Showing 54001 words to 57000 words out of 81944 words

Chapter 19 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2393

karatunki, Allah ya fiddo sakamako mai kyau"

"Amin uncle"

Sai ya cigaba da cewa.

"Da fatan zaki mai da hankali kan karatunki na islamiya, yanzu saura miki shekara d'aya ki yi
saukan Al-Qur'ani"

Insha Allah zan mai da hankali"

Sai ya mik'a mata wani leda mai d'auke da kwali a ciki.

"Wannan shi ne kyaunarki da fatan zai saki farin ciki"

Cike da murna ta amsa tare da cewa.

"Uncle meye a ciki?"

Sadiq ya yi mata hararan wasa.

"In kin shiga ciki kya gani"

"Nagode uncle Allah ya kara bud'i"

Ta ce cike da tsantsar farin ciki.

"Ameen Husna, kuma godiyar ya isa haka, mu shiga ciki"

[10/30, 7:13 PM] Rahma Kabir🌺: *_Page 45 ~ 46_*

Suna shiga falo ta mik'awa Dady kyautar da sadiq ya bata, ya amsa tare da tambayarta.

"Meye a ciki, na waye?"

Dubanta ta kai ga Sadiq wanda yana kallonsu yana murmushi, ta ce.

"Uncle ne ya bani kyautar gama exam"

Murmushi Dady ya yi mai kayatarwa.

"Madallah, Allah ya saka da Alkhairi ya muku Albarka, shiga ciki ki bud'e abin ki"

Amsa ta yi ta wuce d'aki cike da murna fal cikinta.

Baba mai gadi ya mik'e yama su Dady sai da safe ya koma bakin aikinsa, falon ya rage daga
Dady sai Sadiq, Dady ya gyara zamansa a k'asan carpet d'in falon ya jingina da jikin kujera ya yi
gyaran munya.

"Sadiq matsonan ina son magana da kai"

Cikin ladabi ya matsa kusa da shi ya risina, Dady ya cigaba da cewa.

"Sadiq nagode da duk irin d'awainiyar da kake yi da mu, Allah ya saka maka da Alkhairi ya yi
maka Albarka"

"Ameen Dady"

"Yauwa, ina son mu yi wata magana ce mai mahimmanci"

Nan Sadiq ya kara tattaro duk natsuwarsa ya gyara zama.

"Ina so ka gaya min meya ke tsakanin ka da Husna?"

Cike da mamaki Sadiq ya d'ago kai ya ce.

"Babu komai Dady, duk abin da nakewa Husna ina mata ne matsayin kanwata ta jini, banda
wannan babu wani abu a tsakanin mu"

Dady ya girgiza kai alamar gamsuwa.

"Na fahimta! Sadiq gaskiya na zauna na yi tunani da nazari a kan abin da ya kamata na biya ka

bisa k'ok'arin da ka yi da Husna a lokacin da ta rasa gata, ka tallabi rayuwarta ka zame mata
Uwa da Uba, abin da na yanke zan yi maka shi ne na baka Husna ka aureta in har kana son ta"

Cikin razana Sadiq ya d'ago fuska su ka yi ido hud'u da Dady, bugun zuciyarsa ya k'aru tare da
tsananin rud'ewa, dan bai tab'a tunanin wannan maganar daga gunsa ba.

'Son da yakewa Husna bai wuce na 'Yar Uwarsa ba, bai tab'a kawo aure tsakaninsu ba, kuma
Husna ma k'arama ce yanzu, shi da ya da shekara talatin da daya ya bata kusan shekaru sha
hudu, ya hakan zai yuwu?'

Duk wannan maganar a zuciyarsa yake karanto su. Shurun da ya yi na tsayin lokaci bai ce
komai ba, shi ne ya tabbatarwa Dady Sadiq tunani yake yi, Dady ya gyara zama ya ce.

