Showing 27001 words to 30000 words out of 81944 words
Chapter 10 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
mai gadi sai da ya yi kwalla da Allah wadaran Momy, haka ma ta
bangaren Jimmai mai aiki.
******
Tun daga wannan lokacin Sadiq ya fara jin kukan Husna ba sauyi, kullun kukanta kalansa
daban ba safiya ba rana ba dare, ya kasa tantance mace ce ko namiji, shi dai ya shaida muryan
yaro ne yake ji ba babba ba. Tun abin baya damunsa ya dauke shi ba komai bane yana
ta'allak'a abin da k'ila yaron baya jin magana ne, daga bisani ya fara damuwa da yawan dukan.
Wata rana ya fito da shirin zuwa wajen aiki ya fito da motarsa ya yi parking, ya rufe gate kana
ya koma mota, ya fara tafiya, dai dai lokacin da zai gota gate din su Husna, yaga ta fito a guje
kamar an biyota sanye da uniform ajikinta na makaranta, sai ya tafiya a hankali yana bin bayan
ta, mamaki ne ya cika shi sai ya fara tunanin ko dai dama ita ce ake yawan duka? sai ya kauda
tunaninsa da cewa.
'Haba dai k'ila yaran gidan suna da yawa'
Da haka ya shashantar da lamarin ya kama gabansa.
*******
*A Kaduna*
Anty Zainab ta d'an saki jiki yanzu tana harkokinta sai dai ba kamar da ba, little Al'amin ya yi bul
bul abinsa yanata k'ara wayo kamanninsa da babansa yana kara bayyana, yaron ya yi farin jiki
sosai kowa na sonsa wataran ma baya yini a gunta sai wurin Anty Jidda da Umma yake yini,
hakan na yiwa Zainab dad'i saboda tana samun damar yin ibada sosai. Ta wajen su Baffa mai kanti kuwa kasuwancinsu yana ta hab'aka kasantuwar yawan kyauta ga
talaka da suke.
Anty Binta har yanzu Allah bai bata haihuwa ba, magani ba wanda basa nima amma har yanzu
shuru, Alhamdillah ta yi dacen sirikai duk da hakan suna nuna mata so ba wanda ya canza
mata akan rashin haihuwar. Zahra kanwar Sadiq tana wajenta tare da samun gata sosai da
kulawa fiye ma da wajen mahaifiyarta Anty Jidda.
Abba Iro da Inna Kulu suna rayuwar rashin jin dad'i da kewar mutuwar d'ansu tilo d'aya Al'amin,
kullun cikin yi masa Addu'a suke yi, hakan ne yasa Inna Kulu ta karb'o d'iyar k'anwarta daga
k'auye mai suna Kausar wacce bata wuce sa'ar Khadija ba d'iyar Yaya Ismail, sun sanyata a
makaranta tana zuwa, hankalinsu ya d'an kwanta saboda suna ganinta a gabansu.
******
*A Kano*
Sadiq yawan kukan Husna ya fara sanya shi cikin damuwa. Wata rana ya yi wanki yana shanya
ta bayan gidan yaji ana ta kwalawa Husna kira, tunani ya shiga yi.
'Ko dai wannan yarinyar dana gani ita ce Husna?'
Murmushi ya sub'uce masa tare da tambayar kansa.
'Wai meyasa na damu da rayuwar mutanan gidan nan ne?'
Bai k'arasa tunaninsa ba yaji an fara dukanta tare da manya manyan zagi, haushi ne ya cikashi
ya rasa meye dalilin dayasa wannan matar ke dukan yaranta kamar jakai, haka ya gama
shanyan a gaugauce yabar gurin, yana shiga d'akinsa ya zauna, kukan Husna ya fara masa
yawo a kwakwalwa, haka ya yini cikin damuwa. A ranar ne ya gasgata kukanta ne kullun yake ji,
naya cewa.
"Ashe dama mace ce ba namiji ba? to meyesa kullun ake dukanta?"
