Showing 57001 words to 60000 words out of 81944 words

Chapter 20 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2397

ba Addu'a da nasiha zaki yi mata, tunda Khadija ta mallaki hankalinta, ta wuce
duka"

Nan Baffa ya yi umarni da duk su zauna. Ta b'angaren Sadiq kuwa ya ji dad'in abin da Mami ta
yiwa Khadija domin ta cancanci hukunci, Kuma shima yana nan ya yi mata tanadin hukunci kan
munafircin da ta had'a. Baffa ya ce su Sadiq su basu wuri, haka ya mik'e jiki ba kwari ya wuce
d'akinsa, Khadija wacce hawaye keta malala a fuskarta ita ma ta mik'e ta wuce jiki ba kwari ta
nufi part d'in Ammi, domin yau ba zata iya kwana d'akin Anty Zainab ba, dan ita ce ta had'a
wannan rigima, dana sani ne ya cika mata zuciya tana fad'an.

"in da nasan haka zai faru da na rik'e maganar a zuciyata na yi hakuri"

Sadiq yana isa d'aki ya duba agogon dake manne jikin bagon d'akin, yaga k'arfe tara da kwata
na dare, jakar daya tawo da shi ya d'auka tare da key d'in motarsa, fita ya yi ta baya, ya yiwa
mai gadi magana ya bud'e masa gate, ya cilla jakar a seat d'in baya, ya shiga mota kan kace
meye ya figi mota a guje, su Baffa k'ugin motarsa suka ji kan suyi yunkurin fitowa ya fice, ya
kama hangar Kano cikin wannan dare.

*To masu karatu sai mu had'u musa Sadiq a Addu'a Allah ya sauke shi lafiya*
[10/31, 7:16 PM] Rahma Kabir🌺: *_Page 49 ~ 50_*


Baffa ya d'auki wayarsa ya danna number Sadiq bugu biyu ya d'auka, kan ya ce wani abu Baffa
ya soma magana.

"Kai Sadiq ina zaka cikin daren nan?"

"Baffa zan koma Kano ne Addu'atku nake nima sai na dawo"

Bai jira mai Baffa zai ce ba ya kashe wayar gaba d'aya ya jefata kan seat d'in dake gefensa, ya
k'arawa mota wuta.

Baffa ya cire wayar a kunne ya bita da kallo, daga bisani ya nisa tare da ajiyeta, ya kai dubansa
ga Abba Aliyu.

"Kunga irin abin da ake gudu, to Kano ya tafi cikin daren nan"

Abbansa cikin fushi ya ce.

"Yafi ruwa gudu, kuma ba zamu tab'a sauya k'udirinmu ba, aure ne ba fashi"

Ammi ji ta yi ba dad'i domin ta san Sadiq yana k'ok'arin yi musu biyayya, haka nan taji basu yi
masa adalci ba, Mami Ameena ta ce.

"Ba zai yuwu ba tunda bai son Khadija to a bar shi ya auri wacce yake so"

"Ku dakata, yanzu dai za a bi komai a hankali, sannan tunda ya nuna bai so to lallaba shi ya
kamata ayi, kuma yanzu ita Khadija karatu zata yi kunga kila sai nan da shekara biyu kan ayi
maganar auren, inya so kila lokacin sun dai-daita kansu, kuma ina da tabbacin Sadiqu ba zai
bijire da auren Khadija ba dan yaro ne mai biyayya, dan haka magana ta wuce, Addu'a za mu
bisu da shi, Allah ya tabbatar da abin da yake Alkhairi"

Cewar Baffa, duk suka amsa da Ameen. Baffa ya kai dubansa ga yaya Aliyu.