"Sadiq ka kwantar da hankalinka, in har ba kada ra'ayi zan jenye k'udirina akan ka, dalilin da
yasa na zab'eka ka zama sirikina, ba komai bane face, kai yaron kwarai ne kuma mai tausayi da
taimako ga kuma biyayya, ka had'a qualities da duk wani Uba zai gani yaso ya had'a zuri'a da
kai, Husna yarinya ce kuma tana buk'atar taimakonka, sannan akwai shak'uwa mai k'arfi a
tsakaninku, na aminta da kai Sadiq, na san zaka kula da Husna ko bayan bani a doran k'asa,
kai mutum ne mai amana"

Dady yaja numfashi ya cigaba da cewa.

"Na baka nan da sati d'aya kaje ka yi tunani, duk abin da ka yanke sai ka sanar min, bana so ka
zurfafa tunani, kuma karka b'oye min duk abin da ka yanke, zaka iya tashi ka tafi"

Cike da sanyin jiki Sadiq ya ce.

"Dady na d'auke ka mahaifi agare ni kuma ba zan iya jayayya da kai ba, batun inje inyi tunani
bai taso ba, na amince na amshi tayin ka zan auri Husna kuma insha Allah zan rik'eta Amana,
Dady na d'auki Husna 'yar uwa a gareni ba zan juya mata baya ba"

Ya k'arasa maganar zufa na keto masa, yana jin wani yanayi a zuciyarsa, wanda bai iya
tantance murna ne ko damuwa. Cike da gamsuwa da farin ciki Dady ya ce.

"Nagode Sadiq, Allah ya saka maka da alkhairi da gidan Aljanna, yanzu sai kaje ka zanta da
Iyayenka ka turo su, ina ganin ba zamu d'auki lokaci ba dan ba wani bikin kud'i za muyi ba, ina
son Husna ta cigaba da karatu a d'akinta"

"Ameen Dady, nima nagode Allah ya k'ara girma, Insha Allah zan sanar da Iyayena, duk yanda
muka yi dasu zan sanar maka, kuma maganar karatun Husna zata cigaba da yi Insha Allah."

"Nagode Sadiq, banda bakin gode maka sai dai in ce Allah yasa ka gama da gidan duniya
lafiya"

Ya amsa da Ameen tare da mik'ewa su ka yiwa juna sai da safe sannan ya wuce gida.

Cike da farin ciki Dady ya wuce d'akinsa, ya samu Husna har ta yi barci ya shiga ya watsa ruwa
kana ya gabatar da Sallan Nafila, sannan ya kwanta cike da farin ciki.

****** ******

*Washe gari*

Da misalin k'arfe goma na safe, Husna ce zaune a falo tana ta danna wayar da Sadiq ya bata a
matsayin gift, wanda tun dare ta sanyata a chargy ta yi full, yau fuskarta kamar gonar auduga,
d'auke yake da murmushi wanda har hak'oranta na fitowa, number Khadija take dannawa a
wayar wanda jiya ta amsa a gunta, bugu biyu ta d'auka cike da murna Husna ta ce.
"Khadija, Husnah ce ke magana"

A d'ayan b'agaren ta ce.

"Laaa, wannan ne number Dady d'in?"

"Hmmm ba ita bace, wannan wayata ce"

Nan ta shiga bata labarin abin da ya faru jiya, Khadija cike da murna ta ce.

"Wallahi na taya ki murna gaskiya, Uncle d'inki yana ji dake"

Nan dai suka yi ta hira, daga bisani Khadija ta kuma cewa.

"Kin san kuwa yau zamu wuce Kaduna tare da yaya Sadiq, Abbana ya kira shi zai kaimu"

"Iyen ba, ashe zaku sha soyayya a hanya"

"Hhhh, ban son sharri fa, ki mana Addu'a kawai"

"To Allah ya kaiku lafiya"

"Ameen, nagode muna isa zan kira ki"

"To sh ikenan"

Nan su ka yi sallama suka aje kan wayar.

*
Sadiq ya wuce gidan yaya Ismail, nan ya yi breakfast kana ya d'auki su Anty Amina suka wuce
Kaduna.


*********

*KADUNA*

Bayan sun isa, gida ya had'e da dangi kamar dama su ake jira, nan duk suka gaisa Sadiq ya
wuce part d'in Anty Zainab dan bai ganta a falo ba, ilai kuwa ya sameta ta idar da sallar Azahar,
nan ya zauna suka gaisa suka d'anyi hira kana ya wuce d'akinsa dan ya watsa ruwa tare da
gabatar da sallar azahar wanda ya riskesu a hanya basu tsaya yi ba.

