Showing 51001 words to 54000 words out of 81944 words

Chapter 18 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2392

da sauri Likitocin da Sadiq suka yi kansu, da kyar suka b'anb'are hannun Husna a
wiyan Momy, suka mai da ta kan gado suka danne ta, tana wani irin gunjin kuka.

"Ku barni na kasheta kamar yanda taso kashe mana Husna, sai mun rama mata, ku sake ni ku
sake ni"

Nan Sadiq da Baba suka shiga tofa mata Addu'a, suma likitocin da yake Musulmai ne suka
shiga tofa mata har sai da ta tafi, kafin nan Husna ta yi atishawa mai k'arfi ta ta shi tana kallon
kowa dai-dai, ita kuma Momy durk'ushewa ta yi tana mai da numfashi tare da tari mai k'arfi, da
taga Husna ta ta shi zaune ba arziki ta mik'e da sauri cike da borin kunya ta d'auki kwandon
abincin da ta zo da shi ta fita jiki ba kwari, ko sai anjima ta kasa furtawa, duk suka bita da kallo
kowa da abin da yake sak'awa a zuciyarsa.

Sadiq ya matsa mata maclean a akan brush d'in da ya siyo musu, ya kai ta bayi ya fito ya bata
wuri, ta wanke baki tare da d'auro alwala ta fito, ta gabatar da sallar da ake binta, bayan ta idar
ta koma kan gado ta zauna tare jingina bayanta a jikin pillow.

Nan likita ya d'aura ta kan magani, Sadiq ya mik'a mata cup din tea da ya had'a mata tare da
take away na abincin da ya siyo musu. Dady bin Sadiq ya yi da kallon mamaki, nan take yaji ya
kwanta masa a rai, yana jin haushin kansa daya yanke musu hukunci ba tare da bincike ba,
tabbas zuciyarsa na gaya masa Sadiq yaron kirki ne. Baba yana gefe yana kallonta cike da
tausayawa akan ciwon da yake damunta.
[10/30, 3:43 PM] Rahma Kabir🌺: *_Page 43 ~ 44_*


*Bayan kwana biyu*

Su Dady sun ji sauki sosai, dan sun samu kulawa mai kyau a gurin likitoci tare da kulawar Sadiq
da Baba, kwanan su biyu aka sallame su.

Bayan sun isa gida, Dady ya wuce sashinsa, sai da ya watsa ruwa kana ya fito ya sanya kaya
marasa nauyi, ya umarci Husna ita ma taje ta yi wanka ta canza kaya, falo ya zauna ya kunna
tv yana kallon tashar al-jazeera, fanka na juyawa a hankali iska na kad'a shi, hakanan ya tsinci

kansa cikin nishad'i, bayan wani lokaci sai ga Husna sanye cikin doguwar riga na shadda
wanda ya kamata daga sama, fuskarta fayau ba kwalliya amma duk da haka bai hana bayyar
kyanta ba, Dady ne ya bita da kallo, ta rame sai ta yi tsawo, tausayinta ne ya kama shi cike da
kulawa ya ce.
"Har kin yi wankan?"

"Eh Dady na yi har da sallar azahar"

"Da kyau kin kyauta, zoki zauna ki huta kema"

Husna ta zauna gefensa kan 3sitter ta cigaba da kallon TV.

*****
B'angaren Momy kuwa tun ranar da ta dawo gida daga asibiti, ta rasa abin da ke mata dad'i,
abin duniya ya ishe ta, sai ta kiran Haj. Uwani ta labarta mata duk abin da ya faru, cike da
damiwa ta ce.

"Haj. Habee ina ga sai dai mu hakura dan wallahi nima ina cikin matsala, Alhaji ya hanani fita ko
nan da can, ya ce in har na fita a bakin aure na, wai duk yawace-yawacen dana ke yi ana gaya
masa, har zargina yake yi wai ina bin maza, ke in k'ark'are miki labari, a ranar ya cimin mutunci
a gaban kishiyata, na yi kuka har na gode Allah, aure na yanzu lilo yake yi dan haka na saduda
na barwa Allah, zan rik'e aure na tunkan ya gutsire"

Ajiyar zuciya Momy ta yi wanda ya bayyana tsantsar damuwar da take ciki, cike da karayar
zuciya ta ce.

