Showing 33001 words to 36000 words out of 81944 words
Chapter 12 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf
gyada masa kai alamar eh, kana ya fito ya zauna a falo
yana jiranta.
Wanka ta yi sosai iya iyawarta, ta fito d'aure da tawul, ta zauna gefen gado, ta goge jikinta
sannan ta sanya kayan da Sadiq ya siya mata, sannan ta d'aura d'an kwali ta fito, kallo ya bita
da shi dan har kamanninta ya sauya akan na d'azu, murmushi ya yi mata kana ya koma ciki ya
gyara ko ina sannan ya fito da mai wanda zata rika shafawa saboda kurajen jikinta ya ce ta
shafa, bayan ta shafa sannan ya d'auko ledan take away daya yi musu ya bata nata sannan
shima ya d'auki nashi suka faraci. Bayan sun gama ya tashi da sauri ya d'auro alwala ya ce ita
ma taje ta yi, ya tayar da sallah harya idar ita ma tana biye da shi duk abin da ya yi shi take ta
yi, ba zai iya barinta a gidan ita kad'ai ba shiyasa ya yi sallar la'asar dinsa a gida. Wasa ya fara
janta da shi nan da nan ta saki jiki ta fara walwala, sune har kusan k'arfe biyar suna buga game
a computer d'insa, jin karar bugun k'ofar gidansa ne ya katse su, ko da ya fita ya bud'e gate din
sai ya ci karo da Baba mai gadi, ko gaisawa bai bari sunyi ba ya ce.
"Sadiq ba a ga Husna ba tun d'azu data tafi makaranta, kuma anje makarantan ba a ganta ba
shi ne na zo na sanar maka"
Sadiq hankalinsa a tashe ya ce.
"Subhanallahi Baba me kake fad'a haka? Husnar tawace ba a ganta ba? ya salam, ina zuwa
bari na sauya kaya na fito"
Sadiq ya koma ciki ba tare da ya jira amsar Baba ba, yana wani murmushi a ransa, ya kunnawa
Husna tv kana ya ce ta jira shi zai je ya dawo, key ya d'auka ya kulleta ta baya kana ya fita ya
samu Baba.
"Mu je mu bincika ta ko Allah zai sa mu ganta"
Haka kuwa suka shiga zagaye unguwar a k'afa, tare da tambayar mutane harda kwatancen
surarta, kowa suka tambaya zancen d'aya ne basu ganta ba, haka suka gama bulayi basu ga
wata yarinya mai kama da Husna ba, dole suka juyo gida jugum-jugum hankali tashe. Ta
b'angaren Sadiq kuwa a cikin zuciyarsa hankalinsa kwance yake, yana k'issima ko Husna ta yi
barci ko k'ila kuma tana wasa, ya yi murmushi a ransa ya ce.
'Baza ku tab'a ganin ta ba kuwa har sai na tabbatar taji sauki sannan zan bayyanata'
A ranar dai Momy tana Addu'ar Allah yasa ta b'ace kenan bazyata dawo ba, a fili kuma harda
kukan munafunci, ko da ta zantawa Dady bacewar Husna ya nuna ko a jikinsa bai saima ya ce.
"To ai ita ta sani tunda bata jin magana, wato haukar nata ya tabbata kenan, tunda bata san ta
dawo gida ba, to Allah yasa bata yi nisa ba"
Abin da ya iya fad'a kenan ya cigaba da harkokinsa.
*****
Sadiq daya koma gida ya sameta tay i barci ga hawaye ya bushe a kuncinta, alamar ta yi kuka
sosai, ya tasheta ra farka a firgice da ta ga shi ne sai ta rungume shi tana son yin kuka, Sadiq
ya yi murmushi.
"Yi hakuri my Husna, na yi miki laifi ban dawo da wuri ba ko?"
Cikin shasshek'ar kuka ta ce.
"Ni ka kai ni gida ina tsoro kar Momy ta duke ni"
"Husna yau ba zaki kwana a gida ba, tare da ni zaki kwana har sai kin ji sauk'i zan maidaki
gida"
Cike da rashin yarda Husna ta girgiza kai ta ce.