Da dare Sadiq ya samu Amminsa a d'aki tana karanta wani littafi na Addini, zama ya yi a k'asa
ya gaisheta ta amsa, nan dai ya yi shuru bai kuma magana ba, can dai Ammi da ta ga
yanayinsa akwai magana a bakinsa, sai ta ajiye littafin ta mai da hankalinta gare shi ta ce.

"Da fatan lafiya ko?"

Ya gyara zamansa ya sunkuyar da kai k'asa ya ce.

"Ummm dama wani magana nazo mu yi a kan yarinyar da dana ke nema?"

Cike da murmushi a fuskar ta ce.

"Au khadija ko?"

Nan ya kuma duk'ar da kai ya ce.

"A'a, ba ita bace, wannan a Kano take kuma mak'ota muke, mahaifinta ya nima dana tura
magabata na, domin a fara maganar aure, wannan shekaran ta kammala jarabarta na waec, to
shi ne mahaifinta ya ce na turo, bayan anyi auren sai ta cigaba da karatu"

Nan da nan fuskar Ammi ya sauya, cike da b'acin rai ta ce.

"Wato so kake ka watsa mana k'asa a ido ko? ita kuma zancen Khadija mu yi yaya da shi?
wanda kasan iyayenka sun gama magana akai"

D'agowa ya yi cike da mamaki a fuskarsa.

"Ammi yaushe akai haka? ni fa sam bance ina son Khajija ba, ni ban san ma da wannan zancen

ba"

"Eh ai dole ka ce haka saboda ka zama mara kunya, to ka bud'e kunnen ka kaji, babu wata
wanda zaka aura face Khadija kaji na gaya maka, ka koma kaje ka samu Baban yarinyar ka ce
an maka mata dan ba zaka mai damu mutanan banza ba"

Wani gumi ne ya karyowa Sadiq, bai tab'a kawo cewa zai samu matsala gun iyayensa ba.

"Ammi dan Allah ki yi hakuri, ni bana son Khadija ku barni na auri wacce nake so"

"Dalla rufe min baki ni zaka gayawa haka, ta shi ka bani wuri mutumin wofi kawai, to bari kaji
karka yarda Abbanka yasan da wannan maganar dan ranka zai yi nugun b'aci"

*Cakwakiya*�
[10/31, 7:57 AM] Rahma Kabir🌺: *_Page 47 ~ 48_*


Jikin Sadiq ya yi matuk'ar sanyi haka ya mik'e tare da rashin kuzari, cikin dishewar murya ya ce
mata sai da safe sannan ya fita daga d'akin, Ammi ta bisa da kallo babu alamar tausayi a
fuskarta. D'akin Anty Zainab ya nufa, idonsa ya yi ja saboda b'acin rai, ya sameta tana kallo a
TV, yanayin data ganshi zuciyarta ta shaida mata akwai matsala, zama ta gyara ta rage sautin
tv, ta kalle shi cikin natsuwa.

"Sadiq yafiya kuwa?"

Sunkuyar da kansa ya yi k'asa.

"Anty wata magana naji wai za'a aura min Khadija, Wanda ni ban san da zancen ba"

Cike da mamaki ta kalle shi.

"To dama ba soyayya kuke yi ba wasan yara ne?"

Ta k'arasa maganar da zaulaya, Sadiq ya muskuta ya gyara zamansa.

"Wallahi Anty ko maganar kirki banyi da yarinyar nan, sam jinina bai had'u na nata ba, ita ce dai
take ta haukarta"

"Tafd'i jam, mu da har mun fara shirin biki"

Ta yi maganar tana dariya, Sadiq ya k'ara d'aure fuska.

"Anty dan Allah ki bar wannan wasan, na zo ki bani shawara ne kan wata magana"

Zainab ta gyara zamanta.

