Showing 9001 words to 12000 words out of 81944 words

Chapter 4 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2377

gaskiya Zainab 'yar gata ce gun iyayenta da
family É—inta duka. Bayan ta kammala ci ta shiga bayi ta yi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin
riga da sket 'yar kanti, sai ga kiran Anty Jidda ta d'auka suka gaisa sannan ta yi musu bangajiya
kana ta bama Umma suka gaisa sannan ta yi musu sallama ta kashe wayar.

****** ******

*Ranar Monday*

Ta fito cikin riga da zani rafa na atamfa ta yi kyau abin ta sosai, ta yi mild make up, ta sanya
hijab fari takalmi baƙi da jaka, sai takardu da ta riƙe a hannunta, ta rufe d'akinta kana ta juya da
niyyar wucewa class, ganinsa ta yi a gabanta yana yi mata murmushi.

"Amincin Allah ya tabbata a gareki 'yar uwata, da fatan kin fito lafiya"

Ta kallesa ido cikin ido na tsawon minti uku bata ce komai ba, kana ta bi ta gefensa ta wuce, ya
shiga binta suka jeru a hanya suna tafiya ba um ba um-um, har sai da ta lalubo class d'insu
kana na shige abin ta.

"Ya mai cikar kamala ina miki fatan alkhairi ki yi karatu cikin aminci"

Ya ce yana mai kallonta, Zainab ta jiyo ta kalle shi ta yi murmushi da bai kai zuci ba ta shige
abin ta, shima sai ya saki murmushi ya ce a ransa.

'Masha Allah, haƙiƙa wannan ta yi kuma ko ba komai tana da cikar kamala da tarbiyya, lallai
murmushinki ya nuna min ina da alaman samun nasara'

Ya juya ya cigaba da tafiya, a hanya ya gamu da Nuhu suka gaisa.

"Abokina daga ina kake?"

Khalil ya sosa ƙeya yana murmushi.

"Na rako mutumiyata ce zuwa aji"

Nan ya ba shi labari, Nuhu ya shiga jinjina lamarin.

"Hmm Abokina kana son d'auko rigima to Allah ya bada sa'a"

"Yauwa gwara dai ka fad'a Alkhairi, Ameen"

Ya ba shi hannu suka tafa kana suka wuce ajinsu suma.

*Rahma ce*
[10/15, 6:48 PM] Rahma Kabir🌺: *KAƊAICI*

© *Rahma Kabir*

*Wattpad:*@rahmakabir


*_Page 9 ~ 10_*

Bayan sun fito lectures, Zainab ta samu wani dakali kasan wata bishiya ta zauna, ta dauko
wayarta dake jaka ta cire ta a silent, a nan ta ga miss called d'in yaya Al'amin da Ummanta, ta
fara kiran umma suka gaisa suka dan taba hira sannan suka yi sallama, kiran ya Al'amin ne ya
shigo da sauri ta d'auka nan ta shiga ba shi hakuri da kuma dalilin rashin d'aukar wayan da bata
yi ba, suka yi hirar soyayya kana suka yi sallama.
Kamar ance ta kalli gefenta ta ganshi ya kura mata ido ta tsuke fuska sannan ta kauda kai,
Khalil yana zaune nesa da ita kad'an duk wayan da ta yi zan iya cewa a kunnansa duka, tunda
ya hangota ya zo ya zauna yana kallon ta, gundura da ta yi da zaman wurin ne yasa ta mike
cikin yanayin gajiya ta wuce d'akinta, shima ya tashi yabi bayanta har sai da suka ida kofar
d'akin, Zainab ta juyo cike da fushi.

"Malam wai lafiya kake bina, meye matsalar ka dani?"

"Ba komai sai Alkhairi, kawai ina jinki a raina kamar 'yar uwata ce. Dan Allah ina so ki d'aukeni
kamar dan uwanki, insha Allah ba zan zame miki matsala ba ko na cutar dake"

"Na ce maka ina kalan dangi ne? ka fita a rayuwata tun kan in d'auki mataki a kan ka"

Tayi maganar a zafafe tare da jan tsaki kana ta shige d'aki ta barshi a tsaye a gun. Ya shafa
sumarsa kana ya yi murmushi.

