Showing 12001 words to 15000 words out of 81944 words

Chapter 5 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2380


cikin fad'a.

"Malam lafiya meye haka?"

"Kalau, na hango ki ne nace bari na zo mu gaisa, ya hutu?"

"Ban sani ba"

Ta ce a tsiwace ta cigaba da tafiya harta isa wajen wani mai sai da kayan fruit, ta ba shi kud'inta
ya yanka mata kankana, ya mika mata ledan da sauri Khalil ya karb'e kan ta amsa, cike da
masifa ta ce.

"Wai kai maye ne? to wallahi nama na d'aci gare shi, ka fita hanya ta, haba Malam sai kace
ance dole sai kamin magana"

Masifa take masa ta inda take shiga bata nan take fita ba, a takaice dai sai da mutane suka fara
taruwa suna ganin ikon Allah, shi dai mai fruit hakuri yaketa bata, Khalil saboda mamaki ya
kasa ce mata uffan sai kallonta da yake yi, ta gama masifarta ta karb'e ledan kankanar ta yi
gaba abin ta ta barshi tsaye cike da damuwa. Cikin sanyin jiki yabi bayanta har suka shiga
makaranta, d'akinta ta wuce amma bai daina bin bayanta ba, tana gab da isa d'akinta ta juyo
cike da matsananciyar damuwa.

"Yau ka tabbatar min da kai maye ne to nafi k'arfin ka"

Ta cigaba da tafiya, cike da damuwa ya ce.

"Zainab"

"Karna sake jin sunana a bakin ka"

Ta ce cikin bacin rai, ya tsaya yana kallonta.

"Haba Zainab yanzu na cancanci wulakanci a gurinki? me na yi miki ne haka? rabon da mu
had'u kimanin wata guda kenan, wallahi hukuncin da kika d'auka akan na daina miki magana ba
zan iya d'auka ba"

Zainab ta yi saki ta cigaba da tafiya, da sauri ya kamo hijab d'inta, cikin k'unan zuciya ta juyo ta
wanke shi da mari guda daya mai kyau, nan take hankalin mutane gurinsu, da sauri Khalil ya
sake mata hijab d'in, ya zaro ido yana kallonta cike da mamaki.

Zainab taji zuciyar ya yi mata nauyi numfashinta yana fita da kyar sakoman hukuncin marin da
ta yi masa, hankalinta ya yi matukar tashi bata san sanda ta fashe da kuka ba, ta ruga zuwa
d'akinta da gudu ta bude ta shige, Khalil ya shiga kallon yanayin data shiga tare da rik'e
k'uncinsa, ganin ta wuce yasa mutanen da suka taru suka fara janye jiki, wasu na tausaya masa
wasu kuma nacewa Allah ya k'ara.

Nuhu ne ya karaso gurin Khalil ya ganshi a cikin wannan yanayin ya ce.

"Khalil lafiya naga jama'a sun tasaka a gaba suna kallonka?"

Hawaye ne ya gangaro wa Khalil a kuncinsa ya girgiza kai, ganin haka sai hankalin Nuhu ya
tashi, ya kama hannunsa ya ja har wajen motarsa ya bude tare da zaunar da shi kusa da
mazaunin driver sannan shima ya zagayo ya shiga tare da tada motar suka bar makaranta.

Tana shiga d'akinta ta fad'a kan gado kuka ta yi mai isarta, wayarta taji yana k'ara alamar kira
ya shigo sai ta duba ta ga Anty Jidda ce, da sauri ta dai-dai ta natsuwarta ta share hawayenta
ta d'aga kiran, bayan sun gaisa Anty Jidda ta ce.

"Zee yana ji muryanki kamar kina cikin damuwa?"

Aiko kamar Anty Jidda ta zugata ta fashe da wani sabon kuka, cikin lallashi da tausasa murya
Anty Jidda ta rika bata magana, har ta samu ta daina kukan sai ajiyar zuciya, nan ta bata
labarin abin da ya faru tsakanin ta da Khalil d'azun. Anty Jidda ta ce.