"To ina jinka"

Nan Sadiq ya shiga bata labarin maganar auren sa da Husna kamar yadda ya korowa Ammi
labari, ya d'aura da yadda suka kwashe da Ammi, ya k'arasa maganar kwalla sun taru masa a
ido kamar zasu zubo, jikin Anty Zainab taji ya yi sanyi saboda tunawa da ta yi da soyayyarta da
Khalil, ta san so tsartse ne mai zuwan bazata, kuma mai wahalan sha'ani, a yadda ta d'auka
Sadiq na mugun son yarinyar ne sosai, ta gyara murya.

"Sadiq ka yi hakuri, shawaran da zan baka ba lallai ta yi maka dad'i ba, ka daure ka yiwa
mahaifiyarka biyayya domin hakan zai maka amfani nan gaba, duk abin da aka ce iyaye tofa an
gaba komai, ja dasu masifa ce, kaje ka dage da addu'a da niman zab'in Allah, insha Allah zaka
samu mafita, amma duk da haka zanje na samu Anty Jiddan muyi magana akai tunda baka son
Khadija, sai a aura maka wacce kake so, ana yiwa mace auren dole ta zauna amma baga
namiji ba, dan haka ka kwantar da hankalinka Insha Allah komai zai yi dai-dai, karma ka yi
gaggawan gayawa mahaifin yarinyan zancen ka fasa, ka k'ara lokaci tukuna muga hukuncin da
Allah zai yanke"

"To shi kenan Anty nagode sosai, har na d'an ji natsuwa kad'an"

Khadija ce tsaye k'ofar d'akin Anty Zainab wacce ta daskare tun shigar Sadiq ciki. Tunda ta
hongoshi ya shiga, da saurinta ta k'araso dan ta cimmasa a d'akin sai kawai ta tsinkayi bayanin
Sadiq, nan ta yi kasake tana sauraron maganar da suke yi, hawaye ya gama wanke mata fuska,
zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Motsin da taji ne kamar za a fito yasa ta yi sauri ta shige
cikin kicin dake falo ta goge fuskarta, ta tsaya na mintuna. Sadiq ya yiwa Anty Zainab sai da
safe sannan ya wuce d'akinsa cike da tunani barkatai.

Khadija na fitowa ta wuce d'akin Anty Jidda ta same su a falo zaune da Abban Sadiq, suna
zaune da alama hira suke yi, ganinta suka yi tsalam a firgice ta fad'a jikin Ammi ta sanya kuka
mai tsuma zuciya, hankinsu ya yi matuk'ar tashi nan Ammi ta fara tambayar ta.

"Khadija lafiya, me aka miki?"

Cikin matsanan cin kuka ta soma magana.

"Ammi Yaya Sadiq ya ce baya sona ba zai aureni ba, na shiga uku Ammi ki taimaka karya rabu
dani"

Cike da mamaki Ammi ta ce.
"Yaushe kuka yi hakan da shi?"

"Yanzu naji yana gayawa Antynmu a d'aki, wai har tana cewa ba za a ba shi ni ba tunda bai
sona"

Nan dai ta yi ta zuba musu wauta da k'uruciya.
A fusace Abba ya mik'e ya fice, bai zame ko ina ba sai d'akin Anty Zainab, yana huci ya soma
masifa.

"Wato saboda ke kin isa, kin iya bijirewa iyayenki shi ne zaki goyi bayan Sadiq ya bujire mana,
kina so ki d'aurashi bisa mugun halinki da kika yi a baya ko?"

Cike da tashin hankali Anty Zainab ta mik'e.

"Yaya Aliyu lafiya? meya faruwa?"

Hannu yasa ya wanketa da mari ta dafe kuncinta, bai kuma cewa komai ba ya fice daga d'akin a
fusace. Falo ya isa ya shiga kwalawa Sadiq kira kamar saukan aradu, cikin kankanin lokaci duk
mutanan gidan suka fito a gigice, suna tambayar lafiya, Baffa da Umma, Ammi tare da Khadija
duk sun bayyana a falon, haka ita ma Anty Amina da suke kira da Mami ta fito a sittin daga part
d'inta duk tunanin ta ko wani abu ne ya faru, Sadiq shima a sukwane ya k'araso falon domin
kiran ya yi matukar tsorata shi, tunaninsa ko wanin babban matsala ne ya auku, ganin kowa a
tsaye sunyi cirko-cirko, hakan yasa Sadiq ya samu d'an nutsuwa sai ya k'arasa wurin Abbansa
ya ce.

