Showing 60001 words to 63000 words out of 81944 words
Chapter 21 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
ya shiga shirya kayansa a trolley, mamaki ne ya cika Sadiq.
"Kai baka bani amsa ba sai ka shiga had'a kaya?"
Yasir ya kwashe da dariya.
"To ai in nuna mata na amince yasa na shiga had'a kaya"
"In kuma wasa nake yi fa?"
"To saina mayar da kayan, kasan ni ba bak'on zafi bane, daga ni har kai mun saba zaman
gwauranci, gara ma ni su Momy na gidan, kai ko kwalli d'aya kamar maye"
Dariya ya ba Sadiq sosai.
"Wallahi ni ba maye bane, sabo ne kawai da rayuwan *KAD'AICI*, amma d'an zaman da na yi
nan yasa ina son ka zauna dani a gidana"
"Kana so kana kaiwa kasuwa, to ai saina dawo mu cigaba da zama dan ni zamana na tamfarari
ne, kasan na kusa zama Ango, sai na bar maka gidanka, ka cigaba da zaman *KAD'AICI* kan
ka kawo Amaryanka Khadija take ko wa?"
Wani mugun fad'uwar gaba Sadiq yaji, nan da nan fuskansa ya sauya ba annuri, Yasir ya yi
murmushi.
"Allah ya huci zuciyan ran maza, na lura danna kawo zancen nan ne kake huci kamar kumurcin
maciji, to yi hakuri karka sareni"
Pillow dake gefen Sadiq ne ya d'auka ya bugawa Yasir ya mik'e ya ce.
"In ka gama min wulakancin, ina waje ina jiranka karka b'ata min lokaci"
"To malam ban gama shiryawa ba, zaka iya d'aukan motanka ka wuce, ni zan biyo bayanka da
tawa motan"
Sadiq ya yi kwafa.
"Zaka zo ka same ni anjima"
Sai ya fita, Yasir ya bud'e murya ya ce.
"Kar dai ka tafi ba tare da ka yiwa Momy sallama ba garin fushi"
Sadiq na jinsa ya girgiza kai ya ce.
"Yasir baka da M zan rama"
Sai ya wuce sashin Momy ya yi mata sallama, kana ya fito mai gadi ya bud'e masa gate ya fice.
Yasir ya samu Mahaifiyarsa ya yi mata bayanin komawarsa gidan Sadiq, da farko bata yarda da
zancensa ba sai da ta kira Sadiq ta tabbatar, kafin ta amince dan ta san halin kayanta.
Yasir na isa gidan Sadiq, ya cigaba da yiwa Sadiq tsiya, Sadiq banza ya yi da shi bai kula shi
ba, dole ya yi shuru dan yasan miskilancinsa ya motsa.
*Da dare*
Sadiq yaje ya samu Dady ya sanar masa da iyayensa sun amince kamar yanda Yasir ya ba shi
shawara, Dady ya yi murna sosai ya ce.
"Ya sanar musu da nan da mako biyu yana buk'atar ganinsu domin su tattauna akan maganar"
Jikin Sadiq ya yi sanyi, a k'asan zuciyarsa yana fargaban yadda Dady zai ji in Kawun Yasir da
zo da batun nimawa Yasir auren Husna, haka ya yiwa Dady sallama zuciyarsa nata sake-sake
ya wuce gida.
Yasir yaje ya yiwa Kawunsa zancen auren Husna, Kawu Sulaiman ya yi murna sosai nan ya kira
sauran dangi ya sanar musu suka yanke Juma'a Biyu mai zuwa zasu je don tsaida maganar,
nan Yasir ya d'auki kud'i masu tsoka ya bashi ya ce ya ci goro, cike da murna Kawu ya amsa,
da yake shi mutum ne mai son kud'i, nan ya masa sallama ya wuce.
****** ******
*Bayan mako guda*
Yasir ya koma gidan Kawu Suleiman shi da Sadiq, kud'i ya ba shi masu d'an yawa kan
maganar kud'in sadaki da gaisuwa da sauransu, duk yadda aka yanke sai su bayar, a nan Kawu
ya shaida Sadiq ya jinjina masa tare da yi masa godiya.
