Showing 30001 words to 33000 words out of 81944 words
Chapter 11 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
zata
kore shi in har ya cigaba da shiga huruminta.
Sadiq yana zuwa kullun ya tambaya Baba labarin Husna zancen dai d'aya yake gaya masa, shi
ne tana lafiya yanzu ba a barinta tana fitowa waje, hakan ya k'ara sanya shi a damuwa domin
yau kusan wata d'aya kenan bai sanyata a idonsa ba, kullun dai Addu'a yake mata. Ya cigaba
da zuwa aikinsa kamar yadda ya saba sai dai damuwar yana linke a zuciyarsa. Yana k'ok'arin
zuwa gidan Yaya Ismail wanda in ya ga Khadija sai ta rik'a d'auke masa kewar Husna.
******* *******
*Bayan wata biyu*
Ya yi dai-dai da watan Dady Biyar kenan a k'asar Manaco, Sadiq ya samu hutu a wajen aiki na
wata d'aya, haka ya shirya ya bama Baba kud'i dubu Ashirin, dubu sha biyar na Husna, dubu
biyar ya rik'e, nan ya yi masa godiya ya shiga mota sai Kaduna.
******
*Kaduna*
Yana shiga gida ya wuce d'akin Anty Zainab ya sameta tana karatun wani littafin addini, zama
ya yi a k'asa ya sanya kansa a kan cinyarta sai ya fashe da kuka, mamaki da damuwa ne suka
cikata.
"Sadiq Llafiya? ko anyi maka wani abu ne?"
Ya dago idonsa da sukyayi ja ya ce.
"Anty na ina farin cikin ganin ki ne sannan kuma ganin ki ya debe min damuwa ta"
"My son damuwar me kake yi?"
Murmushi ya yi tare da mik'ewa tsaye.
"Ni dai tunda na sameku lafiya Alhamdulillah, sannan ba wata damuwa bace nan gaba zan
sanar miki"
"Yau dai ina ga da rikici ka dawo, halama ko gaisawa dasu Umma baka yi ba?"
"Wallahi kuwa kamar kin sani ina shigowa naga ba kowa a falon shiyasa na taho nan d'in"
"To maza ka je ku gaisa da su Umma, ni bari na shiga kicin da d'aura maka abin da zaka ci, dan
yau tuwo Umma tasa aka yi a gidan, Amminka ma ina ga bata girka komai ba nan ta zo ta ci
namu"
"To shi kenan bari naje na dawo"
Har ya kai bakin k'ofa sai ya juyo da sauri ya ce.
"Anty ina little yake?"
"Yana gun Umma"
Bai k'ara cewa komai ba ya kama gabansa.
*****
Tun ranar da yadawo bai iya fita ko ina yana zaune a gida kullun yana tare da Anty Zainab da
little Al'amin, ko kuma ya kunshe a d'aki yana tunanin Husna.
Ranar juma'a, Baffa ya tara su a falonsa da daddare nan suka gaisa sannan ya d'aura da cewa
"Zainab a kan ki muka yi wannan taron naga zamanki ya yi yawa a gida, shi ne na yanke
shawarar bud'e miki pharmacy a nan bakin babban hanya, na sanya an gama miki komai hatta
magani anyi oder su an zuba, yanzu bud'ewa ya rage tare da sanya sunan wurin, dan haka
yanzu wani suna ya kamata a sanyawa wurin?"
Farin cikinta ne ya bayyana k'arara a fuskarta, cike da murna wanda kowa a gurin ya yi farin
ciki, cikin ladabi ta ce.
"Uhum Baffa ina ga a sanyawa wurin sunan Asma'u pharmacy tunda kaga sunan Umma ce"
Murmushi Baffa ya yi wanda ya san ba dalilin sunan Ummanta bane sai dalilin sunan 'yarta ce,
Anty Jidda ne ta ce.
"Zainab mai zai hana a sanya Husna Pharmacy ai kamar zaifi"
Kunya ce ta rufe Zainab sai ta sunkuyar da kai k'asa tana wasa da yatsunta, saboda ta fahimci
duk sun gano nufinta sai ta ce.