Bai da amsa haka ya tashi ya shirya ya bar unguwa cike da takaici yana dana sanin zamansa
unguwar, wanda har zuciyarsa ya fara tunanin barin area ya koma wani gurin. Wani b'angare na
zuciyarsa ya hane shi, haka dai ya cigaba da zama tunda saura masa watanni yabar garin gaba
d'aya.
****
Rayuwa ya cigaba da tafiya wanda a yanzu shekarun Husna 7 cikin na 8, a yanzu Sadiq
tausayin Husna ya gama maye zuciyarsa kullun tunaninsa ya zai yi ya taimake ta, wanda daga
bisani ya gane Momy ba ita ce ta haifeta ba, kuma mahaifinta bai san da wannan tuggun da
Momy ke mata ba. Kullun da tunaninta yake kwana yake wayar gari.
Ya kammala service d'insa amma sam baya burrin yabar Husna cikin wannan rayuwa yana son
ya taimaki rayuwar ta, ana cikin haka ne ma'aikatar suka rik'e shi dan sun ji dad'in aiki dashi,
farin ciki ne ya kamashi ya kira gida ya sanar musu, suma murna suka yi masa tare da fatan
alkhairi. Da hakane ya cigaba da zama a Kano, wanda har ya fara magana da Husnah ranar
data fita siyo chewing gum, yana son ya jawota a jikinsa dan su saba...
_Wannan shi ne silar shigar Husna cikin rayuwar kad'aici, wanda yake haifar mata da matsaloli
sosai nan gama_
******* *******
** *CIGABAN LABARI* **
_Bayan sati d'aya_
Kamar yadda Dr. Ismail ya buk'aci Momy ta dawo da Husna, haka ta shirya ta kaita. Zaune taje
a gaban Likita, Dr. Ismail yaji dad'in yadda yaga Husna ta sauya kamar ba ita ba, da alama tana
samun abinci sosai, maganin daya bata ran nan ya d'auko ya bawa Husna ta sha, ikon Allah
yau bata yi garda man sha ba, sannan ya k'ara yiwa Momy bayani kamar na baya kana ya
sallamesu da bayanin ba sai sun k'ara zuwa ba, yadda aka bata magananin ya wadatar ba sai
ta kuma sha ba, cike da farin ciki Momy ta isa gida.
********
Husna ce zaune wajen Baba mai gadi yana koya mata karatun Al-Qur'ani, ya ji ana knocking
k'ofa ya mike da sauri yaje ya bud'e k'ofar, Sadiq ya gaishe shi kana yad'an sosa k'eya ya ce.
"Dama na zo duba Husna ce"
Da sauri Baba ya k'arasa fitowa wajen gaba d'aya ya rufe k'ofar
"Taro lafiya kake nimanta? hala kai dan uwanta ne dan naga kuna yanayi"
"A'a ni mak'ocinku ne, ran nan naganta taje siyan abu can shagon sama shi ne muka yi magana
da ita, a tak'aice dai naga kwana biyu ban ganta ba shi ne na zo tambaya"
Sadiq ya yi maganar yana murmushi. Baba shima ya yi murmyshi.
"Ikon Allah ashe kaine mai gidan nan"
Yayi amfani da hannunsa yana nuna gidan, Sadiq ya gyada masa kai alamar eh, Baba ya lek'a
ya kira Husna.
"Ai gata nan ma muna karatu da ita ne"
"Allah sarki"
Husna ta fito, tana ganin Sadiq ta washe baki, fararan hak'oranta da take famfara sune suka
bayyana, gefen kumatunta suka lotsa, shima murmushin ya yi mata tare da cewa.
"My Husna"
Ya kama mata hannu suka gaisa ya ciga da cewa.
"Ban ganki ba kwana biyu shi ne na zo dubaki"
Husna ta yi dariya ta ce.
"Uncle zaka rika kaini makaranta ko ka siya min biskit, kaga Momyna bata bani sai ta rik'a
dukana, Abbana kuma kullun sai dare yake dawowa bana ganinsa har inyi barci, Momy tana ta
cin zalina ai Allah sai ya sakamin ko Uncle"
Sadiq ya b'ata rai ya ce.
"Momin naki kike cewa haka, to mun b'ata ma"
Nan da nan ta yi rau rau da ido tana son yin kuka.
