Showing 78001 words to 81000 words out of 81944 words
Chapter 27 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
suna jiyo bugun zuciyan juna,
tuni suka farfad'o da soyayya, suka fara tuno tsantsar soyayarsu ta da, take nan suka fara
faranta ran junan had'e da nunama juna tsantsar missing da suka yiwa juna. Ganin wannan
yana yi da suka shiga na shayar da junansu zumar kauna, sai nima na lallab'a nayo waje dan
sanin sirrin ma'aurata sai Allah.
Ta b'angaren Amarya Khadija da angonta Yasir da amarya Zahra ita ma da angonta Jabir, suna
can suna gwangwaje soyayya mai cike da so da kauna da tarin tarihi.
To ma'aurata Allah ya baku zaman lafiya. Ameen.
Su Baffa suma sun kai Kaduna kowa ya kwanta yana huta gajiya. ta b'angaren su Baba Husain
suma suna part d'in su sun kwanta suna huta gajiya.
Ta wajen Momy Habee kuwa barci ya k'aurace mata sai jiyu take, ta yi kukan ta gaji, nadama ya
cika zuciyarta, tana tunanin yadda taga mahaifiyar Husna sai da ta raina kanta, gata matashiya
kuma ga kyau ta had'a komai da namiji yake so, a yanzu ta kuma sadak'arwa Khalil ya mata
nisa, tasan tunda ya mai do da Zainab tofa ba wata mace da zata kuma samun k'ofa a
ziciyarsa. Da tunani barkatai barci ya yi a won gaba da ita.
[11/6, 6:42 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 67 ~ 68_*
*Bayan wata d'aya*
Khalil da Zainab suna ragargaza love hankalinsu kwance ba ruwansu da wani, hakan yasa
Momy Habee ke yini a d'aki saboda sam bata sakewa in suna babban falo, domin idonsu
rufewa yake su yi ta soyewa ba ruwansu da tana wurin, Momy Habee har mamaki take yi yadda
taga Khalil ya saki jiki sai soyayya yake yi ga fara'a da sakin fuska ba kamar yadda yake mata
ba, lallai ta san ita ya aureta ne dan kawai ta tusa kanta ne ba dan soyayya, tunani ta farayi na
barin gidan domin hakan shi ne samun kwanciyar hankalinta.
Zainab tana falo zaune bisa kujera tana nazarin wani littafi sallama ta ji anyi tare da shigowa,
Husna ta isa da gudu ta rungumeta suna murna sosai da ganin juna, in kuka gansu sai sun
baka shawa'a, Momy Zee ta ce.
"D'aga ni karki karya ni, ina shi Sadiq d'in ya tsaya bai shigoba?"
Husna dariya ta yi, ta d'aga mata d'in key mota ta ce.
"Da kaina na zo"
Ido Momy Zee ta zaro.
"Yaushe kika iya tuk'i"
"Uhum shiya koya min, kuma wallahi na iya, zo mu je ki d'ana sabon motata da Uncle ya siya
min na zuwa makaranta"
"Kai masha Allah, Allah ya sanya alkhairi, muje na gani"
Haka suka fita haraban gidan ta bud'e mata tana gani, Momy ta yaba sosai da motar, ta yi mata
Addu'a.
"Gaskiya na ji dad'i sosai dota Allah ya yiwa my Son Albarka"
Husna tana mirmushi ta amsa da amin, Momy Zee ta ce.
"Wani course zaki karanta?"
Husna ta kanne ido d'aya ta ce.
"Pharmacy nake so"
Momy zee ta zaro ido cikin wasa ta ce.
"Gasa kike yi dani ko?"
Husna ta kwashe da dariya.
"Haba Mom in rasa wanda zanyi gasa da shi sai ke, kawai ina so ne saboda tun ina k'arama
nake son shi a raina"
"To shi kenan, Allah ya taimaka ya bada sa'a, ita Khadija fa?"
"Eh tare zamu rik'a zuwa, ita biochemistry zata karanta"
"To masha Allah, Allah ya Baku sa'a"
"Ameen Mom"
Suka jera suna hira har suka shiga cikin falo, suka zauna tare da cigaba da hira gwanin ban
sha'awa.