"Uhum Anty Jidda ni dai ba haka nake nufi ba, ko meye ma dai a sanya burina kawai in ga na
fara aiki"
Nan duk suka kwashe mata da dariya Baffa ya ce.
"Ai magana ta k'are tunda Antynki ta zab'ar miki"
Umma ma ta goyi bayan haka ko wanne dai ya fad'i albarkacin bakinsa, nan Yaya Aliyu ya kira
Yaya Ismail da Anty Binta ya sanar musu tunda su ba ayi taron dasu ba, nan dai taro ya tashi
cikin farin ciki kowa yana murna yadda Zainab ta saki jikinta aka yi hira da ita.
******
Bayan mako d'aya, an kammala had'a pharmacy d'in, komai na buk'ata an sanya mata wanda
hatta ma'aikatan da zasu yi aiki a gun an samar mata, mutum biyu safe sai cashier d'aya,
yamma da dare ma haka, sai ita da za ta yi consulting da safe sai wani Dr Idris daga yamma
har dare. Abu dai an tsara shi abin sha'awa, a ranar juma'an aka bud'e wurin tare da yin wata
had'add'iyar walima sun gayya to dangi na kusa da abokan arziki an ci an sha duk a cikin gidan,
sannan aka d'aura da Addu'a da fatan alkhairi ga Husna Pharmacy. Yaya Ismail da Yaya Aliyu
suka hada kudi suka siya mata sabuwar mota. Farin ciki a gun Zainab baya misaltuwa, a
wannan ranar kowa ya shaida Zainab na cikin farin cikin, Sadiq shi ne dan jelarta duk in da take
yana biye da ita shima cike yake da farin ciki, sai dai inya tuna da Husna sai yaji ba dad'i a
ransa, amma ko ba komai sun faran ta masa rai da aka sanya sunan Husna pharmacy, yana
burin inya koma Kano ya bata labarin an sanyawa Antynsa sunanta a pharmacy.
An bud'e wuri ya yi kyau, sun gayyato Liverty TV da DITV a wajen domin su yi tallar pharmacy
d'in, an washe taro lafiya in da kowa ya tafi cikin Farin ciki.
Ranar monday Zainab ta fara aiki a pharmacy d'in ta, wurin ya yi matuk'ar burgeta harda
k'aramin office d'inta na ganawa da marasa lafiya, bayan misalin k'arfe uku na rana Sadiq ya zo
d'aukar ta a mota suka wuce gida.
Tun daga wannan ranar Zainab take cikin rarin ciki amma duk da haka tana da damuwa a ranta
sai dai ta barwa rabbil izzati, ciniki sai k'aruwa yake tare da samun customers sosai.
******
Ana gobe Sadiq zai koma Kano damuwansa ne ya k'aru, burinsa bai wuce yaje yaga halin da
Husna take ciki ba, da daddare yana zaune a d'akin Ammin sa ya ce.
"Ammi haka nan sai naji gabana yana fad'uwa hankalina yana tashi"
"Subhanallahi! meyasa kake jin haka?"
"Ammi wani amana na d'aukarwa kaina wanda yanzu kimanin wata uku kenan ban sanya
amanar a idona ba, shiyasa duk naji hankalina a tashe"
Ajiyar zuciya ta yi tare da yin murmushi, tasan duk yadda za ta yi ta matsa masa ya gaya mata
ba zai fad'a ba saboda tasan shi mutum ne mai mugun zufin ciki, shawarwari ta shiga ba shi
tare da nasiha mai ratsa zuciya da kuma sanin darajar girman Amana, hawaye ne ya soma yi
gaba d'aya hankalinsa ya tashi burinsa bai wuce ya ganshi a cikin garin Kano ba, da lallashi
Ammi ta lallab'ashi ya wuce d'akinsa cike da damuwa.
