Showing 48001 words to 51000 words out of 81944 words
Chapter 17 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
cike da kulawa, ji
ta yi kamar ana kallonta, ta gama had'a komai ta d'auki cup d'in ta juyo karaf suka yi ido hudu,
murmushi ya sakar mata mai cike da ma'anoni da yawa, ya juyawa ya isa falo ya zauna,
tsayawa ta yi tana tunano murmushin da ya yi mata, haka nan sai taji tana jin kunyarsa. Dole ta
fito falo ta mik'a masa ya amsa ya soma sha dan dama yana jin yunwa. Husna da k'arfin hali ta
ce.
"Uncle me zan d'aura maka wanda zaka ci yanzu?"
Murmushi ya yi dai-dai lokacin da ya aje cup d'in hannunsa.
"Haba my Husna kin sha aiki sosai, wannan ma da kika bani nagode kwarai, shiga ciki ki d'auko
min wayata"
To ta ce masa tare da ta shi ta wuce ciki, ta d'auko masa taba shi. Sadiq abokinsa ya kira mai
suna Yasir ya ce ya zo gidansa yana son ganinsa yanzu.
Cikin farin ciki Ya sir ya ce masa gashi nan zuwa.
Yasir abokinsa ne na gurin aiki, tunda yaga Sadiq yake shige masa dan yana burge shi saboda
natsuwarsa, shi kuma Sadiq baya son mutane miskili ne, haka yake basar da Yasir shi kuma ya
kasa fushi da abin da yake masa, a haka har suka d'an saba amma duk da haka Sadiq yaki
sakin jikinsa, saboda shi tun tashinsa bai da wani aboki kullun cikin *kad'aici* yake, ko a school
sai dai abokan karatu amma bai da Amini.
Ta b'angaren Baba kuwa Dady ya dawo da wuri, tafiyar Husna baifi da minti goma ba ya dawo,
suka gaisa Dady ya shiga tambayarsa
"Ina Husnah?"
Cike da tsoro da fargaba ya ce.
"Ta ce min zata gidan k'awarta yanzu zata dawo"
Dady ya gimtse fuska.
"Yaushe ta soma yawo haka har wata k'awa gareta, lallai Husna, mai yasa ma ka barta ta tafi?"
"Ka yi hakuri yanzu zata dawo"
Tsaki ya yi bai ce komai ba, ya fita k'ofar gida ya zauna kan bancin da Baba ke zama dan yaga
ta ina zata b'ullo, tun yana danna waya yana yi naya duban hanya, harya hakura da danna
wayar ya sanya a aljihu dan abin ya soma damunsa, domin kusan awa d'aya kenan da
dawowarsa ba Husna ba labarinta, lokaci zuwa lokaci yake yin tsaki, duk wani annurin fuskarsa
ya d'auke, Baba kuwa matsananciyar damuwa ya shiga bai so faruwan wannan lamarin ba,
yana gudun abin da zai faru.
Yasir ne ya yi parking motarsa k'ofar gidan Sadiq, ya d'agawa su Dady hannu tare da sallama
dan babu nisa tsakaninsu. Baba yaji gabansa ya kuma fad'uwa, domin har an soma
shirye-shiryen kiran sallar magrib.
Da sallama Yasir ya shiga falon cike da fara'a a fuskarsa, Sadiq ya amsa masa, ya kai dubansa
ga Husna da take wasa a system d'in Sadiq ya ce.
"Yan mata ba magana"
Da murmushi ta ce.
"Ina wuni"
Ya amsa cike da kulawa, ya kai dubansa ga Sadiq.
"Amma dai wannan sister d'inka ce ko? dan kun yi bala'in kama"
"Haba Yasir ba wani kama da muka yi"
"Hmmm ai dama kai ba zaka gani ba, amma wallahi kuna kama sosai, ko ita ce sister d'inka
Zahra?"