"Uhum ni dai ka mai dani gida karta duke ni"
Sadiq ya shiga lallashinta da kyar ta yarda zata kwana.
Haka dai ta kwanta bisa gadonsa a d'arare, shi kuma ya kwana a falo kan doguwar kujera
zuciyarsa fari k'al ba d'igon damuwa a ciki.
_Ya labarin zai ƙare? Tirƴashi! akwai sauran cakwakiya_
*Daga wannan shafin 23-24, na yanke muku kuɗin samun cigabansa har zuwa ƙarshe, a cikin
farashi mai sauƙi ta yadda zaku iya siya a sauƙaƙe.*
Don samun cigaban wannan littafin har zuwa ƙarshensa, a biya N100 kacal. A tura ta wannan
account number. í ½í±‡í ¼í¿¾
Ramatu Muhammad kabir.
Acc no- 0106956864
Diamond bank.
A turo shaidar biya ta wannan number 07036993733.
Ko a turo katin MTN N100 ta wannan number 07036993733.
*Rahma ce*
[10/24, 8:02 PM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *KAÆŠAICI*
© *Rahma Kabir*
*Wattpdad:*@rahmakabir
*_Page 25 ~ 26_*
*Bayan kwana Uku*
Husna ta gama amsar treatment d'inta, ta ji sauƙi sosai k'urajen jikinta duk sun soma mutuwa
kad'an ne suka rage, ta yi kyau, har d'an k'iba ta yi, hasken fatarta ya fito, ta saki jiki sosai da
Sadiq sai dai lokaci zuwa lokaci tana yi masa maganar ya mai da ta gida, haka yake fita aikinsa
da safe, da rana ya dawo ya kawo mata abinci in sun ci sai ya koma, zuwa yamma ya dawo, ba
zai sake fita ba sai wata safiyar.
Momy ta saduda da Husna ta b'ace, Dady ya sanya a nemota amma har yau shuru, har gidan
radio ya sanya a sanar cewar.
"Yarinya Æ´ar kimanin shekara takwas mai suna Husna, ta b'ace sanye da uniform d'in karanta a
jikinta tana da matsalar kwakwalwa, ba tada hankali sosai, sannan siririya ce fara mai yawan
suma a kan ta"
Haka suka yi ta yad'a sanarwa, wanda Sadiq ya saurara a radio motarsa, murmushi kawai ya yi
ya cigaba da harkokinsa
******* *******
*Mako d'aya*
Da b'atar Husna amma ba amo ba labari, a b'angaren Sadiq kuwa yana cike da farin ciki sosai
yadda ta sauya ta yi kumari sannan sun k'ara shak'uwa sosai, uniform d'in da ya wanke mata ta
sanya tare da rataya jakarta, tana dariya ta ce.
"Uncle yau zani makaranta na ga k'awata kuma yau zan koma gidanmu ko?"
Sadiq ya yi Murmushi na rashin farin cikin rabuwarsu.
"Eh yau zaki koma amma fa kar ki gayawa ko a nan gidan kika zauna kin ji, in kika fad'a zan
d'auko sojoji su kama ki kuma su d'aureki su bawa zaki ya cinye ki"
Husna ta zaro ido waje tare da toshe bakinta cike da tsoro ta ce.
"Wallahi ba zan fad'a ba Uncle, dan Allah karka sa su kama ni"
Dariya ce taso kuɓuce masa amma sai ya gimtse.
"Ai in baki fad'a ba, ba zasu kamaki ba"
Ta d'ago kai suka had'a ido, gira ya d'aga mata.
"Yes ko zaki fad'a?"
Da sauri ta girgiza kai.
"Ba zan fad'a ba"
"Good girl zo mu tafi ko"
Haka suka fito suka shiga mota suka wuce, bayan sun ƙarasa in da ya d'auketa ran nan, a nan
ya ajiye ta sannan ya bata naira d'ari ya ce ta shiga makaranta, a kan idonsa ta shiga kana ya
wuce office.