Dady ya sanar da Baba Husain maganar zuwan Iyayen Sadiq, cike da murna Baba ya yi
Addu'a, Inna ma Addu'an ta yi suka cigaba da hiran yadda abin zai kasance.
******
Yau ya kama juma'a kuma ya yi dai dai da ranar da Kawu za suje gidan Dady kan maganar
auren Husna. Da misalin k'arfe na dare iyayen Yasir su uku sun zo, suna zaune babban falon
baki, Dady yana zaune shi da Abokinsa Alhaji Ahmad suna tattaunawa, nan suka yanke sadaki
budu hamsin, dukiyar aure dubu dari, kud'in kayan sa rana budu talatin, duka kud'in dubu d'ari
da tamanin. Sunyi farin ciki sosai yadda suka amsa juna cike da mutuntawa, bayan sun gama
zantawa suka tsaida ranar Biki wata d'aya, domin Yasir ya nima alfarman kar a sanya masa biki
da nisa, kuma haka Kawunsa ya nima basu samu wani targard'a ba wajen Dady, domin shima
bai son jan lokaci. Nan suka dai-dai ta daga bisani suka ci abinci gaba d'ayansu, su Kawu sai
wajen k'arfe goma suka tafi cike da farin ciki, hak'ak'i sunyi murna da had'uwa da mutanan kirki,
haka ta bangaren Dady sunyi murna sosai, kana Dady ya raka Abokinsa mota suka yi sallama
ya wuce.
Tun daga wannan rana Dady ya fara gyara gidansa, a b'angaren gidan sa akwai wani part da
yake kulle shima ya gyara shi yaje ya samu su Baba Husain da maganar su koma gidansa
dayan bangaren, suka ki yarda, magiya da ban baki ya yita musu da kyar suka yarda zasu
koma, amma da sharad'in zai gyara musu nan yasa 'yan haya, haka ya amince da k'udurinsu.
*******
*Biki saura sati biyu*
Su Baba Husain suka tattara kayansu suka koma gidan Dady, farin ciki gun Husna kamar me,
ita batasan wainar da ake toyawa ba, ta dai ga Dady na gyara a gidan, tunda taga su Inna sun
dawo sai ta yi zaton saboda sune Dady ke gyaran gidan, can take yini wurinsu sai yamma lis
take komawa b'angarensu.
Sadiq sai rama yake yi abinci sai ya yi da gaske yake iya ci, ya rasa meke damunsa sam baya
cikin farin ciki tunda aka sanya bikin Husna da Yasir, kullun cikin zullumi yake ko Dady zai kira
shi amma yaji shuru, abin duniya ya dame shi, Yasir duk yana kallon halin da abokinsa yake
ciki, ya yi masa tambayar duniyan nan akan me yake damunsa amma yak'i gaya masa, sai dai
ya ce bakomai kawai stress ke damunsa, haka Yasir ya hak'ura ya kyale shi.
******
*Biki saura kwana goma*
Yasir yana ta shirye-shirye ba kama hannun yaro, shi ko Sadiq baya iya tab'uka komai sai ido
daya subawa Yasir, Yasir ya kammala had'a akwati da komai wanda ya kamata ya yi, hatta
kayan da zasu yi fitan biki dasu an gama d'inka sumu, jiran ranar biki kawai suke yi. Ya gyara
gidansa daya gina a hotoro, filat mai kyau guda Biyu a cikin gidan, ya gyara filat d'aya, babban
falo mai d'auke da d'aki uku, ko wanne da bayi a ciki sai kicin a falo, da wani extra toilet acikin
falon, sai wurin dinning , wanda a lokacin Dady ya tura an sanya furnitures d'in daya siya gado
biyu da kujeru, Inna da wasu 'yan uwansu harda Momy Halima sunje sunyi jere. Komai tsaf aka
rufe gidan.