Momy Habe tana d'aki ta zabga tagumi abin duniya ya isheta, TV na kunne yana aiki amma
bata iya gane mai ake yi ba, saboda ta fad'a duniyar tunani, tashan liberty tv ne suna nuna
labarai, gawarwakin mutane uku a ka nuna duk maza da alama ana cigiyar ko za a samu 'yan
uwansu, kamar ance Momy ta kalli TV, haka nan taji fad'uwar gaba ta kurawa tv ido, bata iya
fahimtar me suke cewa illa bin gawarwakin da ta yi da kallo, wani zabura ta yi ta murza idonta
da hannunta domin ta tabbatar da abin da take gani, ilai abin da ta gani gaskiya ne babu karya
a ciki Nura ta gani kwance cikin jini ba rai, hannu ta aza akai ta tsandara wani wawan k'ara,
wanda duk yake gidan nan sai da yaji, a gigice Momy Zee da Husna suka rankaya zuwa d'akin
Momy Habee, cike da kad'uwa Momy Zee ta ce.
"Hajiya lafiya?"
Kuka take rusawa tare da nuna musu tv da hannunta, bin tv suka yi da kallo, Husna na arba da
hoton fuskar Nura ta ji kamar an cikareta, ita ma kuka ta fashe da shi tana fad'in.
"Momy Ya Nura ne, innalillahi wa inna ilai hir rajiun, yaya Nura ne"
Da gudu ta fita falo duk su Momy suka rufa mata baya, wayarta ta d'auka ta shiga kiran Dady,
bugu d'aya ya d'auka ya kara a kunne ya ce.
"My sweet dota"
Kukanta da yaji shi ne ya hana shi k'arasa maganar da zai yi cike da kad'uwa ya ce.
"Husnah lafiya?"
Cikin kuka ta ce.
"Dady yaya Nura ya mutu yanzu aka nuna a TV"
Gabansa ne yaji ya fad'i, ya mik'e cikin sauri.
"Wani asibiti suka ce yake"
"Asibitin Murtala"
Bata jira mai zai ce ba ta kashe waya.
Kan a ce miye dangi da mak'ota sun samu labarin mutuwar Nura, gidan ya soma cika da
mutane. Cikin k'ank'anin lokaci a asibiti aka bama su Dady gawar Nura suka dawo gida aka yi
masa sutura, Momy ne zuk'unne gaban gawar tana kuka mai ban tausayi, hatta Dady a yau yaji
tausayinta ta ce.
"Nura kaine kad'ai kwai na a Duniya, ga shi ka tafi ka barni a lokacin da nake buk'atarka, ina
tsoron had'uwata da Allah da kuma mahaifinka saboda ban baka yarbiyya na kwarai ba,
kaitsona na zamo nurasar uwa mara tsoron Allah, hak'ik'a alhakin Husna ce ya ke bibiyata,
Allah ya gafarta maka yasa ka yi mutuwar shahada, d'a na ka yafe ni"
Wata 'yar uwanta ne ta dafata tana bata hak'uri cike da tausayawa, haka aka d'auke shi Momy
Habee tana ihu had'e da sambatu marasa kangado. Ankai Nura makwancinsa an barshi da
halinsa, tom mu dai sai muce Allah ya jikan duk kan musulmi Ameen.
******
*Bayan kwana bakwai*
Anyi sadakar bakwai kowa ka ganshi yana jimamin mutuwar Nura, domin labari ya ishe kowa
akan hanyan da ya mutu. Sun je club ne sunyi shaye- shayen kayan maye sunyi tatil, tsautsayi
bata wuce ranar ta, wani a cikin abokansu ya ce su zo suje wani club akwai wata kawarsa tana
birthday, cikin maye suka shiga mota dan suje su hole da mata, motan ne ta kubcewa mai
tuk'asu suka fad'a wani rami, dukansu babu wanda ya shura suka ce ga garinku nan, jami'an
tsaro sun kawo musu d'auki, ko da aka kaisu asibiti sun riga sun mutu. Dan haka kowa ke
tausayawa ake musu fatan samun Rahma, Momy Habee har wata k'aramar hauka ta yi da kyar
aka samu ta daina kuka, da yamma 'yan uwanta suka tattarata suka wuce da ita gidansu, gaba
d'aya Momy ta zama abin tausayi ta zama shuru-shuru, magana sai ya zama dole take yi,
nadama kam Momy ta na cikinsa a kullun Addu'a take Allah ya gafartwa Nura ya yafe mata
kura-kuran data aikata.