"Haba Zainab me ya yi zafi da zaki mare shi, nifa dana ce ki yi nesa da shi ba ina nufin ki yi
masa wulakaci bane, ko ki yi masa rashin d'a'a, irinsu fa da lalama ake rabu dasu, nuna fushi ko
masifa ba shi ne zai sa ki samu nasara ba, dole sai kin danne zuciyarki, haba Zainab ki rika aiki
da hankali mana, inda ace wani ne ya bani labarin nan sai na k'aryata saboda ba halinki bane"
Zainab ta saki ajiyar zuciya mai nauyi ta ce cikin rawar murya.

"Insha Allah Anty hakan ba zai sake faruwa ba"

"Yauwa Zee ki yi k'ok'ari ki ba shi hakuri dan ku rabu lafiya dan Allah, kin ji autar Umma"

Zainab ta yi guntun murmushi.

"To Anty zan yi yadda kike, nagode"

Haka dai Anty Jidda ta cigaba da bata magana har taji zuciyarta ta yi mata sanyi, daga bisani
suka yi sallama.

*Rahma ce*
[10/17, 8:17 AM] Rahma Kabir🌺: *KAƊAICI*

© *Rahma Kabir*

*Wattpad:*@rahmakabir


*_Page 11 ~ 12_*

*Da gari ya waye*
Zainab ta yi shirin zuwa class haka nan taji bata son fita saboda abin da ta yiwa Khalil jiya tana
jin kunyar had'uwa da shi, bayan ta gama ta fito rike da littafanta, waige-waige take yi kamar
mai niman wani abu, jikin ta a sab'ule take tafiya duk sai taji ranta ya yi mata ba dad'i, yau ne
rana ta farko da Khalil bai rakata zuwa class ba, iska taji yana busota da sauri ta kara yin
waige-waige jikinta yana gaya mata Khalil yana kusa da ita sai dai bata ganshi ba. Kuma tabbas
yana nesa da ita tare da Nuhu bayan wata bishiya, lab'ewa ya yi yana hangenta abin tausayi,
kawai dai ya yiwa zuciyarsa alkawari zai yi nesa da ita.

Zainab haka ta yini sukuku cike da damuwa da tunanin halin da Khalil ke ciki, Addu'a take yi
Allah yasa ba abin da ta yi masa jiya bane ya sanya shi wani hali.


*****
Kimanin mako uku kenan Zainab bata sanya Khalil a idonta ba, duk wani damuwa da tashin
hankali ba wanda bata ciki, Addu'a kawai take yi da fatan Allah yasa yana cikin koshin lafiya, cin
abinci sai ta yi da gaske take iya ci, duk ta rame daka ganta zaka shaida tana cikin damuwa,
duk yamma take shiryawa ta shiga zagaye makaranta ko zata ganshi amma shuru sai dai ta
gama bulayinta ta koma d'aki taci kuka mai isar ta sannan ta yi shuru dan kanta. Kuma duk
zagayen da take yi lungu da sakon da take shiga, Khalil na biye da ita sai dai baya bari ta
ganshi. Da farko tun Nuhu na gaya masa shi take nima yana k'aryatawa har ya gasgatawa
zuciyarsa cewa tabbas shi take nima. Tausayin ta ne ya dame shi wanda yaso tuntuni ya
bayyana kansa gunta, amma Nuhu ya hanashi ya ce ya bari da sauran lokaci tukunna kan ya
bayyana gareta.

Ranar wani weekend da safe, misalin karfe 10am ta kimtsa ta karya kana ta koma ta kwanta
tana kallon tashar Arewa24, d'akinta taji a na mata knocking, da sauri ta mike tana tunanin kila
Khalil ne, tana bud'ewa taga yaya Al'amin tsaye yana aiko mata da sakon murmushi, ta koma
cikin d'akin shima yabi bayanta, kallon ta ya shiga yi da yake ba hijab a jikinta nan ya hango
ramar da ta yi, wuri ya samu ya zauna suka gaisa da d'an fara'a a fuskarta sannan suka shiga
hira na yaushe gamo, abin motsa baki ta tashi ta d'auko masa cin-cin ne da meltina da kuma
ruwan gora, ta ce.