"Kai fa ka fiye surutu, ba wannan nake so mu yi magana akai ba, me makon ka tambayeni
dalilin kiranka da na yi, amma ka tsaya kana bincike kan abin da ba ruwanka. To asibiti nake so
ka kaini dan ban da lafiya, wallahi tunda na baro office nake kwance sai da Husna ta zo ta taya
ni shiryawa"
"Ayya sannu, Allah ya baka lafiya, to mu tafi daga nan sai mu tsaya a masallaci mu yi sallah"
"Ok, Husna tashi ki je gida kar Dady ya dawo fa"
Ai yana ambaton Dady taji gabanta ya fad'i, tama manta da gargad'in da Baba ya yi mata sai
yanzu ta tuna.
[10/29, 2:12 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 39 ~ 40_*
Da sauri ta mik'e tana cewa cike da damuwa.
"Allah yasa bai dawo ba kuwa"
Yasir ya bita da kallo ya juya yana kallon Sadiq.
"Abokina gaskiya ina ciki da k'anwarka ta yi min, ko da dai bata gama girma ba na san yanzu
bata wuce 16yrs ba"
Harararsa Sadiq ya yi.
"My Husna bata son tuzuru sai saurayi matashi amma kai ka mata tsufa"
"Tafd'i jam amma fa ka samoni, ai dani da kai duk tuzuran ne, ni dai pls ina kamu zan jirata
harta girma, gata mai kyau ta dace da sunanta"
Tsaki Sadiq ya yi.
"Kaifa matsalata da kai surutu, ban ma san meyasa na kiraka ba, da Emanuel na kira hankalina
kwance"
"Haba aboki kana sona ne ka kirani ai dan nafi Ema a gunka"
Sadiq ya yi murmushi tare da fita, Husna na biye dasu ya rufe d'aki yana k'ok'arin bud'e motarsa
yasir ya ce.
"Kai da mota nazo fa yana waje"
"Au nafa manta kana da mota"
"Ai dole ka manta tunda ba damuwa kayi da munatane ba, na zo gunka ma kana niman mini
wulakancin da ka sab"
Dukan wasa Sadiq ya kai masa.
"Yasir mai da wuk'ar, mu tafi"
Sadiq ya fara fitowa da murmushi a fuskarsa Husna na bayansa, sai Yasir daya fito karshe yana
rufe gidan.
Kamar ance Dady ya kallesu, ganin su ya yi tare da Husna wanda ita tuni ta daskare a gun tana
rawar jiki, Sadiq da bai kulaba yana cewa.
"Husna sai da safe"
Jin shurun data yi masa ne yasa shi ya waiwayo, abin da ya gani ne ya tashi hankalinsa. Wani
mugun kallo Dady ke ma Sadiq, cikin tsawa ya ce mata.
"Zo nan"
Jikinta na b'ari ta k'arasa tana kuka, wani mari lafiyayye Dady ya sakar mata a fuska, ya juya
wurin Baba ya ce cikin fada.
"Haka ake rik'on Amana, yarda da na yi da kai yasa na barta gunka ta rik'a zama, amma da
haka zaka saka min, dama na dad'e ina tunanin ta ina Husna take samu kud'in siyan kayan data
ke sawa da wasu abubuwan, ashe ta wannan hanyar take samunsu, yanzu Husna duk
kamewarki ta wannan hanyar zaki saka min ko? Dama abin da Hajiya ke fad'a kina yawo
dagaske ne? ko da yake banga laifinki ba laifi ne dana sake ki sakaka babu wani kulawa, a yau
nake dana sani akan haihuwarki da auren da na yi bisa kuskure, tunda muka yi aure da
mahaifiyarki muka tsinci kanmu a cikin matsala da tashin hankali, har na rabu da ita ban kuma
samun farin ciki ba. Ina kyautata zaton shi ne zai yi ajalina, dan dana ga irin wannan rana gwara
mutuwata kuma...."
Wani irin kwarewa yayi, numfashinsa ya sark'e tare da fidda kwalla mai zafi, bakinsa ne ya
soma fidda jini tare da dafe kirjinsa, yana k'ok'arin fad'uwa Baba yaje da sauri ya kama shi, ihu
Husna ta saki wanda ya yi dai-dai da faduwar ta k'asa a sume.
