Showing 75001 words to 78000 words out of 81944 words

Chapter 26 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2390

ta tsinci kanta a
ciki.

Falon ya yi tsit kamar bakowa aciki sai k'aran fanka dake juyawa, Baffa ya ce.

'Sadiq bani number Khalil"

Jin haka mamaki ya kuma cika Sadiq, ba musu ya karanto mishi number daga wayansa, Baffa
ya yi dialing number a wayarsa ta soma ringing, bugu biyu Dady ya d'auka ya kara a kunnensa
tare da sallama, suka gaisa, Dady ya ce.

"Amma Alhaji ban wayeka ba, ko zaka min bayani domin number nagani"

Baffa ya yi jim da yake wayar yasa a hand's free duk mutanan falon suna ji, Baffa ya ce.

"Sunana Alh. Ahmad mai kanti, Baffan Zainab"

Ai kan ya k'arasa fad'a cikin Dady ya yi kulululu, saboda bai tab'a tsammanin haka daga dangin

Zainab ba, ya nisa ya ce.

"Baffa ka yi hakuri ban wayeka ba ne da farko"

Nan ya kuma gaishe shi cikin mutunci.

"Khalil in ba damuwa ka zo Kaduna yau ina son ganinka a gidana, wancen karan mune muka
kore ka, wannan karon kuma ina mai baka hakuri ka zo dan Allah ba dan abin da muka aikata
maka ba"

Jikin Dady ya yi sanyi ya ce.

"Baffa ai kai uba ne a gareni, ba sai ka bani hakuri ba zan zo insha Allah yanzu, da fatan dai
lafiya?"

"Lafiya lau"

"To ganin zuwa"

Nan suka yi sallama suka aje kan wayar. Cike da mamaki Khalil yabi wayar da kallo, cikin sauri
ya ta shi ya kimtsa, part d'insu Baba Husain ya je ya sanar musu da abin da ke faruwa, ai nan
Baba Husain ya ce da shi za ayi tafiyan, Inna ma ta ce da ita za ayi, cikin k'ank'anin lokaci suka
shirya sai Kaduna.
*****
A nan falon kuma Baffa ya ce kowa yaje ya natsa har kafin zuwansu Dady Kaduna, ba musu
kowa ya mik'e cike da jimami da tunanin wannan bak'on lamari mai cike da abin mamaki, ta
b'angaren Zainab kuwa ta kama hannun Husna don suje part d'inta amma tak'i yarda, dole Anty
Zainab ta rabu da ita ta wuce d'akinta tana mai zubda kwalla, Mami Ameena dasu Umma
tausayinta ya kama su, Abba Ismail da Abba Aliyu kuwa a yau suka k'ara dana sanin raba
aurenta da suka yi da Khalil, ga shi ba aje ko ina ba Allah ya nuna musu ikonsa.


Da misalin k'arfe biyu na rana su Dady sun iso, da yake motar gida ne kuma tafiyar sauri suka
yi, anyi musu masauki a babban falon gidan kana aka cika su da abinci kala-kala da abin sha,
Suka d'an ci, kana Baffa ya fito suka gaisa cikin mutunci sannan ya d'auki waya ya sanar da duk
mutanan gidan da su fito babban falo, d'aya bayan d'aya suka soma shigowa, Sadiq ne suka
shigo shi da Husna, Dady ya kallesu cike da mamaki ya ce.

"Kai Sadiq meya kawo kunan dama kasan mahaifiyar Husna ce?"

Tambayar daya jeho masa, sai ya k'ara rikita Sadiq, idonsa sun yi ja ya ce.

"Dady nima na kasa gane wannan sark'ak'iyar, nan gidan family house d'inmu ne"

Cike da mamaki Dady ya ce.

"What"

Sai ya bi 'yan falon da kallo bai ga Zainab ba, Baffa ne ya ce.

"Kuyi hak'uri komai zai warware yanzu, wai ina Zainab ne? Ke khadija ta shi ki je ki kirata..."