****** **** ******
Bayan Addu'ar arba'in 'yan uwanta suka zo suka kwashe kayanta duka domin ta k'arasa iddanta
a gidansu, ta yi sallama dasu Momy Zee da Dady, Dady ya bata mak'udan kud'i danta juya su in
kuma wani bukata ta taso mata ta zo ta same shi insha Allah zai taimaka mata, da godiya cike
da jin kunya ta tafi.
*********
*Bayan wata d'aya*
Momy Zee ta soma laulayi abu kamar wasa Momy Zee da ciki, farin ciki wurin Dady baya
misaltuwa, ita ko kunya taji wai da girmanta tana da ciki, Dady yana ta mata dariya da zolaya.
"Ai da sauranki ma a haihuwa dan baki gama ba ki shirya jero min 'ya'ya tagwaye say uku"
"Dear ka rufa min asiri, Husna da Al'amin sun ishe ni"
Da yake little Al'amin ya dawo nan Kano, Dady ya rok'a a basu shi ya zauna wajensu.
Ta b'angaren amare suma duk sun kamu suna da ciki, Husna ce dai abun shuru tana ta
karatunta. Anty Binta ma Allah ya amshi Addu'arsu ita ma ta samu ciki, farin jiki wajensu ita da
mijinta Mustapha baya misaltuwa, haka dangi sunyi san barka da Addu'an duk Allah ya saukesu
lafiya.
******
Cikin Momy Zee na wata shiga Husna ta soma laulayi, su Khadija suma suna ta ja da cikinsu
suma da yake wata shiga nasu yake, da Zahra ma, Anty Binta ne mai cikin wata biyar. Tun da
Sadiq yaji Husna na da ciki ya soma nan-nan da ita kulawa ta musamman komai shi ke mata
hatta wanka, makaranta kuwa shi ke kaisu ya dawo dasu. Yasir shima ba baya ba dan shima
Khadija tana samun kulawa ta wajensa, ta bangaren Dady kuwa abin ba'a cewa komai.
Momy bayan ta gama Idda ta auri wani Dattijo mai Suna Alh. Tukur lecturer ne, kuma cikin ikon
Allah ta natsu a d'akinta suna zaman lafiya da mijinta, matsala d'aya take samu wajen kishiyarta
da yaranta, amma dai tana hakuri tare da kau da kai bata kulata, kishiyar nata ganin ga yadda
Momy Habee take bata kulata sai ta sauko suka cigaba da zama lafiya da mutunta juna. Takan
kawowa Momy Zee ziyara dan yanzu suna zumunci.
Ta b'angren gidan Abokin Dady Alh. Ahmad, zumunci ya kullu da Momy Halima da Momy Zee,
sun zama kawaye sosai, Auren Minal da Mujaheed abokinsu Yasir, ya taso su Momy Zee dasu
aka sha biki, su Husna da Khadija sune kawayen amarya, ita ma ta tare a gidanta mai kyau
suka angonce abin sha'awa.
*******
Cikin Momy Zee ya shiga wata tara da sati d'aya ta haihu 'yan biyu duk maza, farin ciki kamar
me a wajen Dady, Momy ta ga So da K'auna a gurin Dady, da kansa yake zama ya bata abinci
ya taya ta kula da yara, har hutu ya d'auka a wajen aiki. Husna da Sadiq kuwa farin ciki a
wajensu baya misaltuwa ita ma tarewa ta yi a gidan tunda aka yi haiguwar. Ta b'angaren dangi
kuwa suma ba baya ba 'yan Kaduna sai zarya suke na zuwa barka, Ammi Jidda, Mimi Amina,
Anty Binta duk sun zo ana saura kwana biyu suna, su Inna suna ta karb'an baki, Baba Husain
har kuka ya yi ya ce.