"Abba gani"

Saukar mari yaji a fuskarsa wanda Abban ya mare shi yana cewa.

"Wallahi baka isa ka raba mana zumuncin mu ba, ka yi kad'an karya kake, mu kake niman
watsawa k'asa a ido"

"Wai lafiya me yake faruwa ne?"

Cewar Umma, Baffa shima ya ce.

"Aliyu wai lafiya kuwa?"

Sai ya yi musu umarni da duk kowa ya zauna, duk suka samu guri suka zauna, Baffa ya kai
dubansa ga yaya Aliyu.

"To yanzu sai ku gaya mana abin da ke faruwa"

Ammi ta soma bayanin abin da Sadiq ya gaya mata d'azun, ta d'aura da cewa.

"Sai da naja masa kunne na gargad'e shi, domin munyi ni da shi mun rufe magana, ashe hakan
bai masa ba shi ne yaje ya samu Zainab ya gaya mata, ashe ita kuma Khadija ta jisu, shi ne ta
same mu muna zaune ta isa da kuka take gaya mana, kuma wallahi na yi niyyar ko shi yaya
Aliyu ba zai ji wannan maganar ba domin mun rufeta, ashe shi ba haka bane a gunsa"
Anty Zainab ce ta fito idonta sunyi jajir saboda tsabar kuka, wuri ta samu ta zauna ta koro
bayanin yanda suka yi da Sadiq, ta d'aura da cewa.

"Hak'ik'a nasan ina da tabo a zuciyarku, tabbas na yi ganganci dana yi k'ok'arin shiga maganar,
insha Allah daga yau ba zan sake cewa komai ba akai, iya ka in ce Allah ya sanya Alkhairi,
insha Allah ba zan zama silar rabuwar dangi na ba"

Ta k'arasa maganar tana kuka. Cikin fusata yaya Aliyu ya ce.

"Ai gwara ki janye bakinki daga cikin maganar, domin kina da record wanda bamu fatan sake
samun irinsa"

Cikin b'acin rai Umma ta ce.

"Aliyu lafiyarka kuwa? k'anuwarka kake gayawa haka, wannan maganar bata wuce ba, meyasa
zaka mai do hannun agogo baya, sannan ka manta a gaban yara kake fadar wannan maganan,
haba in hankali ya gushe hankali ke nemo shi"

Sadiq ji ya yi duniyar ta yi masa zafi, damuwa ya gama baibaye zuciyansa, sun sanya shi cikin
rud'ani akan maganarsu, hawaye yaji yana zuba masa, ya kasa furta komai. Anty Zainab cikin
kuka mai tsuma zuciya ta mik'e ta isa d'akinta, hak'ik'a yau yaya Aliyu ya tado mata da tsohon
mikinta, tana cewa cikin kuka.
"Yau ga rashin bin iyaye abin da ya jawo min cin fuska da wukalanci, hakaki na tafka kuskure,
ko yaushe zasu gane ba laifi na ba, wannan rubutaccen kaddara ce wanda ban isa na goge shi
ba"

Sai ta fada gadonta tana rusa kuka mai tsuma zuciya.

A falo, Mami ta mik'e cikin fushi ta jawo Khadija, mari lafiyayye ta zuba mata guda biyu ta kuma
rufeta da duka. Ammi ce cikin fushi ta kwaceta tana cewa.

"Meye haka kuma Ameena? ya ana k'ok'arin gyara ke kuka kina hukunci?"

"Haba Anty Jidda wannan yarinyar duk ita ce musabbabin wannan tashin hankalin, a cikin daren
nan ta hargitsa mana gida, ina so sai ta gaya min in da ta koyo had'a munafinci tunda ban koyar
da ita haka ba"

Umma ne ta taso ta ce.

"Aminatu karki sake dukanta, in da ba ayi hakan ba tayaya zamu san halin da ake ciki, ba duka
ya kamata ki yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login