Baffa bai rufe baki ba sai gata ta shigo kamar an jehota, har wata 'yar rama ta yi na damuwa,
tsayawa ta yi cak ta kasa k'araso wa, Dady ya kura masa ido ko kiftawa baya yi, ita ma shi take
kallo hawaye na malala a kuncinta, shima Dady hawaye yaji ya cika masa ido sai ya yi na maza
ya danne su dan karsu zubo, ya mai da kallonsa ga Husna da ta takure a jikinsa ya ce.
"my Husna ta shi ki je gun Mahaifiyarki"

Cikin razana ta d'ago kai tana kallonsa.

"Dady wacece Momy na?"

Ya nuna mata Zainab da hannu.

"Gata can a tsaye jeki shigo da ita cikin falon"

Ido bud'e cike da tsoro take kallon mutanan falon, Baffa ne yasa baki ya ce.

"Jikata je ki wurin Mamanki, ita ce ta d'auki cikinki na wata tara kana ta yi nak'udarki kika zo
duniya"

Cikin mutuwar jiki Husna ta mik'e tana kuka tare da jan k'afa don ta isa gunta, ji ta yi k'afarta ba
zai d'auketa ba ta tsaya cak cikin tsakiyan falon, kanta ne taji yana juyawa ya yi mata nauyi
kamar ba nata ba, wani razanan nan ihu ta saki ta fad'i k'asa sumammiya.

Dady, Sadiq, Anty Zainab, Abba Ismail, Abba Aliyu, dasu Anty Jidda, Umma da Mami Ameena,
suke yi kanta da gudu har suna bangazan juna, Dady ne ya ce a kawo ruwa, aka kawo ruwa
kana ya zuba a kofi ya yi tofin Addu'a a ciki ya soma watsa mata a jiki da fuska, wani k'aran ta
saki, ta ta shi zaune tana huci tana furzar da miyau ta ce kakkausar murya.
"Karku k'onani ni masoyiyarku ce, bana nufin cutar da kowa, dan Allah ku rabu dani"

Dady ya ce.

"To ki tafi ki rabu da rayuwarta in dai ke musulma ce"

"Eh ni musulma ce, na shiga jikinta tun tana k'arama ni ke bata kariyar wasu abubuwa saboda
rayuwar *kad'aici* data ke ciki"

Nan ta yi ta surutu, ta k'ara basu labarin yadda Husna ta yi rayuwar *Kad'aici* da rashin gata, ta
nuna su Abba Ismail da Abba Aliyu ta ce.

"Duk kune kuka ja komai, kuka rabata da mahaifiyarta, kuka raba musu aure, harda kai Baffa
saboda wani ra'ayinku na daban"

Nan dai ta yi ta surutu daga bisa ni ta ce.

"Dama wannan rana nake son gani in ga Husna ta ga mahaifiyarta, dan haka zan tafi ba zan
sake dawowa gareta ba dama rayuwar *kad'aici* da take ciki ne yasa na shigeta, na tafi, na tafi"

Husna ta saki wani ashiwa mai k'arfi sai ta koma luuuu zata fad'i, Sadiq ya tare ta da hannunsa
ta fad'a jikinsa.

Ta kai minti biyar a haka kana ta ta shi tana waige-waige, caraf ta had'a ido da Mominta cikin
kuka ta ta shi zaune, da rarrafe ta isa wurinta ta rungumeta kamar zata koma cikin cikinta, wani
nannauyar ajiyar zuciya duka suka saki, kana Zainab ta d'agota suna kallon juna suka sakarwa
juna murmushi, Husna ta ce cikin shagwaba.
"Momy dama kina raye? ki min alk'awari ba zaki sake nesa dani ba, na yi kewar ki ba adadi"

Cikin nuna so da k'auna Zainab ta ce.

"Wace ni, ai muna tare mutu ka raba 'yata"

Duka falon suka sa dariya, amma banda Dady daya sha kunu, ko meye dalili oho.
[11/5, 8:38 AM] Rahma Kabir🌺: *_Page 65 ~ 66_*


Nan suka kara gaisawa daga bisani Baffa ya d'aura da cewa.