Momy Halima Maman su Minal, musamman ta kira mai gyaran jiki mai suna Hajiya Kulu Shuwa,
suka je gidan Dady, d'aki aka ware wa matar wanda ta shiga gyaran Husna ciki da waje harna
tsawon mako guda. Husna ta yi kyau sai sheki fatar jikinta ke yi, ga wani sihirtaccen k'amshi da
take yi duk inda ta gilma k'amshinta sai ya bud'e wurin mai dad'in shaka, wani irin kwarjini ta
k'ara. Husna ta yi matuk'ar mamaki da wannan gyara da aka yi mata, tunanin duniyar nan ta yi
amma ta kasa gano ainahin dalilin wannan gyara da aka mata, ga shi kullun Momy Halima sai
ta zo tare da bata wasu magani masu dad'in sha, wani harda madara a ciki, ita kanta sai da taji
jikinta ya sauya, inta tamabayi Momy sai ta ce mata kawai na gyara jiki ne, kirjinta ya dad'a
cikowa gasu a tsaye, hips d'inta ya k'ara fitowa ita kanta inta duba jikinta farin ciki ne ke cikata.
********
*Biki saura kwana biyu*
Gidan Dady ya fara taruwa da dangi na kusa dana nesa, sai kai komo ake yi, musamman Momy
Halima ta tattaro kayansu suka sauke zango a gidan Dady, wani part aka ware mata tare da
nata gayyan.
Momy Habee dai ta zama har kallo domin ga dukkan alamu jikinta ya gama bata cewa aure
Dady zai yi amma yak'i gaya mata, haka dai take zancen zuci cewa in dai baya k'oreta bane
zata jure ta zauna har ta samu kansa, dan tana son mijinta kuma sai ta mallake shi, ta d'auki
d'amarar raba shi da duk wata 'ya mace dan bata yarda mijinta ya zama mijin biza ba yau yana
can gobe yana nan.
*Wai ma í ½í¸¡Momy baki da tunani. In dai aka juri zuwa rafi da tulu wataran sai ya fashe*
Husna bata fita ko ina kullun tana d'aki tare dasu Minal da Kausar sai wata 'yar uwar su Minal
Khairy, sune kawayenta da suke d'ebe mata kewa, yanzu dai Husna zuciyarta ta gama shaida
mata aure za ayi a gidansu, sai dai bata gama tantance auren waye za ayi ba, ta dai fi karkata
da kila Dady ne zai yi aure shiyasa aketa yi mata gyara dan ta fito taro da kyau.
*******
*Ana gobe d'aurin Aure*
Dady ya kira Husna zuwa part d'insa, domin tunda su Minal suka dawo gidan ta gudu part d'insu
can take kwana, bayan ta k'araso ta samu k'asan carpet ta zauna ta gaishe shi cike da
girmamawa, nan Dady ya soma magana kamar haka.
"Husnah"
Ya kira sunanta, cikin sanyin jiki ta amsa domin yadda Dady ya kirata ta san da magana a
bakinsa mai mahimmanci, ya cigaba da cewa.
"Na kira ki ne dan in shaida miki wasu magana wala Allah su yi miki dad'i ko akasin haka, amma
ina so ki natsu ki saurare ni, domin duk Uban kwarai gatan da ya kamata ya yiwa d'iyarsa kenan
in dai ta kai munzalin girma, Husna kin yi rayuwa nak'unci da KAD'AICI dalilin rashin Uwa,
hak'ik'a hakan yana damuna inna tuna, burina naso ace kiyi karatu mai zurfi kafin in kai ga
aured dake, amma na duba hakan bamai yuwuwa ba saboda ina so ki yi rayuwar freedom da jin
dad'i kamar yadda ko wasu 'ya'ya suke samu, amma na duba hakan ba zai samu ba face na yi
miki aure kema ki samu gata da kulawan da ya kamata a gidan Mijinki"
Jikin Husna ya yi sanyi nan da nan zufa ya jikata ta fara tunanin me yake shirin faruwa da ita,
burinta bai wuce ta yi karatu ba, dan soyayya bata kawoshi kusa ba balle yin aure, kiran
sunanta da Dady ya yi ne ya dawo da ita duniyan tunanin da ta shiga, a sanyaye ta amsa
wanda idonta harya kawo kwalla, ya ce.