Sadiq ya yi kan Dady, Yasir kuma wajen Husna ya nufa. Da taimakon mutane suka sanya su a
motar Yasir, da gudu Sadiq ya figi motar kamar zai tashi sama, ji ya yi ya warke ba wani ciwo
dake damunsa. Sun isa Ummulkhairi hospital, aka turasu emagency, Doctor uku suka dukufa
kan Dady, Husna Doctor biyu suke kanta, tun Magrib suke abu d'aya sai kusan k'arfe takwas
likitocin suka fito tare da yarfe zufa. Su Sadiq suka tare su da tambaya, d'aya daga ciki ya ce.
"Ku kwantar da hankalinku, mun shawo kan matsalar dan yanzu barci yake yi, ku sameni a
office"
Haka suka bi bayansa, Sadiq na tsaye dan ya kasa zama, Baba da Yasir suka zauna kan
kujerun da ke kallon likita, likita shima yana zaune kan nasa kujerar tare da goge zufar dake
fuskarsa da farin hankacif, ya nisa ya soma magana.
"Bincikenmu ya nuna Alhaji yana da damuwa a zuciyarsa wanda yake k'ok'arin haifar masa da
ciwon zuciya, yanzu dai yana barci insha Allah zuwa wani lokaci zai farka"
Nan ya rubuta magani ya ce suje su siya a nan cikin pharmacy na asibitin, sannan kuma zai
cigaba da zama a asibiti yana amsar treatment har zuwa lokacin da yaji sauki, suka yi godiya
Yasir ya karb'a takardar ya ce su Sadiq su wuce gun Dady.
Likitocin da suka duba Husna sun fito tare da yima su Sadiq bayanin cewa.
"An shawo kan matsalarta, kawai firgici ne amma nan da wani lokaci zata farfad'o"
Suka rubuta magani su je su siya, Sadiq da Baba suka musu godiya sannan suka tafi.
B'angaren Momy kuwa, ta ci ado tai kyau kamar ba ita ba, sai kamshi da shek'i take yi, ta yi
wani uban d'aurin dankwali ta dawo kamar yarinya, girki ta shiryawa Dady kusan kala uku tare
da drink kala biyu, ta shirya a dinning ta gama barbad'esu da maganin da Haj. Uwani ta kawo
mata, zama ta yi a falo tana kallon TV domin jiran dawowar Dady, lokacin da taji k'arar motarsa
da ya yi parking sai wani jin dad'i take yi, shi kuma dama ya koma waje ya tsaya yana jiran
dawowar Husna, jin shuru bai shigo ba sai ta yi tunanin k'ila yana magana da wani a wajen ne,
shuru-shuru har aka yi sallar isha'i ba Dady ba dalilinsa, sai ta yi tunanin yana masallaci k'ila tun
sallar magrib.
Shurun taji ya yi yawa sai ta fara damuwa ga shi har k'arfe goma, sai ta sanya gyale ta lek'o dan
ta tambayi mai gadi, shima taga baya nan ta shiga kwala masa kira amma taji shuru, gabanta
ne taji ya fad'i ta fita k'ofar gida shuru ba mutane sai motoci da suke wucewa d'ai-d'ai, tsoro ne
ya ziyarce ta ta koma gida da sauri, cikin tashin hankali ta tsinci kanta tana cewa.
"Wayyo na shiga uku in yau Alhaji bai ci abincin nan ba, ai na yi asara kenan, ga shi duka
maganin na zuba a ciki, tunda dama sawa d'aya ne, na bani ya zan yi"
Haka ta yi ta zaman jiran dawowarsa har kusan sha d'aya da rabi na dare amma shuru. Nura ne
ya shigo gidan a bige yasha giya ya yi tatil sai wari ke tashi a jikinsa, da sauri Momy ta tarbesa
ya kusan fad'i, ta ce.
"Kai Son daga ina haka? Wai bana hana ka shaye shayen nan ba"
Surutai yake mata barkatai mara ma'ana, haka ta tallabe shi ta kai shi d'aki ya kwanta, ita kuka
ta koma falo ta cigaba da zaman jiran Dady, a haka barci ya sace ta, sai sanyin asubahi ne ya
tashe ta, ta tashi cikin rawar sanyi ta nufi d'aki.