"Sadiq da Husna ina so ku sani ku 'yan uwa ne, Zainab ita ce mahaifiyar Husna, Aliyu shi ne
mahaifin Sadiq wato yayan Zainab kenan"

Daga nan ya d'aura da bayanin yadda auren Zainab da Khalil ya faru, bayan ya kai aya Yasir ya
d'aura da bayanin yadda ya had'a auren Husna da Sadiq, aiko Dady ya cika da mamaki da
jinjina wannan lamari na Allah, wanda babu wanda ya isa ya yi shi sai shi kad'ai Allah mabuwayi
gagara misali, wannan kad'an kenan daga cikin ikonsa in yaso ya had'a ko ya raba, babu abin

bautawa da gaskiya sai shi kad'ai Allah, wanda babu wani bayan shi. Falon ya d'auki shuru
kowa na jinjina wannan abin ta'ajibi hak'ik'a aya Allah ya nuna musu domin shi da ya had'a shi
kad'ai yasan dalilin had'awar, su Baffa sun amshi kunkurensu kanma Abba Ismail da Abba Aliyu
da suka yi ruwa su kai tsaki akan raba auren Zainab da Khalil, Sadiq ya jinjina lamarin a she
iyayensa sune masu lafi dumu-dumu, sannan kuma shiyasa yake jin Husna a a zuciyarsa
tamkar jini da tsoka, ya yi murna da aurenta ya zama silar had'uwar dangi da kuma nunawa su
Abba kuransu.

Nan Khadija ta matsa kusa da ita ta ce.

"Husna shiyasa nake jinki sosai a raina a she ke 'yar uwa ta ce, nagode Allah da yasa kika
zamo cikin ahalina, kuma a yau nake sanar da cewa, na hakura da auren Yaya Sadiq, na bar
mini shi har abada dan ba zan iya miki butulci ba"

Nan falon ya gauraye da murna suka shiga sanyawa Khadija albarka, Yasir ne ya sunkuyar da
kai ya ce.

"Baffa ni fa ina kamu dan ina son Khadija"

Baffa ya yi dariya.

"Madallah, Yasir na baka ita amma fa sai ta amince, dan yanzu mu dangin nan namu babu mu
ba auren dole, ko wani naji zai yi haka sai na masa nasiha ya gane illan yin hakan"

Khadija cikin jin kunya ta sunne kai k'asa, Husna cikin dariya ta ce

"Baffa ita ma ta amince tunda ga shi sai dariya take yi"

Duka Khadija ta kai mata ta ce.

"Wayyo Momy na kin ganta ko"

Nan falon ya cike da dariya, sai hira da raha suke yi da murna, sannan suka yafi juna bisa abin
da yafaru a baya. An kira Sallan la'asar dole suka mik'e dan gabatar da sallah. Falon ya watse
mazan suka nufi masallaci su Umma suka shiga ciki, musamman aka gyarawa su Baba Husain
wani part a gidan. Zan iya ce muku wannan family sun kwana cikin farin ciki mara misaltuwa
wanda suka jima ba suyi ba.

*****
Ranar Juma'a bayan an sakko masallaci aka d'aura Auren Zainab da Khalil su Baffa suka yi
komai hatta sadaki, sannan aka kuma d'aura Auren Khadija da Yasir wanda Dady shi ne ya yi
masa wakilci ya biya sadaki da komai, sannan aka d'aura Auren Zahra k'anuwan Sadiq da
angonta Jabir wanda suka jima suna soyayya. an kira dangin Yasir an sanar musu,

mahaifiyarsa ma ta zo nan Kaduna da kannensa da wasu danginsu.