"Wallahi ni kaina ya kulle, ina tsoron matakin da Alhaji zai d'auka a kaina, kuma wallahi ina
sonsa ban shirya rabuwa da shi ba"

"Ato tunda kina son zaman aurenki ai sai ki saduda kema ki ba shi hakuri ki gyara zaman
aurenki, dan ni yanzu na hakura da komai na kama Allah, tunda na yi asirin in fidda kishiyata,
na mallake Alhaji amma bai je ko ina ba ya karye, dan haka zan yi biyayyar aure, ki yi tunani na
barki lafiya"
Bata jira mai Momy zata ce ba ta kashe wayar tare da bin wayar da tsaki.

"Allah ya wadaran kawar banza, duk ke kika jamin matsalar nan, dole ma in rabu dake dan kar
ki ja min na rasa aure na"

Momy kuwa mamakin Haj. Uwani ta yi yadda ta sauya lokaci d'aya, damuwanta ya k'aru da
tunanin matakin da Dady zai dauka a kanta.

Yau ma dasu Dady suka dawo tanajinsu ta kasa motsi mai k'arfi, kunya ce da nadama ya cikata
tana jin nauyin had'a ido da shi da fargaban hukuncin da zai yanke mata, shiyasa ta kulle kanta
a d'aki tana kai ko mo da tunani bar katai.

Sadiq ne ya yi sallama rik'e da leda a hannunsa, cike da farin ciki Dady ya amsa masa tare da
masa umarnin ya zauna, ya zauna a k'asan kafet Dady ya ce ya zauna a kujera, bayan ya
zauna ya gaishe shi tare da yi masa ya jikinsu, Husna ta gaishe shi cike da girmamawa, Sadiq
ya ce.
"Husna tashi ki je ki d'auko plate da cup a cikin"

Da hanzari ta mik'e ta wuce kicin ta d'auko ta dawo ta mik'a masa ya amsa, take away na abinci
daya siyo musu ya fara juyewa a plate d'in ya sanya ta ta d'auko tsokali, ya mik'awa Dady na
shi ita ma ya mik'a mata nata, ya ajiye goran juice a kan center table tare da cup d'in, ya matsar
da shi gaban Dady, sai ya mai da hankalinsa ga tv, Dady na binsa da kallo cike da k'auna a
zuciyarsa, yana jinjina karamci irin na Sadiq, ya fara cin abincin, ita ko Husna tak'i cin nata ta
kalli Sadiq.

"Uncle ina naka abincin?"

Sadiq ya kalleta da murmushi.

"Na ci nawa"

Husna ta yi murmushi sannan ta fara cin abincin. Bayan sun kammala Dady ya kai dubansa ga
Sadiq.

"Sannu da k'ok'ari mungode kwarai, Allah ya saka maka da alkhairi ya yi maka albarka. Ada ina
yi maka wani irin kallon, amma cikin k'ank'anin lokaci na fahimce ka, ka yi hakuri"

Sadiq kansa a sunkuye ya amsa da ameen tare lda yiwa Dady godiya. Dady ya nima Sadiq ya
kira masa Baba mai gadi, shima godiya Dady ya yi masa tare da niman alfarma a nimo musu
'yar aiki wacce zata rik'a kula da Husna tare da yi musu girki, nan Baba ya ce.

"Ai Alhaji zan je na lalubo Jimmai mai aiki domin ta dawo aikinta, dan tana da kirki kuma ta
taimaka wa Husna sosai"

Cikin farin ciki Dady ya amince da haka kana suka cigaba da hira dukansu, Husna na kallon tv
bata sanya musu baki ba.

