Showing 6001 words to 9000 words out of 81944 words

Chapter 3 - KADAICI Complete Book by Rahma Koise .pdf

24 Jun 2025

2385

gamsu kamar yanda na labarta miki, sai kuma rubuta result ɗin dana

yi, amma sam banyi wani abun cutarwa ga yarinyar ba, kawai dai damuwar da nake yi shi ne,
zuciyoyi nawa nasa a cikin damuwa? Kamar yanda nake tsammani kinga ga mahaifin yarinyan
yana cikin damuwa sosai, a yadda na yi waya da shi Allah kad'ai yasan halin da yake ciki,
wannan shi ne abin da ya hanani sukuni yinin yau"
"Gaskiya Abban Khadija ka yi matuk'ar k'ok'ari da taimakon da ka yi, Allah yaga niyyar ka akai,
ba zai kamaka da laifi ba, saboda ka yi dan ceton rai ne, kuma ma da baka yi haka ba Allah
kad'ai yasan ina Hajiyar zata je dan aiwatar da mugun nufinta, kasan dai da kud'i kuma mutane
babu tsoron Allah a ransu zata samu masu yi mata haka, ni dai ka daina damuwa insha Allah
babu wani matsala Addu'a zamu yi, Allah ya yafe maka ƙarya da ka yi dan ceto rai da kuma
Allah ya fidda yarinyar daga wannan damuwa"

"Ameen ya rabbi"

A sannan ne ya iya sakin jikinsa, Ameena ta kawo masa abinci ya fara ci, sai ta shiga yi masa
hira.

"Wallahi haka Khadija take bani labarin wata 'yar class d'insu a makaranta, wai Maman yarinyar
bata bata abinci kullun cikin k'azanta 'yar take zuwa makaranta, ita ke tsammata abincin in ta je
da shi, dalilin daya sa kenan na ƙara mata yawan abincin saboda Yarinyar ta riƙa ci"

"Yanzu haka ita ma bai wuce riƙonta a ka yi ba, Allah dai ya kyauta yasa mufi ƙarfin zuciyarmu"

"Ameen ya rabb, bari na je na duba su Khadija ko sunyi barci"

"Ok ki tawo min da coffee in zaki dawo"

Ta amsa masa to ta wuce tana jinjina labarin da Mijinta ya bata.

******* *******

Daddy bai iya cin komi ba yaje d'akin Husna ya zauna gefen gadonta tana barci, kallonta yake
yi yana zubda kwalla, ya shiga tunanin Zainab mahaifiyarta wacce suka yi taƙaitaccen rayuwa
cikin wahala da tashin hankali, soyayyar da yake mata shi ne ya koma katsokan kan Husna,
damuwarsa yanzu shi ne, in Zainab taji halin da ƴarsu take ciki ya zata yi?
"Zainab na san duk inda kike a yanzu kina cikin kaɗaici da damuwa, na yi alƙawari zan ƙara
nisanta dake ba zan taɓa bari ki san halin da Husna take ciki ba, dan na san in kika ji zaki shiga
cikin tashin hankali, zan kuma kula miki da ita kamar yadda kika danƙa min amanar ta, har
zuwa ƙarshen rayuwata"
Ya ce a fili yana mai goge kwallarsa, ya gyarawa Husna kwanciya ya fito ya wuce ɗakinsa jiki a
mace. Momy saboda bak'in ciki ko d'akin bata biyo shi ba, tana d'akinta sai kai komo take yi

abin duniya ya dameta, harta soma dana sani akan dama bata haukata Husna ba, tunda gashi
hakan na niman barazanar shiga tsakaninta da mijinta ta. Ta ɗauki wayarta ta kira Haj. Uwani
labari duk abin da ke faruwa.

"A gaskiya ina ganin Hajiya zan sauya salo, gobe insha Allah zan zo ki kaini gun boka danya
bani maganin mallaka"

"Karki damu ƙawata wannan ai abu ne mai sauƙi, je ki kwanta ki yi barci mai dad'i kamar kinyi
bak'o ya mutu, kin san boka cika aiki bai da matsala"

"Hakane Hajiya, nagode sai na zo"

"Ok Allah ya kaimu "

Sai suka aje kan wayar.