"Allah unclear duka na take yi, kar kayi fushi dani kaji"
Ta k'arasa maganar tana matsar kwalla, Baba mai gadi yana gefe ya d'auko bancinsa ya aje a
bakin gate d'in ta waje ya zauba, ya ce.
"Yaro rabu da ita kasan shirmen yaro"
Sadiq ya yi ajiyar zuciya yayi ya zauna gefen Baba yana cewa.
"Kasan kuma da wuya yaro ya rik'a fad'ar magana haka kawai ba tare da kamshin gaskiya aciki
ba"
"hakane kuma, dan tabbas gaskiya ta gaya maka"
Sadiq ya gyara zama dan ya samu abin da yake so.
"Baba kana nufin dagaske ne abin da take tafad'a?"
"Kwarai kuwa da gaske ne, zan iya ce maka shekaru uku cikin na hudu dana fara aiki a gidan
nan, wallahi d'ai-d'ai kun rana ne Hajiya bata dukanta, wataran ma fiye da sau biyu take
dukanta a rana, amma kuma zan iya ce maka Alhaji har yau bai iya gane haka ba saboda
makircinta"
Sadiq sai ya k'ara gyara zama yana saurarensa, Baba ya cigaba da cewa.
"A yanzu haka cutar hauka ta d'aurwa Husna wai an kai ta asibiti ance tana da Matsala a
kwakwalwa, ta hada da makircinta ta sanarwa Alhaji yanzu a haka suke d'aukar ta"
Sadiq ya yi salati tare da shiga matsanan cin damuwa, nan dai Baba ya cigaba da ba shi labarin
abin da ya sani game da ita ya sanar da shi cewar tabbas ba Momy ta haifeta ba. Ya shiga
damuwa sosai wanda har sai da yaji kansa na sarawa, sun d'auki tsawon lokaci suna
tattaunawa wanda daga bisani Sadiq ya k'irga dubu goma ya bawa Baba da cewa duk abin da
Husna take so game da abinci in ba a bata ba, da kud'in break na makaranta dama sabulun
wanki ya rik'a siya yana mata, zai rik'a biyansa duk karshen wata. Sannan ya ciro dubu uku ya
ba shi yasa a aljuhunsa, Baba nan ya shiga godiya da sanya masa albarka, hakika ya yaba da
hankalin Sadiq, kuma lokaci daya yaji zuciyarsa ta aminta da shi, yana ji a ransa kila wani d'auki
ne Allah ya kawowa Husna a saukak'e. Ya jima gun har sai da Sallan Magrib ya gabato sannan
ya mik'e ya yiwa Baba sallama, ya kama wa Husna hannu ya ce.
"my Husnee zan tafi, gobe in Allah ya kaimu ki fito da wuri zan sauke ki a makaranta"
Ta gyada masa kai ta ce.
"Zaka siya min kosai da koko, kaga Baba ya dauna bani, kullun haka nake tafiya banci komai,
sai k'awata Khadija ke tsammini abincinta in tazo da shi"
Ta k'arasa maganar da shagwaba kamar za ta yi kuka, bai bata amsa ba ya kalli Baba ya ce.
"Dan Allah ka tabbatar kafin ta tifo ka tanadar mata abin da zata karya da shi in kud'in ya kusa
k'arewa kamin magana"
"To yaron Albarka zan sanar maka insha Allah, sai dai ka rik'e amanar yarinyar nan, kasan
duniya sai sannu, ba a shaidar mutum, kuma kaga duk abin da ya faru da yarinyar nan ni za'a
fara tuhuma"
Sadiq yayi murmushin gefen baki ya ce.
"Jar ka damu Baba insha Allah zaka sameni da rik'on Amana"
Suka k'ara yin sallama kana ya wuce yana dagawa Husna hannu.