Bayan an d'aura Aure aka shirya gagarumin liyafa a wani babban hol dake nan Kaduna, wanda
sai wanda suka jik'e da naira suke shagalin biki a gun. Zainab ta yi kwalliya kamar ba ita ba sai
wani tseki da kyalli take yi, Dady shima ya yi kyau fuskansa cike da murna amma fa suna had'a
ido da Zainab sai ya gimtse fuska ya galla mata harara, murmushi take masa domin ta san
dalilin hararen saboda taki bari su kebance shiyasa yake cin magani, su Husnahm kuwa murna
baya misaltuwa sai wani dad'i take ji ta mance komai na rayuwarta ji take kamar an sake haifo
ta ne saboda farin cikin da take ciki, haka gogan naku Sadiq fad'en farin cikinsa ma b'ata baki
ne sai wani murmushi yake yi, a fagen rawa kuwa sun cashe shi da Husnarsa kamar ba suba,
ni kaina na yi mamaki nace ashe dama su Sadiq suna dariya haka sai wani rawa suke na
burgewa. Ango Yasir da Amarya Khadija abin ba'a magana dan bakinsu ya kasa rufuwa, sai iya
yi su keyi su Khadija dama ba kunya sai rawar kai, suma kam sun yi kyau kuma sunyi matching
sosai, su Zahra ma da Angonta ba'a barsu a baya ba, sun yi kyau kuma suma sun cashe sosai
abin gunin sha'awa, anyi shagali an washe duk sun dawo gida.

******* *******

*Washe Gari*

Aka shirya Momy Zainab tare da Amarya Khadija domin kaisu gidan mazansu a Kano, su Sadiq
ma ba'a barsu a baya ba suka kwashe komatsensu suka bi sahun Amare. Amarya Zahra a nan
kd aka kai ta gidanta dake marafa.

Kusan duka gidan aka dunguma sai Kano hatta su Baffa sun bisu dan suga wurin dasu Khalil
suke zama da kuma Husna, suna isa suka dire a gidan Dady, wanda danginsa sun cika gida
dan tarban Amarya, Momy Habee cike da mamaki take kallon su, an sauke Momy Zee a part
d'in Dady wanda ya sha gyara duk an canza kayan d'akin an zuba sabbi, Zainab ta kalli d'akin
da kyau ta ce.

"Hmmm yau naga auren gata, ji yadda aka kashe kud'i sai kace wata budurwa"

Mami Ameena ta yi dariya ta ce.

"Wannan aikin mijinki ne ba kud'in Baffa a ciki, kuma ai ke yanzu 'yar gata ce kuma kamar
budurwar kike a gunsa"

Ta lumshe ido ta yi murmushi kana suka ci gaba da hira.

Bayan komai ya lafa suka had'u a babban falon gidan, Dady ya ce
Husnah ta kira masa Haj. Habee, Husna taja hannun Khadija suka isa part d'in Momy Habee,
sun sameta gefen gado tana zaune ta zabga tagumi, cikin murna Husna ta isa wurinta ta ce.

"Momy ina yini"

Firgigit ta d'ago kai ta ce.

"Husna yaushe kika zo?"

"D'azun nan muka zo, Dady ya ce ki zo falo mun yi bak'i"

Haka suka dunguma suka isa falon, Momy ganin bakin falon yasa jikinta ya yi sanyi, gefen can
ta samu ta zauna ta soma gaishe su, sannan ta kai kallonta ga Dady ta ce.

"Alhaji gani"

"Yauwa, Habeeba ga dangin mahaifiyar Husna nan, wannan ita ce Zainab wato mahaifyar
Husna jiya aka mai da Aurena da ita, dalilin kiran ki da na yi dama shi ne, na shaida miki cewa
Husna bata hanyar zina na sameta, saboda kinsa fad'ar haka"

Momy idonta na kan Anty Zainab tana mamakin kamarta da Husna, sun kuyar da kai ta yi cike
da jin kunya, kwalla ne ya cika mata ido har ya zibo ta soma hawaye ba tare da sauti ba, ta
d'ago ido wanda suka rine suka yi ja ta ce.

"Dan Allah ku yafe min bisa ga mugun rik'on da na yiwa Husna sharrin shaidan ne da zuciya,
alhakin ta ma nasan Allah ba zai barni ba"

Ammi Jidda ta ce.

"Ba zamu yafe ba munafuka"

Umma ce ta katseta.