****** ******

*Washe gari*

Momy ta fito daga sashin ta, ta nufi ɗakin Husna ta d'aka mata duka ta farka a firgice.

"Maza tashi ki shirya ki tafi makaranta, daƙiƙiyar yarinya kawai, wannan ma ai asarar kuɗin
makarantar yake dan nasan ba wani abun kirki kike ɗauka ba"

Husna ta sauko daga gadon da sauri ta nufi ba yi, Momy taja dogon tsaki kana da juya ta fice
tana sababi. Husna ta wanke fuska da k'afa ba zancen wanke baki ko ta yi wanka babu wanda
yake nuna mata, haka ta taso cikin rashin kula da gata, cikin sauri ta shirya ta sanya uniform ta
ɗauki jakarta ta fito falo taga Momy zaune ta d'aura ƙafa ɗaya kan d'aya, jiki a sanyaye ta je
gabanta ta tsuguna ta ce a tsorace.

"Momy ina jin yunwa"

ta yi maganar kamar zata yi kuka, Momy ta daka mata tsawa.

"Bari na zama abinci sai kici ko, maza ki b'ace min da gani wawuya kawai, mahaukaciya"

Jikinta yana ɓari ta bar falon har tana cin tuntuɓe, ta nufi wurin Baba mai gadi.

"Baba ina kunu na da kosai"

Ta ce fuska kamar zata yi kuka, Baba ya yi murmushi yana kallonta cike sa tausayawa

"Na cinye ban rage miki ba"

Husna ta yi rau-rau da ido kamar kwalla zai zubo ta ce.

"Allah yunwa na keji fa"


Baba ya miƙe zai d'auko mata sai kuma ya tuna da gargad'in da Dady ya yi masa, sai na ciro
naira ashirin a aljihunsa na gaban riga ya bata.

"Gashi ki siya kosai kici yau ban aje miki komai ba, kiyi haƙuri ƴar Baba"

Sai ta fara yi masa kuka ta amsa kud'in ta fita gate ranta a dagule.

*****
Bayan ta isa makaranta ta zauna inda ta saba zama, duk yaran suna cikin walwala sannan sun
kasance fes amma banda Husna da take warin datti, ta zama abin kyama da tsangoma cikin
ɗalibai, ta manta da kayan da Jimmai ta wanke mata, garin sauri da fargaban kar Momy ta
bugeta ta sanya masu datti, dan ba gaba ɗaya Jimmai ta wanke mata ba saboda bata aje su a
fili ba. Khadija ce ta shigo riƙe da basket na abinci ta zo kusa da ita ta zauna tana dariya.

"Husna yau kin rigani zuwa, Abbana ne yasa ni latti"

"Um ni, ni ko brush banyi ba Momy ta koroni wai in tafi makaranta, um um ko kar yawa banyi ba
yunwa nake ji"

Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka.

"Momin ki bata sonki muguwa ce, to ga abincina ki ci Momy na indomie ta dafa min harda kwai"

Cewar Khadija, Husna ta amsa abincin ta fara ci hannu baka hannu kwarya, sai da ta ci kusan
rabi sannan ta rufe kular, ta ɗauki gorar ruwa tasha kana ta yi gyatsa.

Anty Meena ce ta shigo class d'in, duka yaran suka tashi suna gaishe ta, ta musu umarni dasu
zauna cikin harshen turanci, nan ta fara musu karatu bayan ta kammala ta umarce su dasu
kawo mata assignment ɗin da ta basu na ranar friday, duk suka kai mata amma banda Husna,
ta dago kai ta ce.
"Husnah Khalil"

Husna ta amsa sai ta isa gaban Malamarsu ta tsaya.

"Ina naki assignment ɗin ban ganshi a nan ba, ko yau ma ba ki yi ba?"

Idon Husna ya ciko da kwalla.

"Um um na ce ma Momy na ta min amma taƙi sai ta koreni"

Anty Meenat ta dafe kai ta shiga yin zancen zunci.

'Wai yaushe yarinyar nan zata zama mai ƴanci ne? kullun cikin matsala ohhh ya rabbi'

Ta ɗago ta kalle taga kayan jikinta duk datti.