"kai Aliyu ka ta shi kaje ka bawa 'yar uwarka Zainab hakuri dan baka kyauta ba, magana ya
k'are bana so a kuma tadata, zaku iya tafiya"

Haka kowanne ya wuce part d'insa cike da damuwa, Abba Aliyu ya wuce d'akin Zainab ya same
ta gefen gado ta rafka uban tagumi, zama ya yi a kujera nesa da ita ya soma bata hakuri da
lallashi, cikin k'ank'anin lokaci ta sauko suka shirya, harda yi mata alkawarin zai canza mata
mota, da haka ne yasa Anty Zainab ta soma murmushi nan ya yi mata sallama ya wuce cike da
dana sanin abin da ya yi mata, sai yanzu da hankalinsa ya dawo jikinsa ne yaji bai kyauta mata
ba. A can kasan zuciyar Zainab kuka take yi na kuskuren data aikata, wanda ya zama har
yanzu ana goranta mata.

******
Sadiq gudu yake yi kamar zai tashi sama, da yake cikin dare ne ba motoci sai tsiraru, zuciyarsa
ta yi masa k'unci tare da tunani barkatai, mafita kawai yake nima domin dole ya hakura da
auren Husna in dai yana son zaman lafiyan familynsa, da wannan tunani ya isa garin Kano da
misalin k'arfe sha daya da rabi na dare, gidan su 'Yasir ya nufa, wayarsa ya d'auka ya kunna
tare da danna number Yasir. Yasir yana barci sai yaji kiran wayarsa kamar daga sama, ya
mirgina ya d'auki wayar ganin mai kiransa ne yasa ya murza idon don ya tabbatar da ba mafarki
bane, saura k'iris kiran ya tsinke ya yi sauri ya d'auka tare da kara shi a kunensa ya ce.

"Hello! Sadiq ya a ka yi ne?"

Cikin dishewar murya Sadiq ya ce

"Ka fito ka yiwa mai gadinku magana ya bud'e min gate gani a k'ofar gidanku"

Cikin sauri ya mik'e tare da cewa ok, kana suka tsinke wayar. Yasir ya fito ya samu mai gadi ya
yi masa magana cikin minti biyar Sadiq ya shigo ya yi parking, jakan kayansa ya d'auka sai
waya, sannan ya kulle motan ya kalli in da Yasir ya tsaya.

"muje ko"

Shi dai Yasir mamaki ya hana shi magana sai kawai ya yi gaba Sadiq na binsa a baya har suka
isa cikin d'akinsa, kana ya rufe k'ofa. Direct ba yi Sadiq ya nufa ya watsa ruwa kana ya fito
d'aure da tawul, Yasir ya mik'e ya ciro masa sabuwan jallabiya wanda bai taba amfani da shi ba
ya mik'awa Sadiq, ya amsa ya zira tare da ya kammala shirin barci, ya fad'a kan k'atuwar katifar
da aka kwantar a k'asa, Sadiq ya rufe ido kamar mai barci, haushi ne ya fara kama Yasir domin
miskilancin Sadiq wani lokacin yana ba shi haushi, a k'ufule ya ce

"Malam ka zo ka kwanta, kak'i yi min bayani sai wani cin magani kake yi, wai me yake faruwa
ne? Kar dai daga Kaduna kake cikin daren nan?"

Tsaki Sadiq ya yi.

"Kai Malam ka kwanta ka yi kwanciyanka, ka barni naji da abin da ke damuna"

Shima Yasir tsaki ya saki.

"Ka cigaba da barin magana a cikin ka, wata rana sai ya kashe ka"

Sadiq bai tanka masa ba, haka suka kwanta kowa da irin abin da yake sak'awa a zuciya, har
barci ya yi baga da su.

****** ******

*Washe gari*

*Kaduna*

Gidan duk sun tashi cikin walwala kamar babu abin da ya faru, Khadija ta isa d'akin Maminta, ta
same ta zaune kan dinning tana karyawa, ta risina ta gaidata, Mami ta amsa kamar babu komai,
sai da ta kammla kana ta mik'e ta koma falo ta zauna a cushing, Khadija tabi bayanta ta samu
k'asan carpet ta zauna kanta na sunkuye ta ce.
"Mimina ki yafe min, wallahi sharrin shaid'an ne ya jani, amma ba zan k'ara ba"

Mimi ta yi ajiyar zuciya.