"Haba Jidda ai muma muna da laifi dan haka ke Habeeba kike ko wa, ki je mun yafe, Allah ya
yafe mana gaba d'aya"

Duka falon suka amsa da Ameen. Baffa ma ya d'aura da nasiha da kuma jan hankali game da
amana da daraja dan Adam. Nan Dady ya musu bayani cewa.

"Idda Momy Habee take yi a gidan dan ya saketa, kuma da zarar ta gama zata tafi"

Kuka ne yaci k'arfinta ta tashi da gudu ta nufi d'akinta. Duk sai tausayinta ya kama su amma fa
banda Dady, Nan sukaci suka sha.


Da yamma aka d'auki Khadija aka kai ta gidan mijinta, wanda gidansu daya da Husna d'ayan

part d'in Sadiq yasa aka gyarawa Yasir dan su zauna tare kafin Sadiq ya gama gininsa. Da
yamman nan su Baffa suka koma Kaduna akabar gida kowa ya watse sai masu gidan.

Husna sai dare Sadiq ya zo ya d'auketa suka nufi gidansu. Suna isa part d'in Khadija ta nufa,
Sadiq ya zauna a barandar gidan kan kuje ta yana jiran zuwan Ango da abokansu.
Bayan sun k'araso aka yi siyan baki kowa ya kama kansa. Khadija har da kuka wai Husna ba
zata tafi ba da kyar ta saketa ta wuce part d'inta. Ta samu ta watsa ruwa ta yi shigan barci da
shegun wani rigan barci ruwan hanta iya karta rabin cinya ya tsaya mata, ta d'aura k'afa d'aya
kan d'aya a kujera tana kallon TV tare da shan ice cream da Sadiq ya siya mata a hanya.
Gogan naku shima ya fito da wani wando tree quarter sai riga mai guntun hannu fara tas,
wandon ma fari, da murmushi ya k'arasa wurinta ita ma tana mayar masa da martani, yadda
suke jefar junansu da wani sihirtaccen kallo da gani kasan sunyi missing juna, yana zuwa ya
karb'e robar ice cream d'in ya ce.

"Baby Hussy bana so mura ya kamin baby na dake cikin ki"

Da wani irin kallo ta bi shi ta ce cikin sigar kallon d'aukar hankali.

"Nifa ban isa haihuwa ba"

Dariya ya yi ya jawota jikinshi ya ce.

"Ok na ji, amma bari naji da kyau in baki isa ba"

Jawota ya yi jikinsa tana mutsu-mutsu tana son zillewa, matseta ya yi a jikinsa, kafin ta yi aune
ya had'e bakinsu waje d'aya tare da sarrafa harshensa a ciki, tuni ta saki jiki ta suka fad'a wani
duniyan, ina ganin haka nima na kama kaina na nufi gidan Dady.

Na tadda Dady da Momy Zee sun idar da Nafila na godewa Allah daya k'ara nuna musu
wannan rana a matsayin ma'aurata, nan Dady ya ce.

"Zee na"

Ta d'ago ta kalleshi tare dayi masa fari da ido ta ce.

"Naam my Khalil"

Lumshe ido ya yi ya bud'e, ya mik'e tare da yin shirin barci, d'aukanta ya yi chak ya direkan bisa
kan gado yana mai fidda nishi ya ce.

"Kai my Zee kin ji yadda kika k'ara girma, gaskiya da alama ko tunani na ba kya yi, ni kam ji
yadda na lalace tunda na rabu dake ban sake farin ciki ba, sai ranar dana aurar da Husna da
kuma ranar yau"

Murmushi ta yi ta ce.

"My Khalil kusan kullun dare sai na zubda kwalla, da tunaninka nake kwana wasu lokutan harda
mafarkinku nake yi kai da Husna, kullun Addu'a nake Allah ya sadani daku cikin aminci, kuma
ina ji a jikina zan had'u daku, shiyasa tun mutuwar yaya Al'amin nak'i yin Aure, na samu
manema sosai amma nak'i yarda, su Umma sunyi mita sun gaji haka suka hak'ura suka cigaba
da min Addu'a, kaga kuwa kana raina Mijina"

Khalil cike da farin ciki ninke a zuciyansa ya rungumeta tsam har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login