"Yaya me zama ci na d'aura maka?"

Murmushi ya yi ya ce.

"Sha zamanki na taho mana da takeaway"

Tashi ya yi ya fita zuwa motarsa bai jimaba ya dawo rike da manyan fararen ledoji guda biyu ya
dire su a gabanta, ya komawa ya zauna.

"Haba yaya baka gajiya da d'awainiya?"

"isshh ya isa haka, ko ba komai ke k'anwata ce kinga dole ne na yi miki balle kuma nan da wani
lokaci ina sanya ran zaki zama mata ta"

Da sauri Zainab ta dago fuskarta tana kallonsa kamar mai nazari, bugun zuciyarta ne taji ya
sauya numfashinta ya fara bugawa sauri-sauri, ta mai da kanta tana lallon k'asa, nan da nan
Al'amin ya gano cewa akwai abin da ke damunta. Cikin nutsuwa ya kira sunan ta.

"Zainab me yake damunki?"

"Laa me ka gani? ba abin da ke damu na fa"

Ta ce cike da wayencewa.

"A'a my Zee ban yarda ba, kinga yanda kika rame kuwa? gwara ki sanar min in da akwai
matsala sai mune ma miki magani"


"Yaya na ce maka ba komai karatu ne kawai ya sani gaba na rame"

Ba yadda ya iya dole ya yarda amma a zuciyar sa bai gamsu da amsar ta ba. Haka suka ci
suka sha sai misalin k'arfe 4 na yamma suka yi sallama ya tafi. Khalil yana kallon su lokacin da
ta yi masa rakiya tana tafiya sai da ta yi waige-waige tana jin wani iri a ranta kamar Khalil yana
kallonta. Tana komawa d'aki ta gyara ko ina ta gabatar da sallah la'asar, ta mik'e bata cire hijab
d'inta ba ta d'auki waya da malullun d'akinta ta rufe sannan ta nufi bakin gate. Tafiya take yi a
kafa ta rasa ina zata, can bayan makarantan su ta nufa kusa da wani ciyayi, mutane na wuce
wa kad'an-kad'an ta samu wani dakali ta zauna, danne danne take yi a waya ta shiga tunani mai
zurfi, zuciyarta duk ta takura kuka ta fashe dashi mara sauti tana yi tana share hawaye, iska ne
taji yana busata sosai kasan tuwar lokacin damuna ce, hadari ya fara had'uwa. Waige-waige ta
soma yi tana k'ok'arin tashi, idon nan nata ya kod'e saboda tsabar kuka, kamar ance ta juya
bayanta sai taga mutum tsaye ya rungume hannun sa sai kallonta yake yi, ta zare ido waje,
mamaki da tsoro ne ya ziyarce ta. Khalil ya sakar mata murmushi ya zagayo kusa da ita ya
zauna yana kallon ciyayin da ke wurin, ita ma ta sunkuyar da kai kasa kamar mai nazari, sun
d'auki kusan minti goma ba su cewa junansu komai ba, ita ce ta katse shurun, cikin dashewar
murya ta soma magana

"Umm umm lafiya ka zo nan wurin?"

Ya Juyo da fuskarsa gareta ya ce.

"Kema lafiya kika zo nan?"

"To ai ni ce na rafa tambayarka, sannan kuma kaine ka sameni a nan din"

"To naji, yanzu me yasa ki kuka? sannan ma meyasa kika keb'ance ke kad'ai anan gurin, kuma
me yake damunki?"

Tambayar ya zo mata a ba zata, sai ta shiga tunanin zuci.

'Ba dai dama tun d'azu yana nan wurin ba? wato ma har kukan dana yi ya gani?'

Ya katse mata tunaninta da kiran sunanta.

"Zainab"

A hankali ta dago fuskarta tare da motsa bakinta a hankali ta amsa.