Cike da mamaki Anty Meena ta ga Husna, ta san ance ta b'ace kuma ko yau an sanar a
Assembly, da sauri ta kira headmaster ta sanar masa, kan ace miye duk Malaman makarantar
sun taru a kan Husna suna faÉ—ar albarkacin bakinsu, Number Dady suka kira suka sanar da shi
halin da ake ciki, da sauri ya bar gurin aiki ya zo yaga abin mamaki, suna had'a ido da shi ta
fara ja da baya hawaye na fita a idonta, hankalinsa ne ya tashi, a yanzu ne yake jin wani iri a
jikinsa, cikin sanyin jiki ya ce.
"Husnahhh"
Da gudu ta ruga ta rungemshi tana kuka, an kira Æ´an sanda sun yi mata tambayar duniya amma
taƙi ce musu komai, domin ta tuna zancen da Sadiq ya gaya mata, shiyasa taƙi magana haka
aka sallamesu ba tare da wani bayani ba.
Dady gida ya wuce da ita, Baba mai gadi yana ganinsu ya gaishe da Alhaji tare da nuna farin
ciki sosai na ganin Husna, bayan sun shiga ciki Momy cike da tashin hankali ta tarbe su sai ta
fara wani rik'eta irin tana cikin farin ciki da ganin ta, Husna dai gum ta yi yana tsoron kar ta yi
mata wani muguntar, nan Dady ya gama abin da zai yi ya koma office, yana fita Momy ta kama
kunnenta tana ja.
"Dan ubanki ina kake je? kina k'aramarki kin fara yawon ta zubar ko, wallahi sai na yi maganin
ki, iye ji yadda kika canza, daga ɓacewa har ƙiba kika yi, ko ma dai aljanu ne suka d'aukeki ne?"
Husna kunnanta ya fara mata zafi saboda Momy da k'arfi ta rik'e tana jaa, da ta ga ba sarki sai
Allah sai ta mamayeta ta ganna mata cizo a hannu, da sauri Momy ta sake ta tana yarfe hannu
tare da jifarta da mugun kallo irin zaki ci ubanki, Husna tana ganin haka sai ta ruga d'aki da
gudu tana haki. Tsoro da mamaki ne ya cika Momy tana tunanin wani mataki zata d'auka, d'aki
ta bita ta daka mata tsawa, Husna ta sauko daga gado tana kama jikinta, Momy ta É—aga hannu
zata kai mata duka Husna ta saki wani irin razanan nan k'ara wanda ya kaÉ—a hantar cikin Momy,
idanun Husna suka sauya kala zuwa ja kuma sun fiffito waje tare da gunji kamar wata zakanya,
Momy tsoro ya gama rufe ta, ba arziki ta fita daga d'akin a sittin tana waige, tana fita Husna ta
dawo dai-dai sai ta saki dariya tana kyalkyalewa, bayan ta gama ta haye gado ta kwanta barci,
ba ita ta farka ba sai ƙarfe biyun rana.
Husna ta fito falo ta samu Momy zaune a falo tana cin abinci a plate ga juice da cup a gefe,
tana ganin Husna gaban ya faÉ—i sai ta yi saurin kauda kanta ta cigaba da cin abincinta, Husna
tana ganin abinci cikinta ya soma kuka, nan take fuskarta ya sauya ta gwalo ido waje wanda
suka sauya zuwa ja, sai ta saki murmushi ta tunkaro wurin Momy, tana isa ta sanya hannu ya
fizge plate É—in tana cewa cikin wani irin murya.
"Muguwa kawo shi nan ai Abbana ya siyo"
Momy sakin baki ta yi tana kallonta jikinta babu in da baya ɓari, ta kasa kallon fuskar Husna sai
sunne kai take, Husna ta sheƙe da dariya ta aje plate ɗin a ƙasa ta ɗauki juice da cup ɗin ta aje
gefe ta zauna ta tankwashe ƙafa ta fara cin abinci hankalinta kwance, Momy ta zuba mata ido ta
kasa cewa komai zai zare ido take kamar maƙaryaciya.