"Ashe zanga takwarana"
Ya tuna da d'an uwansa mahaifin Khalil daya rasu suma 'yan biyu ne, shi ya yiwa yaran hud'uba
aka bar musu sunansu Hassan da Husaini, ranar suna an ci an sha, su Momy Habee harda
kayan barka ta kawo, Zahra tana cen bata samu zuwa ba domin tana gab da haihuwa. Haka
Khadija ita ma ta zo suna amma bata iya komai zaune take da tsohon ciki turus, Husna sai tsiya
take mata, Husna ita ma cikinta ya fita tana wata na shida ya yi mata das a jiki, ta k'ara kyau
Sadiq kamar ya lasheta dan So. Anci suna an watse koya ya koma gida an bar mai jego da
yaranta da Dady mai taya ta raino. Inna ce ke kula da mai jego ta bangaren wanka dana yara.
***
Bayan sati d'aya da suna, Zahra ta haihu 'ya Mace mai kyau ta yi kama da ita, ranar suna
yarinya ta ci sunan mahaifiyar mijinta Aisha suna kiranta da Nasreen, anci ansha an washe taro
lafiya. Bayan sunan Zahra da kwana biyu Khadija ta haihu itama an samu d'a Namiji, murna
wajen Yasir ba a cewa komai Momyn sa ta yi murna sosai da 'yan uwa gaba d'aya, daga Asibiti
aka wuce da ita gidansu Dady, part d'in Inna a can zata zauna, Inna na kulawa da ita har ta yi
arba'in, Yasir bai so haka ba amma ya ya iya tunda anfi k'arfinsa, mutanan Kaduna nata zuwa
barka, wannan karan harda Baffa ya zo ganin yaro da kuma 'yan biyun Momy Zee, Umma ma ta
zo sai da a ka yi suna ta koma, Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifin Yasir wato Muhammad
Auwal suna kiransa da Na'im, anyi taro lafiya an watse kowa ya koma gidansa.
****** ******
*Bayan kwana arba'in*
Su Khadija sun yi arba'in, Inna ta gyara ta sosai ta koma gidanta, Momy Zee ita ma ta yi arbain
da sati biyu kenan ta cigaba da kula da mijinta da yaranta, su Inna kusan yaran wurin su suke
yini, sai suna buk'atar nono ne ake kai mata su.
Anty Binta itama ta haihuwa ta samu Namiji yaro mai kyau mai kama da Babanshi, ranar suna
yaro ya ci sunan Baffa wato Ahmad suna kiransa da khalifa, anyi suna an waste lafiya. Haka dai
rayuwa ya cigaba da tafiya, wannan dangi suna cikin farin ciki da K'aunar juna.
***
*Bayan wata uku*
Da haihuwar su Momy Zee, Cikin Husna ya kai wata tara da kwanaki, ranar juma'a da yamma
ta fara nak'uda, Sadiq yana tambayarta lafiya? ganin yadda take ya mutsa fuska, amma tana
cewa ba komai, da abin yazo gadan-gadan wani kuka ta barke da shi tana wash, Sadiq da sauri
ya d'auketa ya sanyata a mota sai asibiti. Bayan Sallar magrib ta haihu 'yan biyu Mace da
Namiji. Zo kuga murna wajen Sadiq kamar zai mai da Husna cikinsa dan murna, harda kukan
farin ciki ya yi. Daga asibiti gida aka wuce da ita aka dire ta part d'in Inna, kan kace miye dangi
na kusa zun soma zuwa barka cikin dare, harda su Momy Habee a 'yan barkan dare, little
Al'amin kuwa yana mak'ale da gadon yaran sai murna yake ya samu abokan hira, mutanan
Kaduna da sassafe suka kamo hanya Ammi Jidda ne kawai suka bari a gida irin ta yi kunyar
d'an fari, Umma ko da ita aka zo dan sai anyi suna zata tafi, wannan karan su Zahra da su a
kaci suna suma goye 'ya'yansu gwanin sha'awa sunyi bul-bul. Ranar suna yara suka ci sunansu
Hassan da Husaina, suna kiransu Amir da Amira, anyi shagali sosai. Sadiq har wata 'yar walima
ya had'a a wani hol, Malamai biyu aka kira suka yi wa'azi akan *Tarbiyyan yara A Musulunci*,
bayan an gama wa'azi aka ci aka sha. can na hango matan *sirrin 'ya mace* suna cin rengem,
gaskiya kuna da zuminci domin kun yiw Husna kara da Uncle Sadiq. Allah ya kara zumunci
Ameen. Lol [11/6, 8:28 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 69 ~ 70_*
_Karshe_
*Wannan page din kyauta ce gare ku masoyan wannan littafi, Allah ya bar zumunci ya bar
kauna. Ina muku so d'aya tak mara algush.♥✨*
Bayan Husna ta yi arba'in sai da ta kuma wata d'aya, a lokacin yaran sun k'ara kwari kafin aka
d'auketa sai gidan mijinta, da mai taya ta raino Mama Jimmai mai yi musu aiki, domin Husna ta
ce bata son kowa sai ita, dole aka bata ita su kuma su Momy Zee suka samo sabuwa.