"Babu komai Khadija, ni dai ina k'ara jan kunnenki, ki rik'a yin gaskiya kuma kin san lab'e babu
kyau, domin halin munafukai ne, sannan ina so kije ki samu Antynku Zainab ki bata hakuri"

Nan dai ta yi ta mata fad'a da nasiha, bayan sun gama magana Mami ta ce.

"Tashi kije ki kwashe kayan dining, ki shiga kicin ki gyara min shi"

Khadija ta mik'e tare da cewa to kana ta wuce.

Khadija ta samu Anty Zainab a d'aki, nan suka gaisa sannan ta bata hakuri, Anty Zainab ta
nuna mata babu komai nan ita ma ta yi mata nasiha, tare da nuna mata illar nunuwa namiji so
irin haka, tabi komai a hankali in Sadiq mijinta ne zata aure shi, nan dai ta yi ta mata bayani har
Khadija ta saki jiki suka cigaba da hira kamar wani abu bai faru ba. Anty Zainab kenan tana da
sanyin hali ba tada gaba ko tsananta fushi, kowa nata ne, hakan ne yasa ta saba da yaran 'yan
uwanta domin tana sakin musu fuska sosai, sannan babu raini tsakaninsu.

***** *****

*Kano*

Sadiq bai farka barci ba tunda ya koma bayan sallah asubahi sai goma na safe ya tashi, Yasir
na zaune bisa kujera yana aiki a computer, Sadiq ya mik'e ya shiga bayi, wanka ya yi ya fito ya
shirya cikin riga da wando k'ananun kaya, ya yi kyau sai dai fuskarsa babu walwala, har wani
d'an rama ya yi, ya samu gefen Yasir ya zauna, shuru ya yi Yasir ya waigo suka had'a ido sai ya
kauda shurun da cewa.

"Alhaji ina kwana? tunda naga azumin magana kake yi"

Sadiq ya wurga masa harara ya amsa a dak'ile.

"Lafiya"

"To ga breakfast d'inka can dan ni na ci nawa, Momy ta aiko mana da shi dan na sanar mata da
zuwanka, in ka kammala sai muje mu gaisheta"

Ok kawai ya ce masa ya matsa wurin daninng, ya bud'e kulan soyayyat irish ne da plantain sai
kuma kunun gyada, da yake yana son kunun gyada, sai ya zuba a cup ya soma sha yana cin
plantain, bai ci irish ba saboda bai dame shi ba. Bayan ya gama suka isa falon Momyn Yasir,
suka gaisa kana suka koma d'aki, Momyn Yasir ta yi murna da ganin Sadiq domin da ganin sa
ta shaida natsuwarsa, hakan zai sa Yasir ya natsu ya rabu da tarkacen abokansa danta sanshi
da jaye-jaye, tunda yake bata labarin Sadiq ta ji ya kwanta mata a rai, domin taga sauyin wasu
halayyansa akan yawo da kuma niman matan da yake yi, hakan ya tabbatar mata Abota da
Sadiq Alkhairi ne ga Yasir.

A d'akin Yasir kuwa haka suka zauna jugum-jugum, Sadiq ba yi da niyyar komawa gida. Da
yake ranar lahadi ne, Sadiq ya koma ya kwanta abinsa sallah kad'ai yake tada shi.

Da dare suna zaune sun gama cin tuwon da Momy ta aiko musu da shi, suna kallon wani series
film, Sadiq ya ce.

"Yasir ina so zamu yi magana"

Cike da mamaki Yasir ya juyo ya kalle shi.

"Na'am magana kake yi ne?"

"Van sani ba"

Sadiq ya mai da masa da martani cike da jin haushi. Yasir ya ce.

"Mai da wuk'ar, dan naga tun jiya kake fusge-fusge"

Sadiq ya yi murumushi gefen baki.

"Malam Bana son sharri, in zaka rage volume ka rage mu yi magana, in kuma baka shirya ba
sai ka sanar min"

Yasir ya kwanshe da dariya.