"Tashi ki bani guri kafin in illata idanunku muguwar Mata kawai, kina kallonta sai kace mayya"
Cewar Husna ta ɗago kai tana kallon Momy tare da danƙara mata harara.
Momy ta miƙe a zabure ta kama hanyar bedroom ɗinta tana waigen Husna cike da tsantsar
tsoro har ta shige ɗaki, haka ta jiyo dariyar Husna kamar wata ƙatuwar mace, Momy taji fitsari
ya kamata da gudu ta faÉ—a toilet tana haki.
******
Tun daga wannan ranar Momy ta soma tsoron Husna ko tsawa Momy ta daka mata, ita ma zata
rama da tsawa mai cike da firgitarwa. Ba arziki Momy ta koma gun boka ta yi masa bayani, sai
ya ce iskanci ne kawai amma ba wani abu, domin shi dai ya yi bincike bai ga komai ba, sai ya
bata wani ƙullun magani da zata turare ɗakin Husna da shi. Haka dai Momy ta dawo gida jiki a
sab'ule, ta samo rushin wuta ta sanya wannan maganin da boka ya bata ta nufi d'akin Husna, ta
shiga tana rik'e da kaskon wutan yana fidda hayak'i, Husna tana zaune ta É—ago kai, suna haÉ—a
ido, Momy ta ji gabanta ya fad'i, cikin kakkausar murya Husna ta ce.
"Me kike yi a nan? ki fita min da k'azantar nan tun kafin in illata ki muguwa azzaluma"
Cikin tsoro Momy ta fita daga d'akin jiki na rawa, taje ta kashe wutan ta dawo falo ta zauna a
kujera tare da rafka tagumi, Dady ne ya shigo ya sameta a haka sai ya samu wuri ya zauna.
"Hajiya lafiya kike zaune shuru?"
Kwalla ya sauka a kuncinta.
"Ni fa Alhaji tun dawowar Husna sati biyu kenan na kasa gane kanta, kamar an chanza mana ita
fa"
Nan ta shiga ba shi labarin k'arya da gaskiya, Dady ya yi murmushi kawai ya mik'e tare da
cewa.
"Haba Habeeba ke da kika fi kowa sanin Husna ba tada lafiyar kwakwalwa, shi ne zaki tayar da
hankalinki, kawai Addu'a zamu cigaba da yi mata, ni zan shiga ciki in watsa ruwa"
Bai jira me zata ce masa ya wuce abin sa, Momy ta bi bayansa da harara tana jin haushin
yadda ya ƙi nuna kulawarsa a kan maganarta, Husna ta fito falon tana yatsine fuska, ta kalli
Momy.
"Ƙarata kika kai gun Abba ko? to ko zaki kwana dubu ne kina gaya masa babu wani action da
zai É—auka, mu zuba dani da ke, shaiÉ—aniya kawai mara tsoron Allah"
"Husna ni kike gayawa haka?"
"An gaya miki É—in mai bin boka"
Ta yi maganar cike da tsiwa tana murguda mata baki tare ta jan guntun tsaki. Sai ta fice da
gudu tana dariya, Momy ta bita da kallo cike da mamaki da tsoro, ta rasa gane kan Husna
shakka take a kan anya ba a sauyata ba kuwa?. Husna tana fita ta tsaya ta saki wani atishawa
mai ƙarfi kana ta dawo asalinta ta wuce gun Baba mai gadi.
Tun daga wannan lokacin Husna ta samu freedom, sai dai an saketa sakaka ba wani kwab'a
saboda yanzu Momy tsoranta take ji sosai, bata iya yi mata maganar komai, shi kuma Dady
aikinsa ya sanya a gaba, ba ruwansa da lamarin lafiyar Husna domin asirin da Momy ta yi masa
tana nan a jikinsa, yanzu tana fita wurin Baba su yi hira, wataran ma da Sadiq suke hirarsu,
Dady da Momy dai sun zubawa Husna ido ba mai iya katab'us a kanta.