"Baki bani amsata ba amma kin yi shuru kamar kina tunani"

Ta sunkuyar da kai kasa jikinta ne ya yi mata sanyi, nan take ta tuno da irin wulak'ancin da ta yi
masa amma bai iya nuna mata ba sai ma nuna mata daya yi ya damu da halin da take ciki.
Hawaye ne taji ya wanke mata fuska ta kasa dago ido ta kalle shi, cikin rawar murya ta ce.

"Khalil, na kasance mai babban laifi a gare ka amma sam baka iya nuna min b'acin ranka ba,
saima nuna min wani kulawa na daban kake yi, a kwanakin da suka wuce ina cike da fargaban
mu sake had'uwa saboda ban san irin matakin da zaka d'auka a kaina ba, amma a yanzu na
tabbatar da ba haka kake ba, dan Allah ka yafe min, da ina ganin hukuncin dana d'auka maka
shi ne dai-dai a she babban kuskure na tafka"

Ta karashe maganar da kuka, kallonta yake yi ba kifta ido, yana gasgata nadamar da ta yi,
kuma zuciyar sa ta amshi hakan harma yake zargin ta karbi soyayyarsa cikin kankanin lokaci.
Kukan da take yi sai yaji baya masa dad'i, yayi gyaran murya.

"Haba Zainab ki yi shuru ni Khalil na yafe miki, ki kwantar da hankalinki kuma ni sam banji zafin
abin da kika yi min ba, haushin kaina naji nada kasance mai takura miki a baya, kuma wannan
dalilin ne yasa nayi nesa dake ko zan iya cire sonki a zuciyata na barki kisha iska"

Da sauri ta dago idon ta da suke fal da hawaye.

"Nesa dani da ka yi shi ne abu mafi girma da muni daya jefani cikin tashin hankali da damuwa,
dan Allah Khalil ina rokanka karka kuma nesa dani in ba haka ba wallahi zan shiga cikin wani
sabon damuwa"

Kallonta yake yi cike da mamakin kalamanta bai taba zaton zai ji irinsu sun fito daga dakinta ba,
shuru suka yi na minti biyar, hadari ne ya had'u sosai iska ya fara kad'awa sosai, mik'ewa ya yi.

"Zainab tashi mu koma cikin makaranta kinga ruwan nan ya kusa sauka"

Ta mike suka jera ba um ba um um. Har k'ofar d'akinta ya rakata ta bud'e kofa, ya ce.

"Zainab sai da safe"

Da sauri ta juyo ta kalle shi.

"Ban gane sai da safe ba, ka shigo mana"

"A'a ki barshi kawai nagode zanje gida yanzu"

"A'a ka shigo ka zauna kaga ruwan nan ya kusa sauka"

Ba yadda ya so ba dole ya shiga cikin d'akin, wannan shi ne karon farko da Khalil ya shiga
dakin Zainab, kalle-kalle ya shiga yi d'akin ya yi matuk'ar burge shi ya tsaru dai-dai gwargwado,
ga wani sanyin k'amshi mai rasha zuciya da yake bin bargonsa, bai san sanda ya yi ajiyar
zuciya ba a hankali, a kujera ya zauna a takure ya kasa sakin jikinsa, kicin ta shiga ta debo
masa abin motsa baki, kad'an yaci saboda bak'unta, TV ta kunna musu suna kallo ba wata hira
suka yi ba sai dai ko wannan su da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Ruwa ne ya tsuge kamar
da bakin kwarya, sai nepa suka d'auke wuta wayarta ta lalubo ta kunna haske, sannan ta kunne
rechargeable d'inta d'akin ya gauraye da haske. Haka suka yi shuru ba wani hira da suka iya yi
saboda rashin sabo, ruwan ne yad'an tsagaita saka makon kiran sallah magrib da ake yi,
mikewa ya yi ya ce.

"Zainab zan tabi masallaci"

"Zaka tafi ai ruwan bai tsaya ba"

"Ba damuwa ai tunda yayyafi ake yi"

"To shi kenan bari na baka lema ta"

Tashi ta yi ta d'auko masa sannan ta bud'e d'akin suka yi sallama da alkawarin in Allah ya kaimu
gobe zai kawo mata leman. A wannan ranar daga Zainab har Khalil sunyi barcin farin ciki, ko
wannansu da tunanin juna suka kwana.