*******
Dady daya dawo daga office ya tambayi Momy yadda suka k'arayi da likita kan maganar
Husnah, nan ta shiga jero masa bayanin k'arya, damuwa ne ya k'ara shigarsa ya mik'e ba tare
da ya k'ara cewa komai ba ya wuce d'akin Husna, ya sameta tana ta sharb'an barci tare da
ajiyar zuciya, kwallane ya taru a idonsa ya sauka kan kuncinsa, gefen katifar ya zauna ya rafka
tagumi, kallonta yake yi ba tare da yakifta ido ba, tunani mai zurfi ya shiga yi akan aurensa da
Zainab wanda dana sani ya gama maye gurbin zuciyarsa, yana tausayawa 'yarsa da halin da
take ciki, da basu kauce wa umarnin iyayensu ba da duk haka bai faru ba, tun daga ranar da ya
rabu da Zainab jin dad'i da farinciki ya yi k'aura a cikin rayuwarsa, sai k'unci da damuwa mai
had'e da rayuwar *Kad'aici* yake ciki, wanda ya gasgata itama Zainab rayuwar da take ciki
kenan, domin soyayyar gaskiya sukewa juna. A wannan yanayin kukan badama yake yi sosai,
daga k'arshe ya yi Addu'a ya tofa mata tare da fatan Allah yasa suci jarabawar da ya yi musu.
Bayan ya koma sashinsa ya sanarwa Momy zai yi tafiya na tsawon wata shida, an turashi
K'asar Manaco dan yin wani kwas a can, ya cibaga da yi mata bayani tare da magiyar taciga ba
da rikon amanar Husna har Allah ya dawo da shi lafiya, ta yi murna da tafiyar dan ita ma tana
farin cikin freedom din da zata samu akan business d'inta, ta yi masa addu'a da fatan nasara,
da kuma alk'awarin rik'on amanar Husna.
*Rahma ce*
[10/21, 7:09 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KAÆŠAICI*
© *Rahma Kabir*
*Wattpad:*@rahmakabir
*_Page 21 ~ 22_*
Tunda Dady ya tafi Momy take fita tun safe sai yamma take dawowa, kud'i take bawa Nura ya
nima abin da zai ci ko kuma ta sanya Jimmai ta dafa masa indomi amma banda Husna da sai
abincin dare kawai take bata.
Husna tana samun kulawa dai dai gwargwado wajen Baba mai gadi yana k'ok'arin cika
Alkawarin daya d'aukarwa Sadiq, shi ne kullun yake shiya mata abinci da kuma kud'in break na
makaranta, in wankinta sun taru ya siwo omo da sabulu ya baiwa Jimmai ta wanke mata kayan
ko ya d'auki kud'i ya bata sai ta ki karb'a domin ai Hajiya tana biyanta. Gaba d'aya Husna ta
sauya ko a makaranta Anty Meenah ta yi mamakin sauyawarta, kullun cikin tsafta sannan ta yi
kyau ramar da ta yi ya ragu. Hakan yasa ta mai da hankali sosai a karatunta wanda a yanzu
kwakwalwarta ya samu raguwar damuwa da tunani. Hatta yaran class d'insu da suke kyamarta
sun daina har suna magana yanzu. Abotarsu da Khadija ya kara k'ulluwa sosai kullun suna tare
komai nasu d'aya suke yi, wanda har wasu suke musu kallon ko 'yan biyu ne saboda suna
yanayi da juna haske kawai Husna tafi Khadija. Sadiq yana duba Husna duk bayan lokaci
kamar weekend, hakan yasa suka k'ara shauk'uwa sosai.
********
Bayan wata biyu da tafiyar Dady, ya kama ranar asabar Momy tana gida bata fita ba a ranar,
k'awarta Haj. Uwani ta zo suna zaune suna hira, sai ga Husna daga waje ta shigo falon da gudu
tana dariya, bata san Momy tana gidan ba, tsawar da Momy ta daka mata ya dawo da
hayyacinta jikin ta, sun kunyar da kanta ta yi k'asa nan da nan ta shiga tai ta yin ta, Momy binta
da kallo ta yi cike da mamakin yadda ta sauya ta kara girma da kuzari, tambayar kanta ta shiga
yi.
'Yaushe na yi saken da yarinyar nan ta tamu freedom haka? 'Anya Doctor ya bani maganin
daya dace kuwa?'
Wani b'agare na zuciyarta ta ce.