******* ******
*A Kaduna*
Husna pharmacy ya bunk'asa sosai har bayar da sarin magani suke yi, hankalin Zainab ya
kwanta har wani k'iba ta yi, daga nan kuma sai manema suka yi mata ca, amma sam tak'i
amincewa, kowa dai yana iya k'okarinsa wajen ya samu zuciyarta amma tak'i bari, a ciki harda
Dr. Idris ya nuna yana sonta amma tak'i, ko da su Baffa suka yi mata magana sai dai ta ce su ta
ya ta da Addu'a, dole suke hak'ura saboda basa son takura ta, Addu'a suke mata da fatan
samun miji nagari. A zuciyar Zainab kuwa burinta bai wuce Khalil ya dawo gareta ba, tana
tsananin kewar Æ´arta Husna, lokuta da dama tana kashe lokaci ta zauna tana tunanin rayuwar
da suka yi a baya, duk farin cikin da take ciki a yanzu bai kai farin cikin da za a ce ta wayi gari ta
ga Khalil da Æ´arta ba.
*Rahma ce*
[10/25, 10:16 AM] Rahma Kabirí ¼í¼º: *_Page 27 ~ 28_*
*Bayan kwana biyu*
Momy tana zaune a falo Husna ta fito ta samu Momy tana amsa waya, bayan ta gama ta miƙe
da sauri ta nufi ɗakinta, Husna ta miƙe tabi bayanta tana yin wani shu'umin murmushi.
"Zanga yadda zaki fita yau"
Ta ce, ta isa ɗakin taga Momy bata nan tana toilet, da sauri ta cire key dake jikin ƙofa ta fito ta
jawo ƙofar ta sa key ta rufe ta baya, kana ta bar key ɗin a ciki ta yi gaban a binta tana dariya,
taje ta can bayan window Momy ta tsaya dan ta san ƴila ta leƙo ta nan. Momy ta fito daga toilet
ta shiga shiryawa sauri-sauri, bayan ta natsa ta yafa gyale ta É—auki makullun mota tayo hanyar
ƙofarta, ta kama handle ɗin ƙofar ta ja sai ta ji a kulle yake gam ta duba key baya jiki, ta ƙara
sanya ƙarfinta ta ja sai ta ji fa a kulle yake sai ta shiga niman makullin ɗakin, ta yi nimar duniya
bata ganshi ba, Husna ta ji ɓuruntu ya yi yawa daga cikin ɗakin sai ta kyalkyale da dariya,
Momy ta ji dariyar sai ta yi saurin buÉ—e windon suka haÉ—a ido, Husna ta sauya idonta ya koma
hararagarki ta zaro su waje kana ta kama gefen bakinta da hannu biyu ta wage bakin ta
zazzago harshenta tana yararin miyau, Momy tana ganin haka ta saki labule ta shiga kiran
sunan Allah, ta yi mugun tsorota, a ganinta ba Husna bace tana ganin Aljana ce ta yi suffarta,
Husna ta saki abin da ta yi ta kwashe da dariya, Momy ta kuma buÉ—e labule sai taga Husna ta
dawo dai-dai, Husna ta shiga nuna ta tana dariya.
"Yeeee na bawa Momy tsolo, ba kin ce zaki fita ba to ba zan bari ki je ko ina ba, muguwa kawai"
Ta ƙare maganar tana murguɗa baki sai ta bar wurin windon ta wuce ɗakinta, tana isa ta fada
gado barci mai nauyi ya yi gaba da ita. Haka Momy ta yini a É—aki kuma ikon Allah gidan ba
kowa daga ita sai Husna, ko ta yi ihu ba mai jinta, haka ta zauna gefen gado tana cika tana
batsewa iya ƙuluwa ta yi, ƙarshe haka barci ya ɗauketa mai nauyi har tsawon wani lokaci.
Dady ya dawo gida da misalin ƙarfe shida na yamma, ya samu falon ba kowa sai kawai ya
doshi É—akin Momy, ya samu a rufe yake ta waje.
"Ohhh ita kuma Hajiya ina taje haka bata sanar min ba"
Ya yi maganar a zuci yana buɗe ƙofar da key, da sauri Momy ta taso ta dawo kusa da ƙofar don
ganin wanda ya buÉ—e ta dan ta jima da farkawa, ta