'Uhum kyakkyawar fuska ga kuma murya mai dadi, masifar ma k'ara mata kyau ya yi'

Ya ce a ransa kana ya juya ya tafi.


*KHALIL HASSAN*
D'a ne a gurin Alhaji Hassan dan gombe, Asalinsu mutanan gombe ne, mahaifinsa ya kasance
'yan biyu Hassan da Husain, su kad'ai ne gun iyayensu, sun tashi cikin kulawa da k'aunar juna,
kasuwanci ne ya dawo da iyayensu garin Kano, sunyi karatu iya secondary daga nan suka fad'a
harkan kasuwanci, Hassan ya yi aure da Halima wacce suka hadu a kasuwa daga nan suka
kulla soyayya harta kaisu ga aure. Hussain shima ya yi aure bayan shakara uku da auren
Hassan, a lokacin inna Halima ta haifo d'anta wanda ya ci sunan kakansa Ibrahim suke kiransa
da Khalil.

Fad'i tashi dai na rayuwa ba wanda ba su yi ba kusan tsawon shekara goma wanda har a
lokacin matar Hussain bata haihu ba, hakan ne yasa Khalil ke samun kulawa da soyayya gurin
iyayensa, duk wata d'awainiyar sa Baba Husain yake masa, hasali ma gidan sa yake da zama,
ana haka ne tafiya ya kama Baba Hassan zuwa Lagos dan saro kaya, suka tafi da inna Halima,
suka bar Khalil gidan Baffansa Hussain.

Tafiya karar kwana, A wannan tafiya ce iyayan Khalil suka rasu, kan hanyarsu ta dawowa
sukayi hatsari, wannan al'amari ya tashi hankulan dangi, Khalil ya yi kuka sosai amma daga
bisani inya tuna cewa yana da wasu iyayen sai ya yi farin ciki.
Haka su Baffa Hussain suka cigaba da kula da shi, tare da kulawan kakanninsa. Baffa na kula
masa da dukiyarsa wanda iyayansa suka bar masa, sun ba shi tarbiyya sosai tare da ilimi na
addini, Khalil yaro ne mai natsuwa da hankali tare da biyayya ga manyansa, miskili ne kuma
kyakkyawa ne, yana da idanu da matsakaicin tsawo, kalar fatansa yaba da haske sai dai ba
sosai ba.

Baffa bai so sanya shi makaranta nesa ba, lokacin daya gama secondary school sunyi kokarin
nima masa jami'a a nan cikin kano, amma fir yak'i ya ce shi a Zaria zai yi karatu, ba yadda suka
so dole suka yi masa hakan, basu sha wahalar samun admission d'insa ba a bangaren da yake
so Accounting, suka kama masa gida a nan cikin Zaria nesa da makaranta sannan suka siya

masa mota ta zuwa makaranta da d'an rage zirga-zirga.
Yanzu yana matakin na 2 kenan a karatunsa 200level, yana da mai da hankali shiyasa sam
baya kula mata abokai ma baya kulasu sai Nuhu kad'ai. shima ya yaba da natsuwarsa ne yasa
suka k'ulla abota.

Zainab ita ce mace ta farko daya fara jin sonta a ransa lokaci d'aya, kuma yana ji a ransa duk
wiya duk runshi sai ya mallaki zuciyar ta. Kuma zuciyar sa na tabbatar masa da zasu rayu tare,
dan haka ne bai yi kasa a gwiwa ba yake shanye duk wulak'ancin da zata yi masa.