"Husna wai me yake damunki ne? meyasa Maman ki bata baki kulawa ne? gaki da kwakwalwa
amma iyayenki suna mai da miki karatun ki baya, me yasa jiya monday baki zoba?"

Husna ta fara kuka ta fara ta ce.

"Anty, Momy ne bata min wanki ni kuma ban iya ba, Baba mai gadi nake bamawa ya wanke min
ko Mama Jimmai, kuma Momy tana duka na sosai har zagina tanke yi ta ce min mahaukaciya"

Damuwa ya ziyarci Anty Meena sai ta ƙirƙiro murmushi.

"My dear ki daina faɗar haka Momy ki tana sonki, k'ila kina mata laifi ne, dan haka ki riƙa mata
biyayya kinji zata daina dukanki"

Husna ta girgiza kai alaman ta daina, Anty Meena ta share mata hawaye ta umarce ta data
koma ta zauna...

_Wace ce Husna Khalil?_

*Rahma ce*
[10/14, 5:42 PM] Rahma Kabir: *KAƊAICI*

© *Rahma Kabir*

*Wattpad:*@rahmakabir


*_Page 7 ~ 8_*

*WACE CE HUSNA KHALIL?*

_Waiwaye adon tafiya_

Alh. Ahmad tanko mai kanti babban ɗan kasuwa ne acikin garin Kaduna, babu wanda bai san
Alhaji mai kanti ba faɗin garin da kewayenta, dan ya kasance mutum mai karamci da mutunci,
yana kasuwancin kayan hatsi da ɓangaren madara da sauran kayan masarufi, yakan yi order
daga garuruwa daban-daban, ya bayar da sari ga ƙananan ƴan kasuwa.
Asalin sa d'an garin yola ne bafulatanin asali daga ƙaramar hukuman michika, yana da mata
d'aya mai suna Haj. Asma'u Sani mai kanti, auren zumunci aka yi musu. Sunan mai kanti ya
samo asali ne tun daga gun kakannisu wanda daga yawon kiyo har suka yada zango a cikin
garin Kaduna, daga bisani suka zama sun yad'u a garin sosai, duk iyayensu sun rasu.
Alh. Ahmad yana zaune a unguwar malali, yaran su hud'u maza biyu mata biyu, Aliyu shi ne
babba, sai Ismail da yake bi masa, sai Fatima sannan Zainab ita ce auta.
Alh. Ahmad mai kanti wanda yaransa suke kiransa da Baffa, sai kuma Haj. Asma'u da suke kira
da Umma, sun tsaya sosai wajen tarbiyyar yaransu, sun basu ilimi na Addini har zuwa na
zamani.

Yaya Aliyu kamar yanda ƙannansa ke kiransa ya yi karatu a ɓangaren kasuwanci, bayan ya
kammala ya cigaba da riƙe kasuwancin mahaifinsu, ya yi aure sunan matarsa Jidda d'iyar
abokin Baffansu. Yaransu biyu, Abubakar Sadiq ne farko sai Fatima dake bi masa, wacce suke
kira da Zahra.
Yaya Ismail shi kuma ya kasance mai matuƙar son karatun boko ɓangaren lafiya, Baffa ya
turashi kasar India a can ya yi digree d'insa har ma da masters ya zama cikakken medical
Doctor, bayan ya dawo k'asarmu Nigeria ne ya soma aiki a general hospital dake nan cikin
Kaduna, a lokacin Anty Binta tana karatu a ABU Zaria 400level tana karanta Biology. Sai auta
Zainab da take secondary school matakin ƙarshe.

****** *******

_*Bayan shekara ɗaya*_

Ya Ismail anyi masa transfer zuwa kano wanda bai so haka ba, amma ba yadda ya iya dole ya
tafi. Bayan watanni da tafiyarsa yazo wani hutu a kaduna, Baffa da Umma suka sanya shi gaba
da zancen aure dole sai ya fito da mata, da farko ya tubure bai so saboda shi ko budurwa baida
ita, Baffa ya ce ya yi masa had'i da 'yar wajen abokinsa dake nan Kano Alh. Kamal, yaje su
gana in sun fahimci juna a sanya biki.