"Ni ko na shirya, dan kunnena har sun fara min k'aik'ayi"

Murmushi Sadiq ya yi domin inya biyewa Yasir sai sun d'auki lokaci yana zuba masa shirme,
shurun da yaji Sadiq ya yi shi ne yasa shi rage volume d'in TV kana ya gyara zama ya ce

"Ina sauraronka"

"Yau zan baka labari na kamar yanda kake ta son na gaya maka a baya, inna gama baka
labarin, daga k'arshe sai ka bani shawara dan in samu mafita"

Nan Yasir ya natsu ya aje wasa tare da bama Sadiq hankalinsa. Sadiq ya shiga ba shi
labarinsa, da labarin farkon had'uwansa da Husna, da yadda mahaifinta ya ba shi ita ya aura,
sannan da irin rigimar da suka kwasa jiya a gidansu har ya zuwa dawowansa Kano. Ya nisa tare
da hura iska mai zafi da bakinsa, damuwa fal a fuskansa, hawaye sun cika masa ido wanda
kad'an yake jira ya sauko, jikin Yasir ya yi sanyi ya kuma jinjina lamarin ya ce.

"Yanzu kai ka amince da ka fasa auren Husna bayan da kai ta dace, ta ginu akan tarbiyyarka ka
zame mata komai, wallahi da da farko na d'auka 'yar uwarka ce, sai a ranar da mahaifinta ya
nuna baima sanka ba, wannan ya bani cewa akwai wani b'oyayyen Al'amari a tare da kai da
Husna"

Sadiq ya nisa.

"Hakane, ga shi kuma yau na warware maka komai, kasan waye ni, dan haka sai ka bani
shawara"

*wani shawara Yasir zai ba ma Sadiq?*
[11/1, 8:12 AM] Rahma Kabir🌺: *_Page 51 ~ 52_*


Yasir ya nisa ya ce.

"Ni ina ganin Sadiq kar ka yi saurin yanke hukunci, sai mu yi Addu'a, mu d'an bada lokaci, sai
ka koma wurin iyayenka da maganar sai mu ji me zasu ce"

"Hmmm Yasir kenan, baka san Familyna ba akwai naci da kafiya, ina ganin zanyi musu
biyayya, dama ba son Husna nake yi ba, tausayinta nake yi da kuma ganin girman Dadynta,
kawai zan masa bayanin cewa a gidanmu an bani mata"

Yasir ya yi murmushi ya ce.

"Kai yanzu Sadiq har zuciyanka baka jin son Husna? ni fa ban yarda cewa tausayinta ne kawai
yasa zaka aurenta ba"

"Yasir ka yarda dani, banda tausayi babu abin da nake ji game da ita"

"Hmmm"

Yasir ne ya yi ajiyar zuciya a ransa ya ce.

'Wannan Guy d'in akwai shegen zurfin ciki, amma na san ta in da zan bida shi'

Yasir ya gyara zama ya ce.

"Kasan meye Sadiq? ina ganin tunda ni ina son Husna, dan tun ranar dana ganta naji ta kwanta
min arai me zai hana muje wurin Dady ka nuna ni a matsayin wanda ka barmawa ya auri
Husna"

Wani kallo Sadiq ya yi masa mai cike da tuhuma.

"Ba kada natsuwa, sannan ban yarda da kai ba, saboda kana da son mata, ba lallai na gane da
gaske kake son Husna ba, dan haka bata dace da kai ba. Koda zan bada Husna sai wanda na
tabbatar da halinsa tare da natsuwarsa kana na amince, Malam ka canza shawara wannan bata
yi ba"

Murmushi Yasir ya yi a ransa.

'D'an rainin wayo, kana son yarinya kana wani dojewa'

A fili kuma ya ce.

"Allah abokina dagaske nake, zaka je wurin Dady ka nuna masa iyayenka sun amince, ni kuma
zan je na samu Kawuna Sulaiman na gaya masa sai yaje ya nima min aurenta matsayin kai ne,
in yaso sai kawun yama Dady bayanin ni ya nimawa aure ba kai ba, na san Dady ba zai musa
ba illa kawai ya kira ka dan yaji dagaske haka ne, kai kuma sai ka nuna masa ka hakura ka bar
mini saboda ni na nuna ina son ta kuma ka yaba da halina, kaga sai a d'aura dani"

Shuru Sadiq ya yi yana nazarin maganan Yasir, bugun zuciyarsa ya k'aru zufa ne ya keto masa
duk sanyin dake cikin d'akin, amma bai hana shi zufa ba, Yasir ya ce.