Tun daga wannan rana Khalil da Zainab suka shak'u sosai, duk inda zasu a tare sannan suna
gunadar da soyayya a tsaftace, Khalil shike yiwa Zainab cefane ta girka musu abinci kullun.
D'akinta ya zamar masa wajen zuwansa, hatta Nuhu abokinsa shi ma wataran da shi suke hira
daga nan shima ya cika tumbinsa.

*****
Sun fara shirye-shiryen exam na last semester, sun mai da hankali wajen karatunsu, tare da
gudanar da soyayya mai cike da kauna da yarda, duk sunyi k'iba sunyi kyau hankalin su a
kwance.

Wata rana da misalin sha d'aya na safe, Khalil suna d'akin Zainab shida Nuhu suna karin safe,
ita kuma tana gefe sunata hira, sai suka ji ana yin nocking k'ofa, cikin sauri Khalil ya mik'e
danya je ya bud'e d'akin, koda ya bude abin da ya gani ba k'aramin kad'a masa hanjin cikinsa
ya yi ba, sai ya fuske ya dawo cikin d'akin, mai nocking k'ofar ya biyo bayansa cike da mamaki.
Khalil ya zauna, Zainab na ganin bakon daya shigo hankalinta ya tashi, mik'ewa ta yi cikin
damuwa da fargaba, murmushin tak'aici ya yi mata ganin yanda ta rikice lokaci d'aya, cikin
rawar murya ta ce

"Yaya Al'amin sannu da zuwa"

Ya dakatar da ita da hannunsa.

"Bana buk'atar gaisuwarki, Alhamdulillah yau abin da kike yi a boye ya bayyana, haba biri ya yi
kama da mutum shiyasa kike wulak'anta ni, ashe kin samu sabon farka ne, kin bani mamaki
Zainab duk iya tarbiyya da su baffa suka baki a she a banza suka yi kina nan kina ai kata tsiya
son ranki"
Cikin kuka da takaicin kalamansa ta ce.

"Ya isa Yaya, maganganun ka sunyi min yawa yana da kyau kafin ka yanke min hukunci ka ji ta
bakina tukunna"

Cikin fad'a da d'aga murya ya ce.

"Me zan tsaya na saurara bayan abin da idona ya gane min ya isheni amsa"

"Da kata Malam yana da kyau ka sauraremu kafin ka yanke mana hukunci"

Cewar Khalil cikin saga murya.

"Kai ban sa da kai ba kaja bakin ka ka min shuru mutumin banza kawai, kai in k'anwarka ce
kazo ka samu a haka zaka bari ne, dan haka kafin na yi kasa-kasa daku maza Ku fice a cikin
d'akin nan mutanan banza kawai"

Cikin kunan rai Khalil ya ce.

"Sai dai kaine mutumin banza"

Ya karasa yana huci idanunsa sunyi jawur saboda bacin rai, Yaya Al'amin kansa ya yi yana son
tsakumo Khalil, da sauri Nuhu ya shiga tsakaninsu ya ce.

"Dan Allah ku yi hakuri kar kuyi fad'a, munji munyi laifi ka yi hakuri"

Ya juya wurin Khalil.

"Kai kuma mu tafi ban son na k'ara jin kayi magana a nan"

Khalil ya yi murmushin yake.

"Ba zan bar wajen nan ba sai ya san matsayina a gunta"

"Matsayin ka na banza kai waye? Wallahi saina sa an d'aureka da duk abin da kake tak'ama
dashi"

Cewar Al'amin. Zainab in banda kuka babu abin da take yi, ta shiga rud'ani.

"Ni ba kowa bane amma fa ka sani baka isa ka sanya a d'aure ni ba dan kai ba kowa bane face
Mara tunani, sannan ka sani Zainab tawa ce wallahi babu wanda ya isa ya shiga tsakani na da
ita sai Allah kad'ai"

Cewar Khalil yana huci. yana gama fad'an haka ya yi waje cike da b'acin rai. Al'amin ya bishi da
kallon mamaki har ya fice, tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login