Ana cikin haka sai bikin Anty Binta ya tashi, bayan ta kammala karatunta service take yi a
ministry of education dake nan Kaduna, a nan ta haɗu da Al-mustapha Salis mai siminti,
mahaifinta ya kasance ɗan kasuwa yana sai da siminti da duk abin da ya shafi gini, bayan sun
fahimci juna aka sanya biki har sai ta kammala service nan da wata bakwai.
ya Ismail da yaje kano, ya tafi gidan Alh. Kamal, sun gana da Amina kuma sunyi na'am da

junansu, sun fahimci juna cikin k'ank'anin lokaci soyayya mai k'arfi ya shiga tsakaninsu, ganin
haka ne iyayensu suka tsaida kwanakin biki dai-dai dana Anty Binta a lokacin bikin sauran wata
huɗu.

******

*_Biki wan shagali_*

Lokacin bikin ya gabato, inda dangi da mutanen arziki duk sun hallaro, daga ɓangaren mutanan
Kano harna Kaduna duk suna ta fama da shagalin biki. Ranar asabar aka d'aura auren Anty
Binta da Al-mustapha, su Baffa suku ɗunguma zuwa Kano aka d'aura na Yaya Ismail, ansha
shagalin biki kowa yana cikin farin ciki. Auta Zainab ta yi farin jini kowa Zee, Al'amin d'an k'anin
Umma wanda suke kira da Baffa Iro, suna zaune a nan cikin Kaduna da matarsa Inna Kulu,
Al'amin shi ne d'a ɗaya da Allah ya basu, duk wani son duniya sun d'aura masa, ya yi karatu a
ƙasar Germany ya kammala, dawowar sa kenan ya cimma wannan shagalin, tunda ya yi arba
da auta Zee zuciyar sa ta kamu da sonta.

Haka aka sha biki, matar Yaya Ismail an kaita sabon gidan da Baffa ya siya masa a nan Kano,
ba'a sha wahalar kai Amarya ba, da yake ita ma nan kano suke, Anty Binta kuma an kaita can
gidan mijinta dake tudun wada, anyi biki an watse kowa ya koma gidansa lafiya. Angwaye da
Amare sun angonce cikin farin ciki tare da ƙaunar juna.
******
*Bayan wasu lokuta*

Shaƙuwa mai karfi ya shiga tsakanin Al'amin da Zainab tun sunayin abunsu su kad'ai har 'yan
uwa kowa yasan tsakaninsu, ana haka sai Zainab ta samu admission a ABU Zaria ta samu
pharmacy, farin ciki gunta ba a magana kowa ya yi farin ciki aka fara haɗa mata kaya da sauran
abubuwa na buƙata, lokacin da Al'amin yaji labari zuciyar sa bai yi masa dad'i ba yaso ace a
KASU ta samu saboda baya son ta yi nesa da shi, yaje ya samu Abbansa da zancen yana so a
nima masa auren Zainab, Baffa ya yi farin ciki sosai ya ce insha Allah zai je ya samu su Baffa
dan su dai-dai ta magana.

*Bayan kwana biyu*

Abba yaje ya samu su Baffa da maganar auren Zainab da Al'amin, sunyi murna dan dama
burinsu su zab'awa Zainab miji wanda zai kula da ita, nan suka yanke magana cewar an bama
Al'amin Zainab amma sai ta kammala karatunta sannan ayi bikin, duk suka yi na'am da haka,
kana suna yi hirar zumunci Abba ya tafi gida cike da farin ciki. Ko da ya labartawa matarsa da
maganar da kuma shi Al'amin ɗin sunyi murna kuma sun amince da hakan.

******
Ranar lahadi ya kama ranar da Zainab zata tafi makaranta, duka family sun taru a babban falon

gidan suna tattaunawa, anan Baffa ya shaida musu da hukuncin da suka yanke kan Zainab da
Al'amin, duk abin ya musu dad'i har ita kanta Zainab da taji kunya ya rufe ta, bayan sun tattauna
suka yi mata nasiha mai ratsa zuciya tare da mai da hankali kan karatu da kuma ta kama kanta
da mutuncin ta, sai da Zainab ta yi kuka, bayan sun kammala suka d'unguma dukansu su ka
nufi Zaria birnin zazzau.