***** *****

Tun daga wannan rana Momy taki yarda su had'u da Dady, in kuwa sun had'u kanta na sunkuye
bata iya had'a ido da shi, shi ko Dady kota gaishe shi bai amsawa kuma har zuwa lokacin bai
yanke wani hukunci a gareta ba ya zuba mata ido, haka ta koma rayuwar *kad'aici* ba mai
shiga safgarta, Nura ma baya kwana gidan yanzu sai ta yi kwanaki bata sanya shi a ido ba.
Hatta Jimmai mai aiki Dady ya gargad'eta sosai akan Momy, ita ke musu girki da gyaran gida, in
kuma Dady ya fita suna tare da Husna har ya dawo saboda aikin kwana take yi. Daga Husna
har Dady yanzu suna rayawan walwala da jin dad'i.

Dady ya sanya wasu su yi masa bincike sosai a kan Sadiq, sannan Baba mai gadi ya ba shi
labarin duk taimakon da ya yiwa Husna, wannan yasa Dady k'ara samun natsuwa da Sadiq
sosai, duk kuma binciken da ya yi bai ji wani abu b'atanci ga Sadiq ba, sai dai bai samu wani
cikakken labari game da iyayensa ba, duk wanda zai tambaya sai suce basu sani ba amma dai
sun san shi kad'ai yake rayuwa a gidan kuma yaron kirki ne.

***** **** *****

*A Kaduna*

Husna pharmacy ya hab'aka, kullun suna cikin cikowar jama'a, Anty Zainab ta tattara
natsuwarta gaba d'aya wajen business d'inta, taki bawa mane manta dama kan zancen aureta,
a kullun burunta bai wuce Allah ya had'ata da masoyinta Khalil tare da 'yarta Husna abar
k'aunarta, 'yan uwa sunyi mita har sun gaji kan maganar ta yi aure, ita dai kullun cewa take in
lokaci ya yi zata yi, Little Al'amin yana samun kulawa sosai wajen Zainab, ya yi wayo da girma
wanda har ya soma zuwa makaranta.

******

*KANO*

_*Gidan Yaya Ismail*_

Khadija ta mutu kan son Yaya Sadiq wanda tun tana yi a b'oye harya fito fili, Mahaifiyarta Anty
Ameena tana ja mata kunne tare da yi mata fad'a akan rawar kan da take yi a kan Sadiq, wanda
shi sam bai san tana yi ba. Akwai wani zuwa da suka yi Kaduna, Sadiq na d'aki ta same shi a
can, juice ta kai masa ya amsa cike da kulawa ya sha, nan ta zauna ta fara masa surutu,
hayaniyarta ya ishe shi ya daka mata tsawa ya koreta, cike da kuka ta fita falon Ammi Jidda
tana kuka, nan Anty Jidda ta sameta ta tambayeta dalilin kukan, nan ta labarta mata abin da Ya
Sadiq ya yi mata, cike da jin haushi Ammi ta same shi a d'aki ta yi masa tatas, hakan da Ammi
ta yi masa sai ya k'ara masa tsanar Khadija, tun daga lokacin ya k'ara tamke mata fuska domin
ya gane take takenta. Hakan da ya yi bai sa ta sauya ba, ko gidansu yaje na nan Kano sai ta yi
ta shige masa, a haka har ya gane manufarta sai ya rage zuwa gidan. Wanda a yanzu duk
dangi suna ganin kamar soyayya suke yi, saboda abu kad'an Khadija zata ce Sadiq, kowa na
murna da wannan had'i da suka yiwa kansu. Abin da basu sani ba, shi sam ba haka bane a gun

Sadiq bai san da labarin bama.

*******

Haka rayuwa ya yita tafiya, har su Husna sun kammala jarabawarsu na k'arshen secondary
school, bayan sun fito daga d'akin jarabawa, Khadija ne rik'e da waya a hannunta tana ta
danna-danne, Husna tana gefenta suna tafiya tare, wani wuri suka samu suka zauna, Khadija ta
mai da kallonta ga Husna..
"Besty yau ga shi mun gama makaranta amma baki tab'a zuwa gidanmu ba, gwara ni nazo sau
d'aya, ga shima ba phone a hannunki balle mu rik'a waya"

Husna murmushi ta yi.