"Ki yi hakuri Husna, kar ki yi tunanin na tauye miki rayuwa ne, a'a jin dad'i nake niman sama
miki, insha Allah gobe in Allah ya kaimu za a d'aura miki aure da Mijin dana zab'a miki, insha
Allah ba za ki yi kuka dani ba akan zab'in dana miki domin ya kasance shi ne zab'in da Allah ya
fidda miki kenan"
Wani irin kuka Husna ta b'arke da shi mai tsuma zuciya, tashin hankali ya gama baibayeta, ji ta
yi dama mutuwa ta yi da ganin irin wannan rana, nan Dady ya jawota jikinsa ya soma
rarrashinta, da kyar ya shawo kanta ta yi shuru, sai hawaye ke fita tare da ajiyar zuciya, nan da
nan zazzab'i ya rufeta. Dady ya cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya tare da kalamai
masu dad'i,
"my Husna Insha Allah in an kammala biki zan had'aki da mijinki in baku adress d'in in da
mahaifiyarki take domin ku je ku gana"
Da sauri Husna ta tashi daga jikin Dady, murmushi ya bayyana a fuskarta ta ce.
"Dagaske Dady?"
Wanin hararan wasa Dady ya yi mata.
"Au da na saba miki wasa ne irin haka?"
Dariya ce ta sub'uce mata.
"Ni bance haka ba, tambayarka dai na yi"
Murmushi ya yi yana shafa gashin kanta.
"Insha Allah za kije wurin Ummanki da zarar an kamala bikin nan, in kun natsa sai ku tafi"
Dad'i ne ya lullub'eta, take damuwar da take ciki ya ragu mata, duk da bata son auren a wani
b'angare na zuciyarta ta yi farin ciki, dan auren zai zama sanadin had'uwarta da Ummanta. Da
wannan farin cikin suka rabu da Dady wanda ya bita da kallo cike da tausayawa, a ransa yana
tunawa da Matarsa abin k'aunarsa Zainab, wacce kullun kwanan duniya yake kwana ya shi da
ita a zuciyarsa.
*So da k'aunar gaskiya bata rub'a, hak'ik'a So wani tubali ne a Zuciya wanda in har ya riga ya
ginu, rushewarsa sai Allah. Ko da tazarar ya kai nan da bangon duniya ne to son yana nan
daram, kamar yadda Khalil da Zainab suka tsinci kansu. Allah ka had'amu da masoya nagari.
Ameen*
*******
*_Ranar D'aurin Aure..._*
[11/1, 6:18 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 53 ~ 54_*
*Ranar d'aurin aure*
Yau ya kama ranar d'aurin Aure wanda ya yi dai-dai da ranar Lahadi weekend, wanda za'a
d'aura Auren da misalin k'arfe 11am na safe. Gidan Dady ya kacame da dangi sai hada-hada
suke yi, girki kala-kala aka girka, Husna na masaukin Momy Halima, ta yi wanka ta sanya leshi
pink mai ratsin bak'i da fari, d'inkin riga da zani rafa, Ruky mai make-up tazo ta tsantsara mata
kwalliya had'e da d'auri mai kyau, fad'in kyau Husna zai iya cike spice d'in da ya rage na littafin,
idonta ya kan kawo kwalla sai dai bata bari ya zubo take shanyewa, su Minal ne ma suke dan
zolayarta take murmushi, kwalliyar ya gama bayyana tsarin fatarta kuma ya amshi jikinta, falon
Dady suka wuce can suka baje ita da kawayenta, hakanan Husna ta riski kanta da fad'uwar
gaba in ta tuno da Uncle Sadiq, ta kasa jure hakan da sauri ta mik'e ta wuce bed room d'in
Dady, ta d'auki wayarta Numban Sadiq ta d'anna harya gama ringing bai d'auka ba, sai da ta yi
masa kira kusan uku amma bai d'aga ba. Hakan yasa ta kuma shiga damuwa hawaye taji yana
sauka kan kumatunta wanda bata san dalilin fitan su ba, zama ta yi gefen gado ta rafka ta gumi
tana tunanin rayuwarta.
