na tsaneki bana kaunar ganinki a gidan nan, maza b'ace min da gani
tun kafin in harzuk'a inyi watsa-watsa dake a nan, wawiya jaka"
Jikin ta yana rawa ta matasa nesa da ita, ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita, Momy tashi ma
ta yi ta barta a nan falo ta kowa d'aki cike da jin haushinta. Husna ta tsaya shuru tana nazarin
mafita, ta ga ba sarki sai Allah, da azama ta fita waje bata ga Baba mai gadi ba, baya bakin
gate da sauri ta bud'e k'ofar ta nufi gidan Uncle Sadiq d'inta, ta yi sa'a k'ofar gidan a bud'e yake
tana turawa taga ya bud'e a sittin ta shiga, k'ofar falon ma a bud'e ta samu ta kutsa kai ta shige,
zaune yake a falo kan cushing yana danna system d'insa, ganinta ya yi ta fad'o d'akin a guje ba
sallama tana haki kamar an korota, ta kara fashewa da sabon kuka, a firgice ya aje system d'in
ya taso cikin sauri ya shiga tambayar ta ko lafiya? Ta kara sautin kukan ba sassauci, hankalin
Sadiq ya k'ara tashi dan a iya saninsa da ita bata yin kuka irin haka sai in wani abun ya
tsananta, kuma rabon da yaga kukanta irin haka tun tana k'arama da Momy take dukanta, ya
k'ara rikicewa ya ce cikin damuwa.

"Haba Husna ki gaya min me aka yi miki ko wani ne ya rasu? Gaba daya duk kin tayar min da
hankali"

Husna ta girgiz kai alamar a'a.

"To me aka yi miki? gaya min mana Husnata"

A wannan lokacin sai ta sassauta kukanta ta ce cikin muryar kuka.

"Uncle zan mutu"

"Da a ka yi miki mene?"

Husna bata ba shi amsa ba sai ta shiga kiciniyar daga siket d'inta ta kai shi zuwa gwiwanta, ta
zazzago da pant d'inta, Sadiq dai ya zubawa sarautar Allah ido dan ganin wauta da shirmen
Husnar.

"kalla ka gani, jini ne a jikina"

Ta ce da rawar murya, bai iya gani ba da sauri ya kauda fuskarsa.

"subhanallahi! Meye haka Husna? maza ki mai da pant din"

Ya yi maganar yana kunshe dariya amma sai da ta kubce ya yi mai isar sa, Husna ta tsayar da
kukan ta soma kallonsa sororo baki bud'e, mamaki ne k'arara a fuskarta.

"Uncle dariya kake yi zan mutu ko, mai makon ka yi kuka shi ne zaka rika murna ko"

Nan take Sadiq ya tsanye dariyarsa.

"A'a Husna ba zaki mutu ba akwai sauran lokaci insha Allah, yanzu jirani ina zuwa"

Bai jira me zata ceba ya shiga bed room d'insa, ya hada mata ruwan wanka a toilet, ya lek'o ya
kirata ta bi bayansa har toilet din, ya nuna mata ruwa.

"Ga shi nan ki yi wanki mai kyau, ga tawul nan ki d'aura kafin ki fito zanje na siyo miki kaya
yanzun nan sai ki jirani in kin gama karki mai da kayan jikinki"

Gyada masa kai kawai ta yi alamar to sai ya fita ya barta ya dauki key mota ya fita cikin sauri.

Harta kammala wanka ta fito bai dawo ba, ta kasa zama a gefen gadon tana tsoron karta b'ata
masa zanin gado tunda har yanzu jinin yana d'iga, da sauri ya turo k'ofar bed room d'in ya kutso

kai duk tunanisa bata fito ba, gabansa ne yaji ya fad'i yadda ya ganta daga ita sai tawul, runtse
idonsa ya yi na tsayin minti biyu kana ya bud'e a hankali, wani bakon yanayi yaji yana masa
yawo a jikinsa, kau da kansa ya yi gefe jikinsa a sanyaye ya ce.

"Har kin fito?"

"Eh"

Ta ce cikin dishewar murya, ya shiga ciro kayan da ya siyo a leda, doguwar jallabiya bak'a, sai
riga da wando na Pakistan brown, pant dozin, sai sink'in always guda goma, ba tare da ya kuma
kallonta ba ya ce.

"Ga wannan kayan ki zab'a a ciki ki sanya sai kuma wannan shi zaki saka ya tare abun"

Ya bud'e always d'aya ya d'auki pant guda d'aya.

"Ki kalla yadda zaki rik'a sanya always akan pant dinki"

Nan ya gwada mata yadda ake manna always jikin pant, ya mik'a mata.

"ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login