******
Khalil ya zamar wa Zainab chewing gum, duk inda take yana gun kamar hand bag, duk iya
masifa da bakar magana ba wanda baya sha a gunta, amma ya tsanye ya rufe idonsa kuma ya
kafe, ya zamana in dai ya shigo cikin makaranta tofa kofar d'akinta yake fara dosa, haka kuma
kullun yana kofar class d'insu, abokinsa Nuhu kullun cikin masa fad'a yake, daga karshe harya
fara ba shi tausayi yana ganin abin ya zama masa lalura, dole ya koma masa nasiha da lallashi.

****** ******

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, su Zainab sun kammala jarabawar su na third semester,
wato karshen zangon 100level, kayanta ta shirya tsaf a trolley ta rufo d'akinta, ta fara jan jakarta
har zuwa bakin gate d'in makaranta, Khalil yana tsaye yake a gefen hanya kamar yana jiran
futowarta, yana ganin ta ya matsa kusa da ita.
"Zainab na san kina farin ciki da abu uku a yau"

Kallonsa ta yi cikin harara.

"Ehen ko meye damuwar ka a kan farin ciki na, nifa bana son shisshigi gwara tun wuri ka fita
hanyata, tunda na shigo school d'in nan ka matsawa rayuwa ta, ko wani hutu in zan koma gida
da salon da kake zuwa min, yau kuma ka wani zo min da iyayi"

Ta kare maganar da jan tsaki kana ta cigaba da duba mai napep, Khalil ya yi murmushi wanda
ya bayyana fararen hakoransa.

" 'yar uwa, mai da wuk'ar Dan Allah bana son na b'ata miki rai a kan farin cikin da kike ciki,
sannan ma ai baki jira na gaya miki meye abu ukun daya saki farin ciki ba"

Ya yi Jim yana jiran me zata ce masa, amma sai ta yi masa shuru, ya cigaba da cewa

"Da farko kina farin cikin zaki ga su Umma da sauran family dinki, na biyu kuma kina farin cikin
ganin yaya Al'amin, na uku kuma kina farin cikin yin nesa dani da zaki yi na tsawon wata guda,
zaki huta da naci na da kuma surutu na"

Sai ya k'arasa masanar da fuskar tausayi kamar zai yi kuka. Bata tanka masa ba, lokacin
dai-dai mai napep ya tsaya kana ta shiga da kayanta ta zauna shima cikin azama ya zauna
gefenta, ta sanarwa mai napep inda zata ya wuce dasu, bata bi ta kan Khalil ba saboda in da
sabo ta saba da haka, dan duk hutu sai ya rakata ta shiga moka kan ya wuce shima.
Bayan sun isa ta biya mai napep harda na Khalil d'in kana ta yi shatar taxi ta biya, sannan ta
shiga gidan baya da kayanta duka, Khalil ya sun kuyo da kansa gefen windon motar ya ce cikin
sanyin murya.

"Zee na ina ni man alfarma guda d'aya a gunki, dan Allah ba dan na isa ba ki yi tunani na koda
sau d'aya ne, in har kika yi min haka zuciya ta zata gaya min, kuma zan kasance na yi hutuna
cikin nutsuwa, sannan daga k'arshe ki kula min da kan ki"

Yana gama fad'ar haka ya cire kansa daga motar ya daga mata hannu fuskar sa d'auke da
murmushi. Haka nan take kallonsa bata iya masa ko da murmushi d'aya ba sai dai idonta ya
kasa d'aukewa daga kallonsa, a haka har mai mota ya jata suka nufa cikin Kaduna.

Khalil yana barin tasha, makaranta ya koma ya dauki motarsa kana ya yi sallama da Nuhu sai
ya wuce gidansa ya had'a kayan sa, sannan ya wuce Kano.

******
Zainab tun a mota taji ta kasa sukuni tunanin Khalil ya dameta, kamar ko wani Hutu in zata tafi
da wannan yanayi take isa gida haka ma wannan karan, inta tuna wasu kalamansa sai ta yi
murmushi, in ta tuna wani abu da ta yi masa na wuk'alaci sai taji ba dad'i, a haka har suka isa
gida tana cikin yanayi na tunaninsa.