"Ki yi hak'uri kin san Dady na baya barina fita ko zani school sai ya jamin kunne kar in biya ko
ina, yanzu dai ki bani number ki zan kira ki da number Dadyna, in ya so sai ki yi saving muna
communicating da shi, hakan ya yi miki?"

"Wato ba zaki zo bama sai dai ki yi min waya, to ba matsala ai na kusa barin Kano ma gaba
d'aya, zan koma Kaduna a cen zan cigaba da karatu"

"Aiko na yi miki murna, ni dai ina son zuwa Kaduna amma banda kowa a can, ko a nan Kano ba
wani yawa familyn Dady suke da shi ba"

"To wai ke ba kisan family Momy din ki ba?"

Husna ta yi murmushi wanda bai kai ciki ba ta ce.

"Ban san su ba, ko na fara yiwa Dady maganar Momyna sai ya hauni da fad'a, tunda naga baya
so sai na kyale shi, har yau ban san Momy na ba"

Ta k'arasa maganar da kuka, Khadija duk sai taji jikinta ya yi sanyi.

"Karki damu insha Allah zaki santa ki yi ta Addu'a, amma ina fatan zaki zo bikina da yaya Sadiq,
dan dana soma karatu za a sanya biki, a d'akina zan k'arasa"

Cike da farinci ciki husna ta ce.
"Wai dan Allah da gaske kike yi aure zaki yi da wuri?"

"Kwarai kuwa me zan tsaya jira, tun ina k'arama Allah ya jarabceni da son yaya Sadiq, dan haka
lokaci ya yi ba zan bari wata ta kwace min shi ba"

Husna ta yi dariya.

"Haba k'awata akwai sauran lokaci, dan da k'uruciya a tare damu, shekarun mu 17 fa"

"Eh, ai ba yanzu na ce ba, at least nan da shekara d'aya ko biyu za a yi bikin"

"Ok, Allah ya kaimu, amma ni a nawa ra'ayin sai na kammala degree na kan inyi aure, ni totally
ban ma san ya so yake ba balle har in fara, ni wallahi Khadija har mamaki kike bani kina
kwailarki kin san Soyayya"

Duukan wasa Khadija ta kai mata.

"Eh na ji d'in, ai ba wani nake so ba sai yayana, kin ga kuwa abu ne na family"

"Hakane, yaushe zaki tafi kaduna?"

"Ina ga nan da kwana biyu zamu tafi"

"To Allah ya kaimu"

"Ameen".

Nan suka ta shi suka cigaba da tafiya tare da yin hira gwanin sha'awa har suka kai bakin hanya,
suka samu abin hawa duk suka nufa gida cike da kewar juna.

Husna ta isa gida da misalin k'arfe biyar, direct d'aki ta wuce ta watsa ruwa ta sanya bak'ar
jallabiya mai d'auke da kwalliyar Golding brown, ta fito falo ta zauna ta kunna TV ta soma tallon
tashar Arewa24, Jimmai ce ta fito daga kicin ta ce.

"Au, Husna a she kin dawo shi ne baki ni meni ba?"

"Uhum Mama Jimmai ki yi hakuri, wallahi na gaji sosai kin san yau muka kammala exam
d'inmu"

"Hakane to ya jarabawar, da fatan kun gama lafiya, Allah yasa ya fito lafiya"

"Ameen ya rabb, Mama Jimmai wai Dady bai dawo bane?"

"Ya dawo bayan Sallar Juma'a, Sadiq ya shigo sun fita tare, dan shi ne ma ya yi driving d'insu"

"Ok, Allah ya dawo dasu lafiya"

"Ameen, bari na kawo miki fruit salad d'in da na had'a miki"

"Wallahi kamar kin san ina tunanin had'awa yanzu"

Jimmai ta mik'e tare da cewa.