Da safe ya shirya tare da yin sallama da mutanan gidan ya kama hanyar Kano, yana isa, kaya
kawai ya a jiye ya wuce office, sai yamma lis ya dawo, ya shiga gida ya watsa ruwa kana ya fito
ya samu Baba yana alwalar Sallar Magrib, suka gaisa kana Sadiq ya tambaye shi labarin
Husna, murmushi ya yi wanda yafi kuka ciwo.
"Ai sunyi hutun makaranta kusan yau sati uku kenan ban sanyata a ido na ba"
Wuri Sadiq ya samu ya zauna saboda yaji k'afafunsa ba zasu iya d'aukarsa ba yana jinjina
maganar Baba.
"To lafiya bata fito wa?"
"Uhum ina ga lafiyar kenan tunda har yau Alhaji bai dawo ba, kuma tun ran nan data duketa ban
kuma jin kukanta ba ina ga abin ya yi sauki ne"
"To wai Baba bata zuwa islamiya ne?"
"Gaskiya da tana zuwa sai Hajiya ta ce yawo take zuwa aiko dole aka cireta, an d'auko mai yi
mata karatu a gida, nan ma hajiya tasa Alhaji ya kore shi saboda mugun kissarta"
"Ya salam yanzu haka take zama bata san addini ba, ai tun yanzu ya kamata ace ta fara sanin
addini"
"Uhum to yaro bokon ma ai da da hali hanawa zata yi, nan take zuwa nake koya mata dan abin
da na sani"
"Allah sarki, Allah ya saka maka da alkhairi"
"Sadiq dani da kai duka Ameen ya rabbi"
Nan suka wuce masallaci dan gabatar da sallah magrib.
*****
Dady ya dawo daga k'asar Manaco, ko da ya dawo Husna ya fara tambaya Momy ta ce
"Tana d'aki kwance ba lafiya mun je asibity an had'a mata magani, kuma ni abin na Husna gaba
yake k'arawa, yanzu ko falo bata fitowa kullun tana d'aki, makaranta ma da kyar nake turata
tatafi"
Ta k'arasa maganar kamar zata fashe da kuke, zufane ke karyowa Dady duk sanyin AC dake
ratsa d'akin, gaba d'aya damuwa ce ya rufe shi, mik'ewa ya yi ba tare da ya ce uffan ba ya isa
d'akin, kwance take ta rufa da wani bargo wanda ya yi datti sosai, sunanta ya kira a hankali, da
sauri ta yaye bargon ta tashi zaune, sosai ta rame ga wasu kuraje da suka fito mata ajiki kamar
k'anzuwa, ido waje kamar zata ruga a guje saboda tsananin tsoro, ganin Dadyn ta ne yasa ta
dai-daita girman idonta suka dawo yafda suke, hawaye ne ke fita a idon kamar an bud'e famfo,
bakinta na rawa ta ce.
"Dady"
Mutuwar tsaye Dady ya yi tare da k'ura mata ido, tashin hankali ne ke baibaye duk kan tsokar
jikinsa ganin yadda Husnah ta fita hayyacin ta, juyawa ya yi ba tare da ya k'arasa inda take ba
ya fita cike da masifa a fuskar sa, turaren wuta ne mai sirke da magani ya ziyarci hancinsa tun
daga wannan lokacin bai kuma sanin inda kansa yake ba sai farkawa ya yi ya ganshi kwance
bisa kan gadonsa, shuru ya yi na tsayin mintuna yana son ya tuna abin da ya faru, amma ya
gaza tuna komai illa tunawa da ya yi ya dawo daga tafiya.
Momy ce ta shigo rik'e da tire na abinci ta ajiye ta matsa kusa da gadon sai ta ganshi ya farka,
murmushi ta masa kafin ta ce wani abu ya ce.
"Hajiya ya aka yi na ganni a nan ni da ban dad'e da dawowa ba ko wanka banyi ba fa"
Murmushi ta masa mai cike da kissa.
"Haba dai ka ce ka manta, da k'afarka ka zo ka kwanta, ai kusan yanzu awa hud'u da dawowar
ka, ka dad'e kana barci ga shi yanzu an kusa kiran Sallah Magrib shiyasa na zo na tasheka ko
abinci ka ci"
Mamaki ne k'arara a fuskarsa.