Da gari ya waye Momy ta farka cike da damuwa, wanka ta yi ta dawo falo, d'akin Dady taje sai
ta ji shi a rufe, mamaki da tsoro ne suka kamata, tambayar kanta ta shiga yi.
'To ina yaje tun jiya bai dawo ba? kuwa ga duk kan alamu Husna ma bata nan, wai meke faruwa
ne?'
Haka ta isa wurin dinning ta bud'e abincin da ta yi duk sunyi sanyi, d'auka ta yi ta mai da kicin
da aniyar ba zata zubar ba, zata d'umama masa sai ya ci dole, dan baza ta yi asara ba.
[10/29, 6:32 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 41 ~ 42_*
*A asibiti*
Dady bai farka ba sai misalin k'arfe takwas na safe, Sadiq na gefensa yana danna waya, ajiyar
zuciya Dady ya yi wanda yasa Sadiq ya d'ago kai, ido suka had'a sai Dady ya mai da ido ya
lumshe su, da sauri Sadiq yaje ya kira likita. Baba shi yana zaune wurin Husna, Yasir kuma tun
d'azu ya tafi saboda zai tafi aiki wanda shi Sadiq ya bayar da excuse d'insa. Tare da likita Sadiq
ya dawo, likita ya shiga duba Dady tare da 'yan rubuce-rubuce kana ya ce.
"Alhamdulillah jiki ya samu, dan haka ku kula da abin da zai rik'a b'ata masa rai"
Likita ya fita can sai ga nurses sun shigo suka sanya masa drip da allurai, duk Dady na kallonsu
ba um ba um-um, bayan sun gama suka fita, Sadiq komawa ya yi ya zauna yana masa sannu,
Dady sai ya kauda kansa gefe alamar bai son maganarsa. Sadiq ya ta shi ya koma d'akin da
aka kwantar da Husna, ya samu Baba ya nasar masa Dady ya tashi har da yadda su ka yi da
likita, Baba ya yi hamdala ya ce.
"Ga jikata har yanzu bata farka ba, sai motsi kawai take yi"
"Insha Allah Baba zata farka, ya ka mata su had'a mana d'aki daya, sai kai ka je gida ka
sanarwa Hajiya, ka samu damar watsa ruwa ka huta, zuwa anjima sai ka dawo"
Baba ya yi murmushin k'arfin hali.
"Ina naga hutu Sadiqu, zan dai je na gayawa Hajiya in ya so sai na dawo"
"To shi kenan nan Baba"
Sai ya ta shi ya tafi shi kuma Sadiq ya je gun likita ya nima alfarmar a had'a Dady da Husna a
d'aki d'aya saboda su samu sauk'in jinyarsu, Da farko likita bai so haka ba amma daga bisani ya
amince. Cikin k'ank'anin lokaci aka had'a musu d'aki, gadon Dady yana chan gefe hannun dama
Husna tana gefen hannun hagu, da yake d'akin da fad'i, Dady juyowa ya yi yana kallon Husna
da ke kwance, hawaye ya gangaro masa, ya bud'e baki da kyar ya cewa Sadiq.
"Ta farka kuwa?"
Cikin damuwa ya na shi amsa da.
"Barci take yi"
Dady ya yi ajiyar zuciya tare da lumshe ido.
*******
Baba Mai gadi ya isa gida, ya samu Momy a birkice ya sanar mata Alhaji ba lafiya da Husna,
duk a asibiti suka kwana, cike da tashin hankali ta dafe kirji.
"Na shiga uku meya samesu?"
Baba bai iya mata bayani ba sai juyawa ya yi ya bata guri, da sauri ta biyo shi tana cewa ya
gaya mata in kuma ba zai fad'i ba ya gaya mata sunan asibitin, cike da damuwa ya ce.