Ta b'angaren Sadiq yana kallon kiran amma ya kasa d'auka, zaune yake gefen gado abin
duniya ya lullub'eshi, tunani iri-iri yake yi, ganin kiranta shi ne ya dawo da shi duniyar tunanin
daya lula, bin wayar ya yi da kallo nan da nan idonsa ya kawo kwalla, ya yi yunk'urin kiran ta sai
ya fasa, yana k'ok'arin aje wayar sai ga kiranta ya k'ara shigowa, ya d'auka ba tare da ya furta
komai ba, ta b'angaren ta ta ce cikin muryan kuka.
"Uncle kana ina? cikin kwana kin nan inna k'ira ka baka d'auka uncle ko na yi maka laifi ne?
Uncle ka yi min magana mana"
Ta k'arasa maganar da gunjin kuka, hawaye ne ya gama wanke idon Sadiq, a yau ya k'ara
tabbatar wa zuciyansa ya jima da kamuwa da soyayyar Husna, ya kasa fahimta sai a cikin
kwanakin nan, cikin sanyin murya ya ce.
"Husna baki min komai ba, kawai dai nayi nesa dake ne saboda aure zaki yi, kuma a matsayina
na wanda bamu had'a komai ba kin ga ya kamata na k'auracewa duk wani abin da zai had'amu,
ki yi hakuri ki daina kuka, Husna kin same min wani b'ari a rayuwata ina tare dake a Zuciyata,
duk in da kika je ba zan manta dake ba"
Kukan tane ya k'aru tana yi da shassheka.
"Uncle ni bana son auren nan, har yau ban san waye Dady zai aura min ba, bana son kowa
Uncle"
Da sauri Sadiq ya ce.
"Har ni baki so kenan?"
"A'a Uncle, a duniya daga Dady sai Momyna sai Kai, kune wanda nake So sosai, kuma bana
burin rabuwa daku, dan Allah Uncle ka hana auren nan bana son sa"
"Ki yi hak'uri my Husna hakan ba zai yuwu ba, saboda aski yazo gaban goshi, ki yi hak'uri ki
amshi k'addararki ki yiwa Dady biyayya insha Allah zaki sami fa'idar haka, kuma Mijin da Dady
zai baki mutumin kirki ne, ina kyautata zaton zai rik'e ki Amana"
Nan ya yi ta lallashinta da kalamai masu dad'i har ta yi shuru.
"My Husna yanzu kije ki wanke fuskarki, ki k'ara yin make-up kinga saura awa d'aya a d'aura
auran, bana son d'igon hawaye ya sake sauka a idonki"
"To my Uncle ba zan sake kuka ba amma sai ka yi min murmushi"
Murmushi ne ya sub'uce masa ya ce.
"Gashi na miki"
"To kamin waka mai dad'i"
Dariya ta ba shi har hok'oransa suka fito.
"Husna yau dai da rikici kike ji, kuma ni ban iya waka ba"
Cikin shagwab'a ta ce.
"Uhum my Uncle in baka yi ba zanyi kuka"
"A.a kar ki yi kuka, bari na miki"
Nan ya gyara murya ya soma rare mata wak'ar Nura M Inuwa na wak'ar Amarya.
_"í ¼í¾¶lokacin ki ne ya yi Amarya 'yar Amana zo ki je ki zauna da Miji Aure ibada ne,í ¼í¾¶ babu ke a
yau babu gantali a titi, kinga ke da Angonki ne nakewa baiti, ina da sahibata na kasa b'oye
sonta, me zana je na furta ban shawara Amarya, tunda duk abin cewa yanzu na garekií ¼í¾¶"_
Husna ta katse shi da cewa.
"Uncle waye kake so ne haka?"
Dariya ce ta sub'uce masa ya ce.
"Sirri ne, kuma ai wannan wak'a ce na miki, na M Inuwa bawai ni ne na rera ta ba"
Murmushi ta yi ta ce.
"Ashe ka iya waka sosai?"