An zarce da su sabon gidanta da Sadiq ya gina, babban filat mai kyau, Husna da mamaki take
kallonsu tana son magana amma sai ta yi shuru tana tunanin kila zasu biya wani waje ne, hon
Sadiq ya yi mai gadi ya bud'e musu ya shiga ya yi parking wajen parking space, mai gadi ya
rugo da gudu yana ma Sadiq sannu da zuwa, kayansu ya d'auka ya yi ta shiga dasu, da
mamaki Husna take binsu da kallo har suka gama shiga da kayan, Sadiq yana mata murmushi
ya d'aga mata gira.
"Madam mu shiga ko"
Ba musu tabi bayansa tana rik'e da Amira, Mama Jimmai na rik'e da Amir, suna shiga Husna
tabi falon da kallo tana santinsa.
"Wow gaskiya gidan nan ya had'u tsarinsa ya min"
Sadiq ya yi dariya Sadiq yana kallonta.
"Ga key d'in, gidanki ne"
Husna tsalle ta yi ta rungume shi da yake ta kwantar da Amira a kujera, shima rungume ta ya yi
tsam a jikinsa kana ya d'auketa cak ya wuce da ita bedroom d'insa, Mama Jimmai ta bisu da
murmushi da alama sun manta tana falon, yaran ta gyarawa kwanci ta kunna TV ta soma kallo.
su Sadiq kuwa sabon soyayya ce ta b'arke, suka shiga tarairayen juna saboda tsabar missing
d'in da suka wa juna, tuni salon ya canza nan na fito na basu guri.
Bayan komai ya lafa suka filo cikin sabon shiga Husna sai sunna kai take k'asa wai tana kunyar
Mama Jimmai sai yanzu ta tuna da ita, Sadiq ya nunawa Mama Jimmai d'akinta dake cikin
falon, d'akine mai d'auko da gado da Waldrop da bayi a ciki, Jimmai ta jinjina wannan
karramawa da suka mata nan ta yi godiya suka barta. Sadiq ya nunawa Husna nata sannan
suka koma part d'insa mai dauke da k'aramin falo da d'akuna biyu a ciki nata d'aya na shi d'aya,
sannan a nan babban falo a kwai nashi da nata ma, komai ya yiwa Husna kyau.
Bayan kwana biyu da dawowarta, ya kai ta gidan Yasir da shima ya dawo kusa da gidansu, duk
in da Sadiq yake yana biye da shi kamar bindi, ganin Sadiq yana ginin gidansa yasa shima ya
siya filin kusa dana Sadiq din ya soma gini, sun gama kusan lokaci daya sai ya riga shi tarewa
saboda Husna tana gida wanka. Mak'ota suke ginin na jikin juna, akwai k'aramar k'ofa a tsakani
wanda zasu sadu da juna ba lallai sai sun fita ta gate ba kan suje gidan juna, kusan gininsu iri