"Awa hud'u fa kika ce?"
"Kwarai kuwa awa hud'u ka yi kana barci"
Mikewa ya yi da sauri ya fad'a bayi danya watsa ruwa. Momy bin shi ta yi da kallon mugunta
tana k'issima wani abu a ranta.
_Momy sun je wurin wani boka, ya bata maganin mallaka da wanda zai mantar da Dady Husna,
boka ya tabbatar mata da Alhaji na shigowa to karta bari ya d'auki lokaci ba tare da ta turare
gidan da wannan turaren maganin. Lokacin kuma daya shiga d'akin Husna shi ne taje da sauri
ta sanya maganin a wuta ta gauraye d'akin, Dady yana fitowa ya shak'i maganin, daga nan
kuma da kyar ya iya kai kansa d'akinsa ya fad'a gado sai wani barci mai nauyi ya d'auke shi
cike da mafarkai barkatai. Wannan shi ne abin da ya faru kafin awa hud'u da suka wuce._
Tun daga wannan ranar Dady baya tambayan lamarin Husna, daya dawo aiki tofa sai barci
tunda dama bai dawowa da wuri, Momy burinta ya cika daga nan ta cigaba da abubuwa yanda
take so, ta gama sangarta Nura duk abin da yake so taje masa, gaba d'aya baya karatun kirki in
banda rashin ji da d'aukar magana babu abin da yake yi.
*****
Sadiq duk ya rame saboda tsananin damuwa, abinci sai ya yi da gaske yake iya ci, ulcer ya yi
masa mummunar kamu, gabansa ke yawan fad'uwa duk lokacin daya tuna Husna, tun yana
tambayar Baba labarinta har ya yi shuru sa idai su gaisa kawai, lamarinsa yana bawa Baba
mamaki saboda ya lura sam baya cikin natsuwa kuma kuzarinsa ya ragu, a zuciyarsa yake
cewa.
'Allah mai iko kai kad'ai kasan dalilin shakuwar yaron nan da Husna"
********
Husna sun koma makaranta da safe Jimmai ta shigo d'akin dan ta taimaka mata ta yi wanka
tare da shiryata, Momy ce ta shigo d'akin dan ta sanya ta ta yi shirin makaranta, baki bud'e ta
tsaya tana kallon Jimmai, ita kuwa Jimmai jikinta ne ya d'auki rawa domin ta tuna da gargadin
da ta yi mata akan in har ta kuma shiga d'akin Husna a bakin aikinta, baki na rawa ta ce.
"Hajiya dan Allah ki yi hakuri naga ba tada lafiya ne shiyasa na shigo na taya ki shirya ta"
Bata bari ta k'arasa maganarta ba ta wanke ta da mari, ta ce.
"Zi zaki gayawa na yi hakuri? ai na gargad'e ki akai kuma kika karya min dokata, to ki sani
yanzu ba sai anjima ba, ki tattara kayanki ki bar min gidana, matsiyaciya dama irinku baku iya
cin arziki ba"
Kuka Jimmai ta fara yi tana yiwa Hajiya magiya, amma ina banda sirfa mata zagi babu abin da
take yi, dole Jimmai ta tattara kayanga ta fito cike da k'unar zuciya, bata tsaya bawa Baba mai
gadi labari ba tasa kai ta fita. Baba girgiza kai ya yi kawai, yaji duk zaman gidan ya gundure shi,
domin yadda yaga Jimmai, yasan cewa Hajiya ce ta koreta, kuma bai wuce dalilin Husna ba.
*Rahma ce*
[10/23, 3:49 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KAÆŠAICI*
© *Rahma Kabir*
*Wattpad:*@rahmakabir
*_Page 23 ~ 24_*
Husna ta isa makaranta a latti, Anty Meena tana ganinta ta ce ta koma gida sai taji sauki sai ta
dawo makaranta, haka tabar class d'insu jiki ba kwari, Khadija duk ta damu da taga kawarta ba
lafiya. Husna a nesa da makarantarsu ta samu kan dakali ta zauna ta sanya fuskarta akan
cinyanta tana kuka a hankali tare da nishi kad'an-kad'an na masara lafiya. Sadiq ne a cikin mota
ya wuce ta da sauri, kamar ance ya duba madubin gefen motarsa sai ya hango yarinya, Sadiq
shi mutum ne mai tausayi da taimako, hakanan yaji bazai iya wucewa ba dole ya yi ribas ya
dawo kusa da ita ya yi parking, ba tare da ya fito ba ya bude murya yadda zata ji shi ya ce.