"Kayi shuru? kafa tuna ka ce zaka cewa Dady iyayenka sun ki amincewa, to da kace masa haka
gwara muyi hakan, kaga Dady ba zai ce ka watsa masa k'asa a ido ba, kuma zai gane bawai
iyayenka bane suka k'i auren ba"

Sadiq ya yi ajiyar zuciya ya ce.

"Hakane, ka kawo shawara mai kyau"

Yasir ya yi murmushin jin dad'i ya ce.

"To ka amince kenan?"

"Eh, na amince, amma da sharad'in zaka rik'e Husna amana"

"Abokina karka samu damuwa, wallahi ina son Husna kuma zan rik'e maka ita amana, kafa san
halina fa"

Wani irin damuwa ne ya ziyarci Sadiq, zuciyarsa na gargad'insa, amma babu yadda zai yi domin
hakan ne mafita, Yasir ya karanci halin da Abokinsa ya shiga amma sai ya basar kamar bai kula
ba, nan suka cigaba da tattaunawa daga bisani suka yi shirin barci suka kwanta.

********

*WAYE YASIR?*

_*Yasir Muhammad Auwal*_
D'a ne ga Alh. Auwal, wanda Allah ya yiwa rasuwa tun Yasir yana secondary school, Alh. Auwal

d'an kasuwa ne, yana saida atamfofi da yadika. Asalinsu mutanan garin Kano ne, mahaifiyarsa
Haj. Aisha, yaransu uku duk maza, Yasir ne babba sai Aliyu mai bi masa sai autansu Umar
Faruq, tunda mahaifinsu ya rasu Abokan Baban suka rik'e Amanar dukiyansu, da Yasir ya girma
suka danka masa ya cigaba da business da gadonsu, sannan bayan ya gama karutunsa na
engineering anan BUK, ya gama service, sai ya samu aiki a ma'aikatar matatan man fetur, inda
a nan ne suka had'u da Sadiq suka k'ulla abota, tun Sadiq na ja baya da shi har ya saki jiki suka
zama abokai sosai. Yasir mutum ne mai barkwanci da son mutane, matsala d'aya gare shi son
mata, da yaga mace zai nuna yana so hakan yasa Sadiq yake masa fad'a, wanda a yanzu ya
soma natsuwa, sannan ya rabu da abokansa na shashanci, ya sakesu ya kama Sadiq shi
kad'ai, sai sauren tsiraru da yake mutunci dasu. Yasir yana da kyau dai dai gwargwado, ya iya
wanka, wankan tarwad'a ne, yana da tsayi dai dai misali, yanada idanu sai dai bayi da tsayin
hanci sosai, V face gare shi mai dauke da baki dan dai dai. A takaice dai shima yana da nasa
kyau d'in, amma fa bai kama k'afar Sadiq ba.

_Wannan kenan._
******

Cigaban labari.

*Bayan kwana biyar*

Sadiq yana gidansu Yasir ya kasa komawa gidansa, tare suke zuwa aiki su dawo, d'an zaman
da Sadiq ya yi da Yasir ya k'ara fahimtan hayayyarsa, mutum na mai kirki da barkwanci, nan da
nan yaji ya k'ara kwanta masa yaji ya kara amincewa da ya auri Husna.

Ranar Juma'a sun dawo daga masallaci sunci abinci Sadiq ya shirya zuwa gidansa, Yasir ya ce.

"Ni kam da ka saki gidan cen ka dawo nan mu cigaba da zama tare, ni fa yanzu ka tashi a
abokina ka koma d'an uwa na kuma Aminina"

Murmushi Sadiq ya masa, dan shima kansa zai so ya cigaba da zama da Yasir, dan yana deb'e
masa kewan damuwarsa, amma ya zama dole ya koma makwancinsa, ya nisa ya ce.

"Kai mai zai hana muje kamin sati a gidana"

Yasir ba musu ya mik'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login