Duk dangi sunyi farin ciki da dawowarta musamman Umma da Anty Jidda, ta samu tarba mai
kyau sosai, hira suke yi na makaranta da sauran abin da ya faru a nan gida da bata nan har
zuwa dare, bayan sallah isha'i ya Al'amin yazo duk suka gaisa kana suka watse gaba d'ayansu
suka bar Zainab da yaya Al'amin, haka nan Zainab taji gabanta ya fad'i take taji bak'on yanayi
ya ziyarce ta, tunanin Khalil ne ya fad'o mata a rai, wanda har ta soma jin kamar yana ganinta,
zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, nan da nan yanayin ta ya canja, sai taji sam bata yi farin
ciki da ganin Al'amin ba.
Sun d'auki kusan minti goma a haka ba wanda ya ce wa wani uffan, mamaki ya cika yaya
Al'amin mamaki saboda ya san Zainab ba haka take masa ba a duk lokacin da ta dawo
makaranta, takan yi masa abinci mai kyau tare da nuna masa yadda ta kosa ta ganshi dan ta ba
shi labarin Exam d'insu, sab'anin yau da ko magana ta kasa yi masa sai wasa take yi da
yatsunta. Cikin yana yi na damuwa ya ce.

"My Zee"

Ji ta yi kamar ya caketa da mashi a kahon zuciya, ta d'ago kai ba tare da ta amsa ba, ya cigaba

da cewa.

"Lafiya yau na ga sauyi a tattare da ke? ki gaya min meke damunki ko kuma na yi miki laifi ne?"

"Ba komai kawai dai kaina ke ciwo"

"Hmmm kanvki na tsiwo ne zan zo na taddaki kina hira dasu Anty Jidda harda dariya, amma
suna tafiya sai kika chanza fuska, haba my Zee ki gaya min laifina sai na baki hakuri kinji"

Zainab ta saki murmushin k'arfin hali.

"Nifa ba komai, abin da na gaya maka da farko shi ke damuwa kawai"

tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye.

"Yaya Al'amin zanje na kwanta kaina ya matsa min da ciwo, gobe in Allah ya kaimu mayi waya"

Bata jira me zai ce mata ba ta yi gaba abin ta ko zata damu sassauci daga bugun da zuciyarta
ke mata.

Cike da kallon mamaki ya bita har sai da ta k'ule, zuciyarsa yaji ya takura da damuwa ga kuma
rud'ani da ya ziyarce shi.

'Allah karka jarabceni da abin da ba zan iya ba, tabbas akwai matsala kuma ina gudun
afkuwarta'

Ya ce a zuci tare da sauke ajiyar zuciya, ya fuskanci tunda Zainab ta koma wancen Hutu ta
canza masa, in suna waya ya tambayeta sai ta ce k'alau take ko ta gindawo masa da wata
maganar da zai kawar da tambayar da ya yi mata. Cikin sanyin jiki ya tashi ya tafi ba tare da ya
yiwa kowa sallama ba.
Zainab d'akinta ta shiga ta rufe, gado ta fad'a tare sakin wani irin kuka da ya kubce mata mai
ban tausayi, tambayar kanta take yi.

"Meyasa haka? zuciyata ki na niman sani a matsala, wai meke shirin faruwa dani ne?, Allah
kamin maganin abin da ba zan iya ba"

Ta ci kukanta ba mai lallashin ta harta yi shuru kana ta share hawayenta tare da shiga bayi ta
wanke fuska, ta fito ta yi shirin barci ta kwanta tare da Addu'a. Rufe idon da da zata yi ta hango
Khalil na mata murmushi sa mai kara masa kyau da kwarjini, da sauri ta bud'e idonta still abin
da ta gani idon ta rufe haka ta k'ara ganin sa a zahiri, nan da nan bugun zuciyarta ya k'aru, ta
runtse idonta sai Addu'a take yi kuka ne ya kuma kubce mata tana cewa.

"Haba Khalil me na yi maka, dan Allah karka shigo rayuwa ta, baza ka samu abin da kake so
ba"

Haka ta yita sambatu har barci ya yi awon gaba da ita da busasshen hawaye a k'uncinta.