"Ni ma can zan koma yanzu, a Ummulkhairi Hospital aka kwantar dasu"
Bata ce masa komai ba ta koma cikin falo ta shiga kicin ta had'a abincin da ta dumama na jiya
wanda take jiran Dady ya dawo ta matsa masa ya ci, aiko shi ta sanya a kwando har biyu ta fito
dasu nik'i-nik'i, ta isa wajen gate ta tari mai napep ya d'auketa sai asibiti.
Baba ya samu har an had'a su d'aki d'aya, gadon Dady ya matsa ya yi masa sannu, Dady ya
gyad'a masa kai alamar yauwa, Sadiq ne ya tashi ya ce.
"Dady me zaka ci a kawo maka?"
Ya girgiza kai alamar a'a, bai kuma tambayarsa ba yasa kai ya fita Baba ya cigaba da zama a
wurinsu, Sadiq gida ya koma ya watsa ruwa saboda jikinsa ba k'arfi ga kuma rashin barci na
jiya, kuma har yanzu jikinsa baya masa dad'i, cikin sauri ya shirya ya wuce wani restaurant ya yi
musu take away ya koma asibiti.
Momy ta shiga asibitin da kaya a hannunta da tambaya ta isa d'akin su Dady, da sallama ta
shiga, wani irin motsi Husna ta yi ta bud'e ido kamar zasu fito waje saboda girmansu, duk ba
wanda ya lura da haka, Momy ta ajiye kwandon Dady yana binta da kallo, a fuskar kamar
mutuniyar kirki, gaishe shi ta yi ya amsa da gyad'a kai ba tare da ya ce komai ba. Wani irin ihu
Husna ta saki mai ban firgici, duk wanda yake kusa da dakinsu yaji wannan ihun mai cike da
ban tsoro, ai Momy da gudu ta je gefen gadon Dady jikinta na rawa ta k'ank'ame kamar wacce
take jiran saukar bulala, Baba salati ya shiga yi, shiko Dady wani mugun fad'uwan gaba ya yi
wanda sai da ya tashi ya zauna, likitoci har biyu suka fad'o d'akin a guje domin ganin me ke
faruwa.
A dai-dai wannan lokacin Sadiq ya k'araso d'akin, ganin kowa ya yi cirko-cirko a tsaye, zama
Husna ta yi kamar ita ce, kwayar idon ta kamar zai fad'o k'asa, tana wani irin gurnani, takai
dubanta gun Momy wacce ta kasa had'a ido da ita, Husna ta yi dariya mai cike da ma'ana ta ce
cikin kakkausar murya.
"Habiba ki d'auki abin da kika shigo da shi ki fita daga cikin d'akin nan, da fatan kin gane me
nake nufi"
Momy ta yi tsuru-tsuru tana kallon ta, daga likitocin har Sadiq, Baba, Dady sun shiga rud'ani
tare da tsorata da yanabyin Husnar, cike da izza ta diro daga kan gadon ta tsaya kem, hannu ta
d'aga tana nuna Momy dasu.
"Kin d'auka ban ganin ki ne, kin aika an amso miki magani ko, kin kuma zuba a cikin abinci dan
Khalil ya ci ko?"
Ta k'arasa maganar tana murmushi tare da girgiza kai, ta cigaba da cewa.
"Na gaya miki had'uwa ta dake ba zai yi kyau ba, mashirkiya kawai, kin takuwara Husna kin
sanya mata cutar hauka, kin gallaza mata, kin muzguna mata, kin kuma raba ta da mahaifinta
mai sonta, kin shiga tsakaninsu, daga k'arshe kin had'a mata sharrin zina, k'aramar yarinyar da
bata wuce shekaru sha shida ba, tunda Khalil ya aure ki ya baki amanarta tun tana shekara uku
kike cin zalinta, kike mata tuggu da k'eta, wallahi ba zamu yarda ba tunda kika tab'a mana
Husna, mu muna sonta kuma sai mun wulakan taki"
Kuka Momy ta fara yi tana cewa.
"Wallahi sharri kike min, Alhaji karka yarda da maganarta karya take yi"
Wani irin zabura Husna ta yi ta isa gurin Momy kamar walk'iya, ta damk'i wuyan Momy ta matse
iya k'arfinta,