'Kwarai ya baki ke ce dai ki kai sake, tunda wata biyu kenan baki zama a gida'
Nan da nan fuskarta ya sauya kamar anyi mata mutuwa, take ta gasgata abin da zuciyarta ta
raya mata. Mik'ewa ta yi ta zaro wayar wuta, Husna tana gani ta fara ja da baya har sai da ta
iske jikin bango tare ta runtse idonta, duka ne ta fara yi mata ta ko ina sai da ta yi mata lilis tana
ihu, kafin nan Haj. Uwani ta kwaceta tana cewa.
"Haba Hajiya ai sai ki sanya mak'ota su zage ki, ai a kwai ta inda zaki rik'a hukunta ta ba sai
duka ba, kawai ki rik'a rufebta ad'aki kina tura mata abinci yadda haukar zai kamata da kyau,
amma wannan ai wahalan da kai ne, k'ila ma garin dukanta ki zubawa kanki"
Wani nannauyar ajiyar zuciya Momy ta yi.
"Wallahi Hajiya banda ina tsoron yadda zan kwashe da Alhaji da sai na kasheta na huta, na
tsaneta bana kaunarta"
"To ai kisan mummuk'e kike yi yanzu, tunda kin je gun likita ya miki abin da kike so ai ke ce
kuma abu ke hannunki, shawarar dai dana baki farko ita zaki mata ki huta kawai"
"Gaskiya ne kin bani shawara mai kyau, bari ma ki gani tun yanzu zan fara"
Ta kama k'afar Husna tana janta kamar akuya, tun tana kuka a fili har ta koma sai hawaye ke
fita da ajiyar zuciya, a haka ta isa da ita d'aki tare ta yi mata barazanar kisa in har ta kuma ganin
k'afarta a waje, ido a bud'e cike da tsoro Husna ta amince da dokar ta, nan ta barta tana ta
susar jiki tare da matsanancin kuka, haka Momy ta fito falo suka cigaba da hira. Jimmai mai aiki
tana kicin, banda kuka babu abin da take yi, tana tausayin Husna, da tana da yadda zata yi da
ta raba Husna da wannan muguwar rayuwar, tana aiki tana zancen zuci.
Sadiq ne ya fito da sauri daga gidansa mako guda kenan rabonsa da Husna, sai dai suna
gaisawa da Baba time to time yana tambayarsa lafiyarta, yanzu ma kukunta da yaji ne ya kasa
sukuni ya fito, ya samu Baba a bakin gate zaune, a gau-gauce suka gaisa ya samu guri ya
zauna.
"Wai Baba kamar kukan Husna nake ji tun d'azu?"
Baba ya yi murmushin takaici.
"Eh yau kuma dukan ya juyo, kwanakin nan da yake bata wuni a gida ba zancen duka"
"Wai dan Allah Baba Alhaji baya nan ne? Ai wannan huk'uba ta yi yawa"
"Uhum wannan matar gogaggiyar 'yar duniya ce ni ina ganin ma zata girme Alhajin, kawai dai
hukuncin Allah ne mai had'i amma ai tafi k'arfinsa, kuma dan makirci har yau bai san ana yiwa
'yarsa wannan huk'ubar ba, kuma baya nan ya yi tafiya"
Tsaki Sadiq yaja mai cike da tsananin jin haushi.
"Allah ya saka mata"
"Amin"
Bai kuma wata magana ya mik'e cike da damuwa, su ka yi sallama ya koma gida idonsa ya
dawo kwalla, bai sani ba sai dai saukar hawaye ne yaji a kwance kan kuncinsa, yasa hannu ya
goge tare da cewa.
"Allah ka kawo wa wannan baiwa taka d'auki"
******
Tun daga wannan ranar Momy ta sauya salo, Husna ko falo Momy bata bari ta fito, in har ta fito
to makarantar boko zata, shima sai ta rakata har gate taga ta yi nisa da gida kan take komawa
cikin gida ta yi shirin fita, sannan tana k'ok'arin ta dawo da wuri kan a tashe su a makaranta dan
ta cigaba da b'oyeta a d'aki, ta yiwa Baba warning sosai akan Husna, har da barazanar