Ko da suka isa, suka shiga cikin makaranta, b'angaren d'akin dalibai mata suka nufa, d'akinta
dake jerin k'asa sannan ita kad'ai zata yi using d'inta, babban d'aki ne ciki d'aya sai ba yi da
kicin aciki, sun gyara mata ɗakinta, sun sanya mata gado da katifa, sai kujera guda ɗaya
sannan kayan kallo sai kicin da suka gyara mata da tsirarun kayan buk'ata, sun wanke mata
bayinta, sun kammala mata komai, bayan sun gama suka ƙara mata nasiha kana suka kamo
hanyan Kaduna, suka bar Zainab cikin damuwa da kewar su, tana tsaye har sai da taga ƙulewar
motansu sannan ta juya tana share kwallan daya zubo mata a idonta.

Juyawar da zata yi sai taga mutum tsaye a gabanta, ta ɗago ido tana kallonsa ya sakar mata
wani lallausar murmushi wanda ya sanya gabanta faɗuwa.

"Ki yi haƙuri kowa ma haka ya tsinci kansa lokacin da aka kawo shi karatu, insha Allah da haka
zaki saba"

Ya ce yana kallonta, ta ɗaure fuska ba tare da ta ce masa komai ba ta matsa ta ba shi guri ta
wuce, ya shiga binta a baya kamar an sanyashi tsaronta, ta buɗe ƙofa sannan ta juyo ta harare
shi ta girgiza kai ta shige ɗakinta ta rufo ƙofa, murmushi ya yi wanda yake ƙara masa kyau kana
ya juya ya tafi. Gurin da suka saba zama ya nufa, ya hango Nuhu abokinsa sai ya k'arasa da
sauri yana ƴar fara'a ya ce.

"Abokina kasan kuwa yau na yi gamo da d'awisu"

"Haba a ina ka gani?"

"Hmmm yau ɗin nan na ganta, uhum kyakkyawa ce mai matsakaicin tsaho, dara-daran idanu
masu kama da kalar barci, mai d'an k'aramin baki tare da siririn hanci, fara ce dai-dai mai kama
da balarabiya, Allah ya yi halitta a wajen dawisu mai kyau da ado"

Nuhu ya saki baki yana kallonsa har sai da ya gama lissafowa ya ce.

"Ya kake magana a dunƙule kamar wani zautacce, ni fa ban gane maka ba, dawisu ka ganni ko
mutum?"

Ya yi wani lallausar Murmushi ya lumshe ido kana ya buɗe su.

"Ba zaka gane ba tunda baka san yadda nake ji ba, idan ka ganta sai ka tabbatar da abin da
nake gaya maka, hmmm yanzun nan na gamu da ita"

Nan dai ya kwashe yanda suka yi ya ba shi labari, dariya sosai Nuhu ya yi.

"Lallai Khalil yau Allah ya kamaka, ashe akwai rana irin ta yau da zanga Mace ta tafi da imanin
ka, kullun mata suna binka amma ka tsanesu sam kai wai baka soyayya, to yau gashi ka shiga
hannu da alama kuma zaka sha wuya"

Dariya ya yi ya ce.

"Kuma insha Allah duk wuya sai na yi nasara ba"

Yana faɗar haka ya miƙe tsaye da cewar.

"Tashi mu wuce in ka ga dama, in kuma zaka cigaba da min sharrin ne sai ka zauna"


********
Ɓangaren Zainab kuwa tana komawa d'aki ta zauna gefen gadonta ta yi ta gumi, tunanin
rayuwa take yi sai ga kiran yaya Al'amin ya shigo wayarta, sai ta d'auka nan suka soma hiransu
na masoya har kusan minti ashirin kana suka yi sallama, ta tashi ta gabatar da sallar la'asar
sannan ta ci abinci da yake Anty Jidda ta yi mata miyar stew mai yawa, da danbun nama tare
da soyayyar naman kaza, Anty Binta kuma cin-cin mai kwakwa ta yi mata sannan da meat pie,
Umma kuma yaji ta yi mata mai kyau da daɗi, a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login