****

*Gari ya waye*

Duk gidan sun had'u a dinning dan karyawa amma babu Zee ba alamarta, Anty Jidda ta aika
Zahra data je ta taso ta, ko da ta isketa ta fito daga wanka tana shafa mai, Zahra ta gaya mata
sakon Mamanta sannan ta wuce, k'aramin tsaki taja.

"Uhum ni ban jin ma yunwa"

Ta ce a fili ta mike ta sanya riga da wando ta sanya na fakistan, ta d'aura gyalen a kanta, ta fito
ta samesu sun kusa gama nasu breakfast d'in, kujera ta ja ta zauna ta gaida su duka kana ta
jawo plate ta shiga zuba nata, haka dai take tsakura har suka gama nasu breakfast din, sai ita
data rage harta kammala sannan ta tashi, mai aiki ta kwashe kayan kana ta gyara wurin. Anty
Jidda ta ce.

"Zainab zo muje part d'ina ki tayani gyara d'akin Sadiq anjima zai dawo"

"Ok, kin san na manta fa yana body schools ashe, amma ya kusa gamawa ko?"

"Ina fa, mutumin da yake jss 2"

"To Allah ya dawo da shi lafiya"

"Amin"

Suka wuce suna hira, a nan Zainab ke tambayar Anty Jidda.

"Anty meyasa in kamar mutum ya tuna da wani abu ko wani mutum sai yaji gabansa ya fad'i,
bugun zuciya ya rika tafiya da sauri?"

Anty Jidda ta tsaya da aikinta taba kallon Zainab.

"Meyasa kuka tambayeni?"

Nan Zainab ta shiga bama Anty Jidda labarin Khalil bata boye mata komai ba har zuwa yadda
take ji game dashi, Anty Jidda ta jinjina maganar ta ce a ranta.

'Lallai akwai matsala'

A fili kuma ta ce

"Zainab zauna muyi magana"

Duk zuka zauna suna kallon juna.

"Zainab kin tab'a jin irin haka akan yayanki Al'amin?"

"A'a ban taba ji ba"

"Zainab a iya fahimtar da na yi ma zancen ki, babu abin da ke sanya mutum yaji haka face So"

Zainab ta dago da sauri ta kalleta.

"Anty so fa kika ce? kina nufin ina Son Khalil?"

"Kwarai kuwa amma ki kwantar da hankalin ki, Zainab ina so ki sani kuma ki sanya a ranki babu
ke babu Khalil, ki nisanta kanki da shi, ki guji duk abin da zai had'aki da shi, ki tuna da akwai
baikon d'an uwanki Al'amin aka ki, wanda muna jira ki gama karatunki ne mu sha biki, ki manta
da kin tab'a sanin Khalil, saboda wallahi in har kika bari soyayyarsa ya rinjaye ki tofa akwai
babban matsala, ki ta Addu'a Allah ya cire miki sonsa da hakuri, wannan ita ce shawarar da zan
baki nima kuma zan ta yaki da Addu'a kuma insha Allah ba zan fad'awa kowa wannan maganar
ba, ki kuma daina canza ma Al'amin fuska gudun karya zarga wani abu"

Hawaye ya wanke idon Zainab, cikin shasshekar kuka ta ce.

"Anty Jidda nagode insha Allah zanyi amfani da shawarar ki da kika bani"

Nan dai Anty ta lallashe ta kana suka cigaba da aikin su.

******** ********

Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, Zainab sun kammala hutun su, a ranar lahadi ta shirya ta
wuce makaranta. Ta iske d'akinta duk ya yi k'ura haka ta yi shara ta gyara dakin tare da jera
kayanta data dawo dasu, da misalin karfe biyar na yamma, ta fito zuwa bakin gate dan ta siyo
kankana, kamar daga sama ta ga Khalil ya tsaya a gabanta, nan take ta ji gabanta ya fadi, ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login