"Ke me kike yi a nan baki shiga makarantar ba? ko an koreki kud'in makaranta ne?"
Husna ta ji muryar da ba zata iya mantawa ba ya daki kunnenta, da sauri ta d'ago idonta wanda
suke cike fal da hawaye, suka yi ido hudu da sauri Sadiq ya bud'e motar ya fito jikinsa yana
rawa, da k'arfi ya furta.
"Husna me kike yi a nan, me yake damunki naga jikinki duk kuraje?"
Haka ya jero mata wannan tambaya wanda bata da amsarsu sai ma kukanta da ya k'aru ta
tashi ta rungume shi tana shasshek'ar kuka, Sadiq yaji jikinta ya yi zafi sosai, da sauri ya
d'auketa cak sai a cikin mota ya direta kana ya dawo mazaunin driver ya figi motar a guje kamar
zai tashi sama. Wani asibiti dake kusa ya kai ta, cikin k'ank'anin lokaci ya yanki kati tare da ba
shi damar ya shiga su ga likita, da yake asibitin na kudi ne ba layi, suna shiga suka ga wata
matsiyar likita mai zuna Dr. Safiyya, nan ta shiga duba ta tare da rubuta musu gwajin jinin da za
ayi mata, nan ya wuce da ita dakin gwajin jini, sun diba jininta suka dauki awa biyu suna
gwaje-gwajensu, bayan sun gama suka basu sakamako sannan suka koma gun likita.
"Abin da ke damun Husna malaria da typhoid sai kuma ulcer daya kamata, wannan kurajen
kuma k'anzuwa ce wanda kazanta ke kawota"
Dr. Safiyya ce kewa Sadiq wannan bayanin, idonsa ya yi jajir makar zai yi dan damuwa, nan ta
basu gado dan sai an kwantar da ita, ya nima alfarman ayi musu treatment d'in yinin ranar in
yaso zai rik'a kawota kullun har a gama mata komai, nan likita ta amince tare da kiran Nurse
Ruky ta zo ta karb'i folder d'insu tare da kaisu d'akin da aka kwanatar da su.
An sanya mata drip da duk wani magani daya kamata a bata, Sadiq ya siyo mata moltina tasha
daga nan barci ya yi awon gaba da ita, ya nima alfarma gun Nurse Ruky ta kula masa da ita
zaijye ya dawo, ba musu ta amince saboda taga yaro mai kyau da kwarjini zuciyarta ta kamu da
son sa a lokaci d'aya. Su Ruky anga sweet guy lolí ½í¸œ.
Wurin aikinsa ya wuce ya d'auki uziri kana ya dawo, sai misalin karfe uku ruwan ya k'are
sannan suka sallame su tare da umarnin su dawo gobe a cigaba da treating d'inta.
Gidansa ya wuce da ita, bayan sun shiga cikin falonsa ya ce ta zauna a kujera ta jira shi, ba
musu ta zauna, d'akinsa ya wuce ya shiga bayi tare da had'a mata ruwan wanka mai zafi ya
sanya mata dettol a ciki kana ya fito ya ce ta biyo shi a baya, da farko kamar bazyata bi shi ba
saboda tana jin tsoro, da yaga haka sai ya tsaya ya lallasheta haka ta bi shi badan ta so ba, ya
shiga da ita tare da nuna mata yadda zata yi wanka ya bata tawul wanda in ta gama zata
d'aura, sannan ya nuna mata kayan da zata sanya inta fito, riga da wando fakistan ya siyo mata
su tun a hanya kafin su shigo gidan, ta