"To bari na mik'o miki, ban ma yi komai ba Dady ya ce kar na yi girki, shiyasa na ce bari na
had'a miki dan nasan kina so"

"Gaskiya naji dad'i nagode kwarai"

Bayan ta kawo mata Hunsa soma sha, suna hira tare da kallon TV, Momy ce ta fito falon, duk ta
lalace ta rame, bata kalle su ba ta wuce kicin, ta d'auko abin da take buk'ata ta wuce su, suma
babu wanda ya kulata harta shige, Husna ce ta ce.

"Ni ko Mama Jimmai ina son yima Momy magana amma ina tsoro"

"Karki kuskura ki soma dan Alhaji ya ja min kunne sosai, dan haka ki adana maganarki"

Daga nan bata kuma cewa komai ba suka cigaba da kalon TV.


Su Dady basu dawo ba sai bayan Sallar Isha'i, sun samu falon ba kowa, Dady ya nufi sashinsa
bai ga Husna ba sai ya wuce sashin Jimmai, can ya jiyo hirarsu ya k'arasa cike da farin ciki a
fuskarsa ya yi sallama, duk suka amsa masa Husna ta mik'e cike da shagowa ta ce.

"Dady shi ne kuka tafi kuka barni kuma kunsan yau ne na gama exam"

Murmushi ya yi wanda har sai da hak'oransa suka bayyana.

"Haba 'yar lelena kar ki yi kuka, fitan da muka yi dan ke na yi, zo mu je ki gani,Jimmai kema zo
mu je"

Nan suka d'unguma gaba d'ayansu suka nufa falo.

Sun samu Sadiq zaune shi kad'ai, nan suka gaisa, duk suka samu guri suka zauna, nan Dady
ya fara kiciniyar bud'e wani kwali, katon cake ne ya bayyana wanda ya sha decoration mai
d'auke da sunan Husna a kai, cike da farin ciki Husna ta isa wurin cake d'in, tana kallo, Dady ya
d'ago tare da yi mata murmushi.
"Wannan cake d'in naki ne, na taya ki murnar gama exam"

Da murna ta rungume Dady tana tsalle, duk suka sa mata da dariya, nan suka taya ta yanka
cake d'in, Dady ya yanka ya sa mata a baki, farin ciki ne fal cikinta tana ta dariya wanda ya k'ara
bayyana mata kyawunta, duk suna mamakin dama Husna na dariya haka, a takaice dai wani

'yar kwarya kwaryan walima Dady ya shirya mata a wannan dare, sun ci sun sha sunyi hani'an,
shima Baba mai gadi ba a barshi a baya ba dan da shi aka ci walima, haka shima Yasir abokin
Sadiq ya zo walimar, gasu Inna da Baba Husain sun hallara, sai wani Abokin Dady mai suna
Alhaji Ahmad, wurin aikinsu d'aya, shima yazo tare da iyalinsa, matarsa Halima tare da yaransu
mata biyu Minal da Kausar, Minal tsarar Husna ce amma ita yanzu take SS2 sai Kausar da take
JS3, Husna taji dad'in ganinsu wanda daga nan suka kulla k'awance da Minal.
Momy na cikin d'aki tana jinsu abin duniya ya isheta, tana son fitowa amma tsoro ya hanata. Sai
misalin k'arfe goma taron ya washe in da Dady yasa Sadiq ya mai da su Baba Husain gida,
Alhaji Ahmad shima ya wuce da iyalensa, Jimmai ta wuce d'aki dan tana so ta kwanta barci
yana damunta, daga Dady sai Baba aka bari a falon, Husna ta raka Sadiq kai su Inna gida,
Yasir shima tuni ya wuce gida.

Bayan sun dawo daga kai su Inna, Sadiq ya yi parking mota suka fito, har Husna ta wuce shi,
sai ya kirata ta dawo ta tsaya.

"My Husna ina taka yi murnar kammala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login